𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin zan iya
sayar da fatan layya ko wani abu na daga abin layyana?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Manzon Allah ﷺya ce: "Wanda ya sayar
da fatan layyarshi to ba shi da layya". Albaniy ya ingantashi.
Shaykh Muh'd
Saleh Al-Uthaimeen ya ce: "Haramun ne sayar da wani abu na daga abin
layya, nama ne ko waninsa, har da fata.
Kuma ba'a ba
ma mahauci/me pawa wani abu na daga layya a matsayin ladan aikinsa, domin yin
hakan kamar siyarwa ne.
أحكام الأضحية والزكاة/الفصل 6
Wallahu A'alam
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.