𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman
Sunna akan kuɗin da
banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu?
Allah ya karemu daga aikata kuskure.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi
ya buɗe
account ɗin da
za'a dinga saka masa kuɗin
ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda
bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo
bayanta:
الَّذِينَ يَأْكُلُونَ الرِّبَا لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ الَّذِي يَتَخَبَّطُهُ الشَّيْطَانُ مِنَ الْمَسِّ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا إِنَّمَا الْبَيْعُ مِثْلُ الرِّبَا ۗ وَأَحَلَّ اللَّهُ الْبَيْعَ وَحَرَّمَ الرِّبَا ۚ فَمَنْ جَاءَهُ مَوْعِظَةٌ مِنْ رَبِّهِ فَانْتَهَىٰ فَلَهُ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُ إِلَى اللَّهِ ۖ وَمَنْ عَادَ فَأُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Wadanda suke cin ribã ba su tashi, fãce kamar
yadda wanda da Shaiɗan
yake ɗimautarwa
daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba
yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa´azi
daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'annan ya hanu, to yana da abin da ya shige,
kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta
madawwama ne. (Suratul-Bakara Aya ta 275)
يَمْحَقُ اللَّهُ الرِّبَا وَيُرْبِي الصَّدَقَاتِ ۗ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ
Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra
sadakõki.
Kuma Allah bã Ya
son dukan mai yawan kãfirci,
mai zunubi. (Suratul-Bakara Aya ta 276)
Annabi ﷺ ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da
wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito
a hadisi ingantacce.
Idan mutum ya amshi Interest ɗin Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da
niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana.
A zance mafi inganci zai iya amfani da kuɗin wajan yin aikin da zai amfani jama'a
kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za
su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba
dukiyarsa ba ce.
Wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na
wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.