Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaji Labaran Baban Musa

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alhaji Labaran Baban Musa

G/ Waƙa: Ai irin jibo dan tsula Labaran baban Musa,

: Su Alhaji Labbo ciwon cikin ‘yan sarki.

 

 Jagora:  Ai yaka sakwati ai yaka toron giwa,

: Yaka sakwati ai yaka baban Musa,

: Babban Sa’adatu Labbo,

: Ya wa manoma nisa,

: Ita hanyar Bena ko wabbi daidai gandu,

: Ko mutum bai son Labbo,

: Ai ba ya ce mai raggo,

: Ban hana dai shi duɗe idanunai ba,

: Ai zaman ijiyam mutum,

: Na gwada mai haushi,

: In taga abinda hat bai iyawa an yi,

: Labbo in dai ya tai ga aiki gabakin gona,

: Hau wata addu’a ta ya kai in ya zo,

: Sai ya ce hatta tatiya humul bayyanatu,

: Wajen bayyanan nomanai,

: Waman yaƙanut kuma da kalme

: Na tonon laka.

 

Jagora : Aiki ƙaro darajja ma’aikin sarki,

: Addu’ar zurƙallaini ta yaj jiya yab bam mai,

: Bayan zurƙalaini su am manoman farko,

: Ai manomin duka duni....

: Ya bai yi tamkatai ba,

: Dole ka dole ko dole baban Musa,

: Labbo ubanka cilas a ce mai sarki,

: Kuma kakanka cilas a ce mai sarki,

: Tun da dai lardin Bauchi

: Duk ba a yi tamkatai ba,

: Ai sama dagga gidanka

: Mamman kana sauna tai.

 

Jagora: Wanda duk ba ya da gaskiya,

: Ba ya jin daɗi nai,

: Mamman bai sai da iko jiran kuɗɗi ba,

: Sanda na gwamatse Sanda toron gwari,

: Ai Sanda na gwamatse

: Ka yi gaba Bauchi,

: Katsina ta Dikko,

: Ta samu shedun girma,

: Daga Labbo na zaya zaɓa Bauchi,

: Tunda dai Hillanci[1],

: Ina za ya ƙin Katsinanci,

: Shi Katsinanci,

: Ina zaya ƙin Hillanci,

: Ai gidan tara ne goma,

: Sai ta ishe ta kwana.

 

Jagora: Ya ka sakwati ai yaka toron giwa,

: Mai kyau bashi toshi ga matar arme,

: Ai ɗiya ka gani nai,

: Ta ƙalge[2] ta ce ai sai shi,

: Uwa da ubanta duk ba su cewa komi,

: Ko sun ce ƙala duk bata dangin banza,

: Ai mu yanka sadaki,

: Da kowa kason armenai,

: Ga kaɓaki ruwayye ka na kallon nai,

: Kul badaɗe Labbo sai an naɗa ma sarki,

: Mijin hajiya Amina,

: Gaishe ka toron giwa,

: Mijin hajiya Tele,

: Ciwon cikin ‘yan sarki,

:Ya ka sakwati kai yaka toron giwa,

: Daga bana Haruna ka wa manoma nisa.

 

 Jagora: Ai Labbo ubanka cilas a ce mai sarki,

: Kuma kakanka cilas a ce mai sarki,

: Alhaji malan Isah a ciyaman alhazzai,

: Ai babban wa,

: Kamad dai mahaihi yaz zan,

: Malam ya taimakai don ka toron giwa,

: Allah dai ya cece shi domin na ci,

: Baban Asma’u ciwon cikin ‘yan sarki,

: Ai baban Binta ‘yan haihuwat tsohonai,

: Ba duka ɗa ka gadon uwaye nai ba,

: Ai zalangaɗe[3] wane,

: Kam ya yi ba daidai ba.

Jagora: To ina jaka ku da jaki ma ci karmami,

: Ina dan tara tsuhu jaki matsagi jaka,

: Wanda duk dai ma uwasshi dai bai sanin hali nai,

: Ni da nis san halinshi ɗibat tsumata niy yi,

: Ban ɗaga hunnunmu ko da ya na tsingilla[4].

 

Jagora : In dai ya ɗillan in zuba mai kashi,

: Irin jaki da ɗai sai da wannan hali,

: Alhaji Ahmad, ya taimaka don dogo,

: Alhaji Sulaiman, ya taimaka don dogo,

: Alhaji Isan Isa, ya taimaka don dogo,

: Alhaji Sanin Ayyu, ya taimaka don dogo,

: Ai Musa na Biba ya taimaka don dogo,

: Allah dai ya cece ku domin na ci.



[1]  Fulatanci.

[2]  Hawan wani ra’ayi ka mayar das hi naka.

[3] Tana sifantawa ne wato tana nufin mutum dogo musamman wanda bai san ciwon kansa ba-baya noma.

[4]  Tsalle-tsalle. Tafiya ana soka ƙafa ana gurgunta wajen tafiya. 

Post a Comment

0 Comments