𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mallam yaya akeyin sallah walaha kuma su wani
surori ake karantawa dakuma lokacin da za'ayi sallah
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Sallar Dhuha ita ce Bahaushe ke ce mata
"Walha. Sallar Walha sunnace mai karfi wadda aka kwadaitar akan kowane
musulmi ya raya wannan Sallar domin dacewa da abu biyu koyi da Manzon Allah ﷺ da bin Umarnin da kuma dacewa da falala
da lada mai yawa.
●بن باز رحمه الله:-
Yana cewa:- "Sallar Walha sunnace ta Manzon
Allah ﷺ mai
karfi wadda ya aikata ta kuma ya kwadaitar da Sahabbansa akan aikita ta".
Allah yana cewa:
وَالضُّحَى
Allah yana rantsuwa da Hantsi ko Walha idan Allah
yayi rantsuwa da wani abu to yana nuna girmama wannan abu da matsayinsa awajan
Allah".
Hadisan Manzon Allah ﷺ masu yawa sunzo masu bayyana falalar
sallar Walha, ga kaɗan
daga cikinsu;-
1- Yazo acikin Hadisil Qudsy, Allah mai girma da
Buwaya yana cewa:- {Ɗan Adam, kayi min Raka'o'i guda huɗu a farkon yini, zai isarmaka wannan yinin
zuwa karshensa}
@أخرجه الترمذي (475).
"Wannan yana bayyana mana dukkan wanda yayi
sallar Walha raka'a huɗu a
farkon yini to Allah zai isar masa zuwa karshen yinin da kariyarsa da
taimakonsa na musamman".
الطيبي رحمه الله تعالى:
Yana cewa; An isar maka al'amuranta da
shagulgulanka da baka kariya da kiyayeka daga abin ki bayan sallarka ta Walha
har zuwa karshen yini,......".
@تحفة الأحوذي :2/478
2- Manzon Allah ﷺ yana cewa; (Jikin mutum akwai gabobi guda
360, kuma an dora masa yin sadaka akan kowace gaɓa) sai Sahabbai suka ce masa:
"Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon
Allah ??" sai Yace;
(Goge majinar ko kakin da akayi a masallaci, ko
dauke wani abin cutarwa daga akan hanya, idan kuma mutum bai sami damaba, to
yayi sallah raka'a guda biyu na Walha ya isar masa)
@الألباني رحمه الله ,صحيح الترغيب
3- Manzon Allah ﷺ yana cewa;
(Babu mai kiyaye Sallar Walha sai bayin Allah masu
yawan komawa zuwa ga Allah, sallar Walha sallace ta bayin Allah masu yawan
konawa zuwa ga Allah)
@صححه الألباني رحمه الله.
Mafi karancin Sallar Walha raka'a biyu, amma bata
da adadi wajan yawanta ko nawa ka iya ne, amma wasu Malaman sun tafi akan mafi
yawanta shine raka'a Takwas kamar yanda Manzon Allah ﷺ bai wuce raka'a takwas ba kamar yanda
Hadisin Ummu hany R.A ta ruwaito.
Lokacin Sallar Walha yana farawane daga fitowar
rana ta ɗan
daga kaɗan
kamar bayan fitowar rana da minti 30 zuwa 45am har zuwa gab da zawalin rana
daga tsakiya da yan mintina biyar.
@ابن عثيمين مجموع الفتاوى (14/ 306))
Wato kamar; "Daga karfe 7am zuwa 11:45am.
mafi falala da alkhairin lokacin yin Sallar Walha,
shine lokacin da rana ta fara zafi sosai, lokacin da mutane sukafi shagaltuwa
da aiyukansu na yau da kullum, kai kuma sai ka shagaltu da gani da Ubangijinka,
gab da zawalin rana.
@اللجنة الدائمة (6/148)
بن باز رحمه الله:-
Yana cewa; "Abinda yafi muhimmanci shine idan
mutum yana da damar yinta a lokacin mafi falala to yayi amma idan baya da dama
to yayita a farkon yininsa, amma yinta lokacin da rana tafara zafi sosai
yafi".
Daga Nana A'isha رضي الله عنها
tace; Manzon Allah ﷺ yayi
Sallar wallaha, sannan yace;
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ, ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ , ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
"ALLAHUMMAGH FIR LI,WA TUB ALAIYA, INNAKA
ANTAT TAUWABUR RAHEEM" har sai da ya fadi hakan sau 100.
@رواه البخاري رحمه الله في اﻷدب المفرد وصححه الألباني رحمه الله حديث رقم
619.
●ابن عثيمين رحمه الله
Yana cewa: "Sallar walha idan lokacinta ya
wuce to ta wuce ba'a ramawa domin Sallah ce mai lokaci kayyadadde".
●ابن باز رحمه الله:
Yana cewa: "Sallatul Ishraki wato Sallar
hantsi itace sallar walha afarkon lokacinta, kuma sunnace ta kowace rana".
Allah ka bamu ikon kiyaye wannan sunnah mai girma.🤲
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
SALLAR WALHA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, ina so a yi min bayani kan sallar
Walha. Sannan yaushe ne lokacin wucewarta? Na gode Allah saka maka da alkairi,
ameen.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Sallar Dhuha ita ce Bahaushe ke ce mata "Walha".
Kuma ita ce Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya yi mata laqabi da sallar masu
tuba (صلاة الأوّابين) a wani hadisi,
sannan ita ce wasu malaman suke kiranta da suna Salatul Ishraq (صلاة الإشراق), an kira ta da
wannan sunan ne saboda sai bayan rana ta ɗago
ake yin ta. Kuma sunnah ce ba farillah ba. Amma tana da falala mai girma.
Sallar Walha tana cikin sallolin nafila mafi falala wadda
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yayi a aikace kuma ya Kwaɗaitar akanyinta, sunnace
mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da yake
kiyayeta hatta a lokacin Bulaguro".
Farkon lokacin sallar Walha yana farawa ne daga lokacin da
Rana ta kammala ɗagowa
har zuwa kusa da kafin zawali, wato kusa da kafin lokacin Azuhur ya shiga,
kamar yadda Sheikh Ibn Uthaimeen da wasu malaman suka kimasta. Duba Assharhul
Mumti'u 4/88.
Amma mafificin lokacin sallar walha shi ne kamar yadda
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa
cewa: “Lokacin sallar walha lokacin da ‘ya’yan raquma suka fara jin zafi ne”
Muslim 748. Wato lokacin da rana ta riga ta ɗau
zafi.
Lokacin sallar Walha a kasarmu (Nigeria) shine daga Karfe
tara (9:00am) Zuwa karfe sha-ɗaya
da rabi (11:30am) Na Safe. Zakayi sallar a ɗan
wannan Tsakanin. Ana yinta ne a Lokacin da Akasarin Mutane Suka Gafala Akan
Harkar Duniya. Domin a Daidai lokacin ne yan Kasuwa Suke Fita kasuwarsu kuma a
irin wannan Lokacin ne Zakaga Yan Kasuwa sun Gafala da harkar cinikayya da kuma
saye da Sayarwa, Wasu Kuma Sun Tafi Wajen aikinsu na gwamnati da dai Sauransu.
Ibn Usaimin Rahimahullah Yana cewa: "Sallar walha idan
lokacinta ya wuce to ta wuce ba'a ramawa domin Sallah ce mai lokaci
kayyadadde".
Imamu Maliku Ya Rawaito a Cikin Muwadda cewar Mafi Akasarin
Raka'o'inta shine 8, ko dai kayi 2 ko 4 ko 6, idan kayi da Yawa Kayi Raka'a 8.
Amma ba'a Wuce Raka'a 8 ɗin.
Babu wata Surah da Aka keɓance
a karanta a Sallar Walha. Zaka Iya Karanta Kowacce surah.
Kaɗan
daga Falalar Sallar Walha Shine. Ka Fanshi kanka a Wajen Allah a wannan yinin,
zaka sami kusanci ga Allahu Subhanahu Wata'ala, Allah zai Ɗaukaka
Darajarka, Uwa Uba Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce: sallar
mutanen kirki ce, masu maida lamiransu ga allah ko kace sallar mutanen Allah.
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa; (Jikin
mutum akwai gaɓoɓi guda 360, kuma an ɗora masa yin sadaka akan
kowace gaɓa) sai
Sahabbai suka ce masa: "Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon Allah
(Sallallahu alaihi Wasallam)?" sai yace; (Goge majinar ko kakin da akayi a
masallaci, ko ɗauke
wani abin cutarwa daga akan hanya, idan kuma mutum bai sami damaba, to yayi
sallah raka'a guda biyu na Walha ya isar masa)
@الألباني رحمه الله,صحيح الترغيب
Allah ne mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
1 Comments
Allah Yasaka Da Alkhairi
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.