Ticker

6/recent/ticker-posts

Haruna Mijin Dije

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Haruna Mijin Dije

G/ Waƙa: Ai dan mazan yi ma noman dawa bugun kamai,

: Haruna ɗebi da dama maƙi gudu Gwarzo.

 

Jagora: Ai maƙi gudu kawa hakin dawa koma,

: Rana ta yi arzuhur,

: Sani mai burodi,

: Meli babbn Jirgi,

: Sani mai buredi na ɗaki takwas,

: Sani ya gwada ya hini baya saman hannu ba.

 

Jagora: Sani mai burodi na ɗaki takwas,

: Ai sani ya gwada ya hini ba yasa man hannu ba,

: Sani ya gwada ya hini bayasa man hannu,

: Haruna ɗebi da dama maƙi gudu gwarzo,

: Maƙi gudu sa hakin dawa kwana,

: Rana ta yi arzuhur,

: Ta yi la’asar,

: Magariba  hart a danno,

: Kuma har yanzu banga Dodo ba,

: Sai mu ishe giwa gona,

: Haruna tashi ka huta maƙi gudu gwarzo.

 

Jagora: Maƙi gudu kawa hakin dawa koma,

: Ashe ɗan horo baya jin hwaɗa ko dai an yi,

: Ban hana sai a ɓata baki ba,

: Ai tubarakallah,

: Wadda ba tawa tsoho komi,

: Samu dai wanda na fi baki na ya roƙo,

: Ɗiya maza na kuriƙa da gaske ƙwazo,

: Ba wani saurayi ido gabakin banza ba,

: Ce ni da dama maƙi gudu gwarzo.

 

Jagora: Haruna na yi ma noma dawa bugun kurma bebe,

: Haruna na yi ma noman dawa bugun turun bebe,

: Godiya Bello matsoki godiya kai komai,

: Muhammadu mai shayi

: Ruwan zuma mamman anba,

: Sarkin hawa na ukku,

: Sarkin hwawan ciyaman,

: Ya biya yai man komi,

: Hajiya Bagobira A’ina,

: Hajiya bagobira A’i,

: Ai ta gwada ta hi ni bata saman hannu,

: Ai ita ta gwada tai yi ba saman hannu,

: Ai godiya maiki ka biyani dai-dai,

: Lawali gima,

: Lawali ya biyani dungul.

 

Jagora: Haruna mijin Dije ka baya ba,

: Haruna mijin binta sai duhu ya,

: Baban Azima,

: Baban Basira,

: Baban Basiru,

: Baban Talatu,

: Baban Auwali,

: Ina baban gwande sai duhu ya,

: Sannu da hwaman kashin daji,

: Hat yau sannu da dama maƙi gudu.

Post a Comment

0 Comments