𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, Allah ya ƙara wa malam lafiya da imani, malam tambayata ita ce shin
mutum zai iya yin sallah da lalle a kansa, kuma zai iya yin sallah bayan ya
sanya tafarnuwa a al'aurarsa? Na gode sosai Allah ya ƙara taimakonmu ya azurta
mu da kyakkyawan ƙarshe.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
salám, ƴar
uwa lalle ba najasa ba ne, idan mace ta yi sallah da shi a kanta ko a jikinta
sallarta ta yi, amma dole ta kasance ta yi alwala ne kafin ta sanya lalle ɗin, amma kuma duk da haka
ta yi abin ƙyama.
In da ace lalle najasa ce to da zai zama sallarta ba ta inganta ba sai ta sake
yi
Bai kamata
mace ta sa lalle a lokacin sallah ba, abin da ya fi kyau ta bari sai dare ya
yi, bayan sallar Isha'i sai ta sa lalle ɗin
a jikinta, kafin Asubahi ya bushe ta cire shi. Haka nan sallarta ta yi ko da ta
sa tafarnuwa a al'aurarta saboda maganin wata cuta, saboda ita ma ba najasa ba
ce, yin sallah da abu mai najasa a jiki shi ne ke ɓata sallah.
Allah S.W.T ne
mafi sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.