Ticker

6/recent/ticker-posts

Danmakau

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma 

Ɗanmakau

 

 G/ Waƙa: Ya ci gona,

: Ɗan Makau,

: Ya kashe haki,

: Ɗan Indo,

 

  Jagora: Ɗan mai gona,

: Ɗan Sahabi,

‘Y/Amshi: Alhukumin haki,

: Giye na ‘Yam Molo.

 

  Jagora: Ɗan Mai mai gona,

: Ho[1] da rana.

  ‘Y/ Amshi: Alhukumin[2] haki,

: Giye na ‘Yam Molo,

: Ya ci gona,

: Ɗan Makau,

: Ya kashe haki,

: Ɗan Indo,

 

  Jagora: Yarinya tana faɗin,

: Ɗan Mai gayya,

: Mai hatci da kyawo,

‘Y/ Amshi: Gero nai kamad damuttsa[3] ,

  : Ɗamra giri,

: Garagurun wanke.

: Ya ci gona,

: Ɗan Makau,

: Ya kashe haki,

: Ɗan Indo,

 

  Jagora: Muhammadu,

: Kana da daɗin suna,

: Batun gayau ba,

: Tun hwarko,

  ‘Y/ Amshi: Kowak kirai[4],

: Ubangijinmu,

: Sai ya ce,

: Muhammadu Rasulullah,

: Ya ci gona,

: Ɗan Makau,

: Ya kashe haki,

: Ɗan Indo,

 

 Jagora: Wani doki kakai ka,x2

 ‘Y/Amshi: Ka miƙa man,x2

 

 Jagora: In dai ana yi man kyauta,x2

 ‘Y/Amshi: Fasali Daudu ba ya ƙarewa,x2

 

  Jagora: Magana ta yi man yawa,

: Wani lotto waƙa nikai,x2

‘Y/Amshi: Kamar reno.x2

 

  Jagora: Gurmu ya ishekke Maiƙuru,

: Sannan sun ishe Ƙurungugu.

‘Y/Amshi: Sai yas sa guruf ga ƙeyatai.

 

 Jagora: Ga Tunau ya yi tuma,

‘Y/Amshi: Ya hisge tumu,

: Ya yi tuntuɓe,

: Ya gurhwana[5] gun tumu,

: Da Ɗan tohi.

: Ya ci gona,

: Ɗan Makau,

: Ya kashe haki,

: Ɗan Indo,

 

Jagora: Boboniya[6] da kwanan amre,

: Mijinta ya gama ya kwanta,

:Ta yi mai kalami,

: Tac ce mai gidan da kali?

: Koko in ɗamra zanena,

‘Y/Amshi: Ya ce ɗaura wagga  ba ni ƙarawa,

: Ya ci gona,

: Ɗan Makau,

: Ya kashe haki,

: Ɗan Indo,



[1]  Gaisuwa ce ga mutanen Sakkwato. Kamar a ce sannu da rana.

[2]  Wasu maganganun larabci ne da sukan shirya abinsu, a nan yana nufin mai hukunta haki.

[3]  Damtsen hannu.

[4]  Faɗin suna ko neman taimako ko ambato.

[5]  Durƙusawa.

[6]  Macen da ba Bahausa ba.

Post a Comment

0 Comments