Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ali Na ‘Yankuzo
G/Waƙa: Gonar Alhaji
Ali,
: Ƙare-kallonka[1],
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Ni Maidaji gani.
‘Y/ Amshi: Na shirya kaya zani
‘Yankuzo,
:
Dalilin Alhaji niz zaka,
:
Domin in gano gida.
Jagora: Gonar Alhaji Ali,
: Ta
yi buhun gero dubu-dubu[2].
‘Y/ Amshi: Kuma gonar Alhaji Ali,
: Ta
yi buhun dawa dubu-dubu.
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare
kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Gonar Alhaji Ali,
: Ta
yi buhun gero dubu-dubu.
‘Y/ Amshi: Kuma gonar Alhaji Ali,
: Ta
yi buhun dawa dubu-dubu.
Jagora: Shi buhun jad dawa an ce,
: Ya
hi buhun gero tuwon Ƙwarai.
‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,
: Ya
hi buhun dawa hurar ƙwarai,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka[3],
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Shi buhun jad dawa an ce,
: Ya
hi buhun gero tuwon ƙwarai.
‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,
: Ya
hi buhun dawa hurar ƙwarai.
Jagora: Naga matana na murna,
‘Y/ Amshi: Kowace sai ta kwashi zamiya[4],
:
Halama Alhaji Ali,
: Yai
masu masha’a hatsin tuwo,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Da Ta’Allah da amai kuɗɗi.
‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta
washiya[5],
:
Halama Alhaji Ali,
: Yai
masu masha’a hatsin tuwo.
Jagora: Da Ta’allah da amai kuɗɗi.
‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta
washiya,
:
Halama Alhaji Ali,
: Yai
masu masha’a[6]
hatsin tuwo,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Akwai wani babban dam wurin
Ali,
: Ya
yi tsayi yai hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Ni da niz zo in ebo shi,
: Na
ishe[7]
ya koma,
:
Hwarau-hwarau,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo,
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Akwai wani babban
dam wurin Ali,
: Ya
yi tsayi yai hwaɗi.
‘Y/ Amshi: Da niz zo in ebo shi,
: Na
ishe ya koma,
:
Hwarau-hwarau.
Jagora: Hillani[8]
kun cika gurin ku.
‘Y/ Amshi: Mashayarku ta koma ruwan hura.
Jagora: Hillani kun cika gurinku.
‘Y/ Amshi: Mashayarku ta koma ruwan
hura.
Jagora: Hillani kun cika gurin ku.
‘Y/ Amshi: Mashayarku ta koma ruwan
hura.
Jagora: Na game da hillanin Tsafe.
‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin
hura.
Jagora: Harda hillanin Bilbis.
‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin
hura.
Jagora: Har na ‘Yankara sun takas.
‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin
hura.
Jagora: Har na garin ‘Yammalammai.
‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma
wurin hura.
Jagora: Har na Ɗansaɓau sun tadakka.
‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma
wurin hura.
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Ashe harda ni makaɗin ganga.
‘Y/ Amshi: Ashe lokacin tashinmu ya
taho.
Jagora: Ashe harda ni makaɗin ganga.
‘Y/ Amshi: Ashe lokacin tashinmu ya
taho.
Jagora: In dai ana mana ɗan busau[9].
‘Y/ Amshi: Sai na tashi na koma wurin
hura,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Ni Maidaji gani
na,
:
Shira[10]
kaya zani ‘Yankuzo.
‘Y/ Amshi: Dalilin Alhaji Ali,
: Niz
zaka domin in gano gida.
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Hajiya Halima tana kyauta.
‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Ina godiya hajiya Mairo.
‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Hajiya Sa’a na gode mat.
‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Hajiya Sa’a na gode mat.
‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Dab baya tai mani anhwani[11].
‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Dab baya tai mani anhwani.
‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Lalle Alhaji na gode,
:
Ya ba ni buhu goma.
: A
yi min tuwo.
‘Y/ Amshi: To su kau dangi nai,
: Sun
ban buhu shidda,
: A
yi min hura.
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Lalle Alhaji na
gode,
:
Ya ba ni buhu goma,
: A
yi min tuwo.
‘Y/ Amshi: To shi kau dangi nai,
:
Sun ba ni buhu shidda,
: A
yi min hura.
Jagora: Lalle Alhaji na gode,
:
Ya ba ni buhu goma,
: A
yi min tuwo.
‘Y/ Amshi: To su kau dangi nai,
:
Sun ba ni buhu shidda,
: A
yi min hura.
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Shi buhun jad dawa[12]
an ce,
: Ya
hi buhun gero tuwon ƙwarai.
‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,
: Ya
hi buhun dawa hurar ƙwarai,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Shi buhun jad dawa an ce,
: Ya
hi buhun gero tuwon ƙwarai,
‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,
: Ya
hi buhun dawa hurar ƙwarai.
Jagora: Na ga matana na
murna,
‘Y/ Amshi: Kowace sai ta kwashi zamiya[13].
:
Halama Alhaji Ali,
: Yai
masu masha’a hatsin tuwo,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Da Ta’allah da mai kuɗɗi,
‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta
washiya[14].
:
Halama Alhaji Ali,
: Yai
masu masha’a[15]
hatsin tuwo?
Jagora: Da Ta’allah da Maikuɗɗi.
‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta
washiya,
:
Halama Alhaji Ali,
: Yai
masu masha’a[16]
hatsin tuwo,
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Akwai wani babban dam wurin
Ali,
: Ya
yi tsayi yai hwaɗi,
‘Y/ Amshi: Ni da niz zo in ebo shi,
: Na
ishe[17]
ya koma hwarau-hwarau[18],
:
Gonar Alhaji Ali,
: Ƙare-kallonka,
: Na
‘Yankuzo.
:
Wagga gona,
:
Allah yai mata,
: Ƙarhin
albarka,
: Ƙwarai-ƙwarai.
Jagora: Akwai wani babban dam wurin
Ali,
: Ya
yi tsayi yai hwaɗi[19],
‘Y/ Amshi: Ni da niz zo in ebo shi na
ishe ya koma,
:
Hwarau-hwarau,
Jagora: Hillani kun cika gurin ku.
‘Y/ Amshi: Mashayar ku ta koma ruwan
hura.
Jagora: Hillani[20]
kun cika gurinku,
‘Y/ Amshi: Mashayar ku ta koma ruwan
hura.
Jagora: Hillani kun cika gurin ku.
‘Y/ Amshi: Mashayakku[21]
ta koma ruwan hura.
Jagora: Na game da hillanin tsafe.
‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin
hura.
[1] Mai yawa sosai, wanda kan kure kallon mutum.
[2] Wato dubu saw dubu miliyan kenan
[3] Idan duk abin da kake tsammanin ka gani ka
gane shi hard a ƙari,
ka ƙare kallonka.
[4] Murna mai sa rawa.
[5] Jiki mai kyawo.
[6] Alkawalin za a bayar da wani abu.
[7] Iskewa.
[8] Fulani.
[9] Fari.
[10] Shiryawa/kimtsawa don tafiya.
[11] Amfani wato bashi kyauta.
[12] Jar dawa.
[13] Murna mai sa rawa.
[14] Jiki mai kyawo.
[15] Alkawalin bayar da wani abu.
[16] Alkawalin za a bayar da wani abu.
[17] Iskewa.
[18] Ruwan shad a aka zuba fura a ciki.
[19] Faɗi
[20] Fulani.
[21] Wurin da suka ba dabbobinsu ruwa.
0 Comments
Post your comment or ask a question.