𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaika malam don Allah ya halasta in yi Kitso da wiwi? Ma'ana in sa shi a cikin
man kitso.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu. Ya tabbata a hadisi cewa Manzon Allah ﷺ
ya ce: Duk abu mai sa maye giya ce, duk abu mai sa maye haramun ne. Kamar yadda
Albukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta (2003).
Wiwi kuma yana
daga cikin abubuwan da ake hukunta su a matsayin kayan maye, don haka ita ma
giya ce, hukuncinsu ɗaya
dai-dai-wa-daida. Sannan Allah Ta'ala a cikin Alƙur'ani ya bayyana giya a matsayin najasa
ce a aya ta (90) da ke suratul Ma'ida.
Malamai sun yi
saɓani a game da
najasar da ake nufi a wannan aya, wasu malaman suna ganin siffanta giya da
Allah ya yi da najasar da ke wannan aya tana nufin najasa ce ta ma'ana ba ta haƙiƙa ba,
don haka suke ganin ko da giya ta taɓa
jikin mutum ba dole ne sai ya wanke ba, saboda su a fahimtarsu ba najasa ce da
idan ta taɓa jikin
mutum sai ya wanke ba.
jumhur ɗin malamai kuma suna da
fahimtar duk wanda giya ta taɓa
jikinsa dole ne sai ya wanke hannunsa domin najasa ce ta taɓa jikinsa, saboda a
fahimtarsu ita giya najasa ce ta haƙiƙa ba ta ma'ana ba. Kuma wannan fahimtar
ita ce ke da rinjaye.
A bisa wannan
dalili, sai ya zama bai halasta a sanya wiwi a kai a yi kitso da shi ba, saboda
wiwi giya ce, giya kuma najasa ce, kuma ba ya halasta a shafa najasa da gangan
a jiki.
Don ƙarin
bayani a duba Fataawá Nurun Alad Darb (7/2), na Ibn Uthaimeen.
Allah Ta'ala
ne mafi sanin daidai.
Jamilu
Ibrahim, Zaria.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.