Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin wasu alamomi ne ke nuna cewa mamaci ya cika da imani?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin wasu alamomi ne ke nuna cewa mamaci ya cika da imani kuma shin akwai wadanda za su shiga aljanna Ranar alqiyama ba tare da an yi musu hisabi ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Daga cikin alamomin akwai:

1.CIKAWA DA KALMAR SHAHADA: saboda faɗin Annabi "Duk Wanda maganarsa ta karshe ta zama La'ilaha illallahu zai Shiga aljanna".

2. MUTUM YA MUTU YANA AIKIN ALHERI: kamar sallah ko Hajji, saboda faɗin Annabi   "Ana tashin bawa akan abin da ya mutu yana yi".

3. IDAN MUTUM YA RASU DAREN JUMA'A KO YININTA: saboda faɗin Annabi "Duk Wanda ya rasu Daren juma'a ko yininta Allah zai kare shi daga azabar Kabari"

4. IDAN MUTUM YA RASU DA GUMIN GOSHISA: kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi .

5. Idan mutum ya yi shahada kamar mace ta mutu wajan haihuwa ko ciwon ciki ko nutsewa a ruwa ko ya mutu a ciwon Kwalara ko kare kansa ko dukiyarsa da sauransu.

Idan aka koma can cikin littafin Ahkamul Jana'iz Sheikh Albani yakawo alamomin a farko farkon littafin. Amma wannan ana kyautatawa mutum zatone ba'a yanke hukunci kai tsaye ace mutum ɗan aljanna ne ko ace kai tsaye ya cika da imani.

Manzon ALLAH () Ya ce: "Lalle za a samu masu shiga Aljanna a cikin al'umma ta mutum dubu Saba'in, babu Hisabi ko Azaba agare su, tare da kowani dubu ɗaya akwai mutum dubu saba'in da zasu shiga Aljanna.” [Saheeh Al-jami: 5366]

Abin da hadisin yake nufi: mutum Biliyan Huɗu da miliyan ɗari Tara (4.9B ko 4,900,000,000) Zasu Shiga Aljanna Babu Komai Salin Alin.

Waɗanda suke shiga aljanna babu hisabi sune waɗanda Annabi ya faɗesu acikin hadisi Ukasha binu Mihsan wato waɗanda suke basa camfi basa neman magani da sauransu.

ALLAH Yasa mu dace, Yasa muna daga cikin Al'ummar Annabi () waɗanda zasu shiga Aljanna ba tare da Hisabi ba (Aameen)

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments