Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halasta In Bayar Da Kaina Ga Wanda Ba Musulma Ba Ta Yi Min Saloon?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Mallam tambayata ita ce mutum ne ya yi tafiya zuwa wani gari karatu sai ya zamana babu mai saloon musulma, shin christian din za ta iya mun?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, To malamai dai sun kasu kashi biyu game da irin waɗannan matsaloli na wacce ba Musulma ba ta yi wa Musulma saloon ko kitso.

Wasu malaman suna ganin bai halasta mace ta ba da kanta ga wadda ba Musulma ba ta yi mata kitso ko saloon, daga cikin dalilinsu kuwa ita ce aya ta 31 ta cikin suratun Noor, inda Allah Maɗaukakin Sarki ke cewa:

"KADA (MATA) SU BAYYANA ADONSU SAI GA MAZAJENSU, KO GA IYAYENSU, KO GA IYAYEN MAZAJENSU, KO GA ƳAƳANSU, KO GA ƳAƳAN MAZAJENSU, KO GA ƳAN UWANSU, KO GA ƳAƳAN ƳAN UWANSU (MAZA), KO GA ƳAƳAN ƳAN UWANSU (MATA), KO GA MATAYENSU...".

Daidai nan da Allah ya ce ko ga matayensu ɗin nan, to sai wasu malaman suka ce mataye Musulmai su ne kaɗai ya halasta mace musulma ta bayyana wa adonta, saboda matayen da aka faɗa a cikin wannan aya mata Musulmai ake nufi. Suka ce bai halasta ta bayyana wani ɓangare na jikinta da ba kowa da kowa ya halasta ta bayyanar wa ba ga wadda ba Musulma ba, kamar zira'in hannayenta da ƙwaurinta, da kanta, saboda haka sai suke ganin bai halasta Musulma ta buɗe kanta macen da ba Musulma ba ta yi mata kitso ko saloon.

Amma wasu malaman suka ce, ya halasta wadda ba Musulma ba ta yi wa Musulma kitso ko saloon da makamantansu, suka ce faɗin Allah cewa kada mata su bayyana adonsu sai ga matayensu, wannan matayen da Allah ya faɗa ba matayen Musulmi kawai ake nufi ba, ana nufin dukkan mata ne.

To bisa shawara ƴar uwa, duk lokacin da ya zamana ga Musulma ga wadda ba Musulma ba, kuma duka suna yin saloon ko kitso, to ki yi ƙoƙari ki ba Musulma ta yi maki, idan kuma babu Musulma, to ki ba wacce ba Musulma ɗin ba, saboda lalurar rashin Musulmar da za ta yi maki, saboda ki fitar da kanki daga saɓani.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments