Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Hallata Na Yiwa Wani Ɗawafi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam yayata ta jidda ta ce in tambaye ka mene ne hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma wai don Allah ka amsa a facebook, saboda ana buƙatar sanin amsar.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam To ‘yar’uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba’a samu magabata na ƙwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba’a yin ta sai da dalili daga Alƙur’ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu’a lokacin da mutum yake yiwa kansa dawafi.

Akwai dalilai da yawa waɗanda suke nuna ingancin yiwa wani Umara ko Hajji, saidai ba’a samu na dawafi a karan kansa ba.

Kiyasin dawafi a kan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka haɗa jiki da dukiya, duk ibadar da ta haɗa jiki da dukiya, tana amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah.

ALLAH NE MAFI SANI

Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta: 87

Amsawa🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.

KU BIYOMU A TELEGRAM:

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

KU BIYOMU A FACEBOOK👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments