Hukuncin Yin Fitsari A Tsaye

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah malam menene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko namiji a Musulunci?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da Bukhari ya rawaito cewa: "Annabi ya je jujin wasu mutane sai ya yı fitsari a tsaye" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi na 222...

    Tare da cewa duk hukuncin da ya zo dağa Annabi yana haɗa mace da namiji, in ba'a samu abin da ya keɓance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar da Allah ya yı mata.

    Yana daga cikin Ka'idojin sharia gabatar da wajibi akan abin da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba ta ingantuwa saida ita.

    Duk hadisan da suka zo cewa Annabi ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana A'isha wanda Hakim ya inganta, in da take cewa: "Duk wanda ya ce muku Annabi ya yi fitsari a tsaye kar ku gaskata shi" kamar yadda Nasa'i ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 29.

    Malamai suna cewa: za'a dau maganarta akan tana bada labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da ba koyaushe take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka'idoji a wajan malaman Usulul-fiqhi:

    Duk wanda ya tabbatar da abu za'a gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya buya ga wanda ya kore.

    Don neman Karin bayani duba: Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa'i 1\26.

    Allah ne mafi sani.

    Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nzqRq

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.