Ticker

6/recent/ticker-posts

Tun Da Na Samu Juna Biyu Na Tsani Jima'i Da Mijina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum mlm Dan Allah atemakamun da shawara Ina da ciki wata 5 amman tinda nasamu ciki kwata kwata natsani jima'i banasoma mijina ya taɓa ni musamman ya taɓa nono dina natsana daya fahimci haka seya dena semufi 1mouth bamuyi jima'i ba kuma senake ganin kaman Ina cutar dashi innayi niyyan zanbashi hakkinsa kuma kwata kwata ni bana sha'awah inkayyadema de mlm Ni haryanzu tun da nayi aure bansan daɗin jima'i ba saboda Ni ban taɓa realizing ba dama aurena watansa biyar ne kuma cikina ma watansa biyar bangane Ina da ciki ba se danayi 1mouth period dina bezoba nafara ciwon ciki toh asannane nasan Ina da ciki kuma nafarajin banaso yana taɓa ni tun auranmu zaman da muka yi nawata dayannam kafun nasan Ina da ciki duk wani wasa dazemun kafun jima'i zan ji nadan jike kaɗan amman da anfara inyayi sau ɗaya zekara se inji na bushe baruwa Sam senake gani kaman zena daukana ba cikakkiyar maceba nide mlm har zuwa yanzu kafun yashiga senaji zafi kullun kaman sake rufe kofan akeyi amman da zaran yashiga shikenam amman in yanatayi beyi realizing da wuriba senaji nagaji kuma nafarajin zafi zafi yanzu de mlm shawara nakeso kabani shin lfy ta qlau ne kokuma akwae abun da yake damuna kuma in akwae taya zan maganceshi zanbari sena haihune kokuma tun yanzu zanyi nagode🙏Allah yakara basira

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Gaskiya hakan da kike kuskure ne babba domin Zaki sa mijinki ya Fara biye biyen Mata idan Kuma Yana da Hali zai tunanin qara aure, akan haka gaskiya sai kin yi haquri kin daure kina bashi kanki dan ya biya buqatarsa idan Kuma kinqi toh ke kika jayo kuma Duk abin da yabiyo baya lafinki ne kada ki zargi mijinki, ki zargi kanki.

Sannan kina cutar da kanki da kanki da Kuma Ɗan cikinki domin saduwar daza'ayi dake ita zata qarami kuzari da karkashi sannan ɗan cikinki yasamu lapiya da kuzari da kaifin basira sabida maniyyin da ke shiga jikinki Zai anfaneki dake da bebinki Baki Ɗaya.

Sanan yakamta kisani Daman Duk sabuwar amarya bazata Fara Jin daɗin jima'i ba sai saduwar aure tabi jikinta ta Saba sanann zata Fara Jin daɗin da gamsuwa, Wasu matanma sai sun haihuwa sannan zasu Fara Jin daɗin saduwa  da wadatacciya ni'ima da Kuma daina Jin zafin saduwa, kada ki tada hankalinki lapiyar qalau garau.

Kuma Rashin son jima'i ga Mai juna biyu Daman gaskkiya halittane domin akwai matan da zarar sun Sami ciki toh gaba Ɗaya zasu daina son jima'i hatta  sha'awarma basaji so wanann ba matslaa bane halitttarki ne kina haihuwa Zaki dawo daidai sai kinzo ma kina bin mijjnki da kanki yana cewa na gaji, lokaci ne Yana tafe.

Amma yana da kyau ga ma'aura sudinga sadaukarwa akan abin  da abokin zamanka yakeso sai dai idan da larura ko rashin lpiya, ko kuma, likita yace a dan saurara saduwa sabida wani dalili wanan Kuma ba yadda zakayi tun da ba lepinka bane larurace.

Wanann zamanin da muke ciki ya wuce Duk tunanin Mai tunani Duk wacce take Hana mijjinta kanta cutar kanta takeyi domin wllh kina kallo wata zata qwace Miki shi ko bai aureta ba toh zata rage Masa nauyi Kinga kuwa kice da sorry, wllh Mata kuyi hattara Kan haqin mazanku zakuyi jifan  gafiyar Baidu, Allah ya sawwaqe.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments