Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Namiji Mai Dukan Matarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

malan ina da tambaya mijina kullum idan muka yi faɗa saiya dinga duka na, koyaya  na batamai rai sai duka, yamai Dani jaka sai idan dare yayi sai yace Yana bukatata sabida ya kasance me bukata malan menene  hukuncin wannan auran. Nagayama iyayena sunce yadena duka Amma dukda haka bai bari ba Malan menene mafita Dan Allah, Wlh malan komai kankantar laifi sai duka zagi yayitamun masifa mutane naji. Dan Allah menene mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Tabdi! Duk Macen da ta tsinci kanta a gidan namiji mai duka tofa sai tayi hakuri kan hakuri. Domin wani ya mai da kumatun matarsa kamar kumatun wani kato, sai dai kawai kaji ya falleta da mari, ya tadiyeta yayi ta dukanta kamar baiwarsa shi ko kunya ma ba ya ji.

Yazo a Hadisi Annabi  Yace "Shin dayanku baya jin kunya ya duke matarsa kamar yana dukan baiwa, zai duketa da rana sannan ya nemi saduwa da ita a karshen dare shin baku jin kunya". Don haka ba komai bane matar ka za ta yi maka kayi ta dukanta, kayi mata targade ka kumbura mata jiki wata ma har tana zuban jini saboda mugun dukan mijinta. Ba'a kwana biyu ba tare da ya lallasa matarsa ba.

Allah Maɗaukakin Sarki ke cewa:

 ... وَاللَّاتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَاهْجُرُوهُنَّ فِي الْمَضَاجِعِ وَاضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيرًا

"Matayen da kuke tsoron saɓawarsu, to ku yi masu wa'azi, ku qaurace masu a shimfa, ku dake su, amma idan suka yi maku biyayya kada ku nemi hanyar cutar da su, lallai Allah Ya kasance Mai ɗaukaka ne Mai girma. (Suratun Nisá'i aya ta 34.)

Malaman Tafsiri sun nuna cewa waɗannan matakai guda uku su ne miji zai bi wurin mu'amala da matarsa a lokacin da ta saɓa wa umurninsa ko umurnin Allah, wato da farko zai fara yi mata wa'azi da nasihohi ne, ba sau ɗaya ba, a lokuta mabambanta, idan ba ta gyara ba sai ya qaurace mata a shimfiɗa, wato ya daina kwanciya da ita, idan duk ta qi gyara halinta bayan waɗannan matakai guda biyu, to yana iya dukanta amma ba duka mai cutarwa ba, kamar yadda malamai suka bayyana a Tafsirai. Amma wasu malaman sun ce barin dukan ya fi, duk da kasancewar addini ya ba da damar a yi.

Kaɗan daga cikin Shawarar da zan baki a nan 'yar'uwa shi ne, Fushi da zafin zuciya da ɓacin rai shi yake jawo namiji ya daki matarsa, don haka idan yace wance kibar kaza kiyi kokari ki bari, idan yace wance ayi mun kaza yi sauri ki tashi kiyi masa. Ki ɗaure wurin kaucewa abin da zai jawo ya duke ki.

Sannan wani lokaci kace nace shi yake janyo namiji ya kaiwa mace duka, don haka idan yazo yana fada yana zagye zagye kice wane nasan abin da nayi ban kyauta I'm sorry, Allah ya huci zuciyar ka, daga nan kiyi shiru yayi ta fadansa, domin kada yazo garin tanka masa ya faffaleki da mari.

Sannan iya magana, idan mijin ki bahagon namiji ne tofa sai kin iya magana ta yadda da yazo yana fadan nan sai ki kalallame shi da sanyayan kalmomi, kiyi taushi kiyi sanyi ki zama kamar kankara. To idan mai tausayine sai kaga yayi shiru ya daina fadan. Don wasu kwata kwata basu iyawa namiji mai zafi sanyayan kalamai ba.

Sannan ki dage da addu'a, domin gaskiya rayuwar auren ba zai rinka yi miki daɗi ba, tun da wanda ya kamata yasa kiji daɗin shi ne kuma yake kilarki. Ina rokon Allah ya gyara tsakanin ko wacce mace da mijinta mai irin wannan halin.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments