Ticker

6/recent/ticker-posts

Rusau Babban Wa'azi Ne Ga Mai Hankali

Ni fa batun rusa shataletalen kwa'r gidan Gwamnati, ba abin da ya ja hankalin mutane ne ya ja nawa hankalin ba. Kun san me ja min hankali?

Daren da za a rushe shi na wuce ta jikinsa a kan hanyar zuwa na gida amma ko ƙiris ban tsaya na yi masa kallon bankwana ba.

Sai ji na yi washe gari anai masa kukan mutuwa an tashe shi daga aiki, har abadan abada kuwa.

Kwatankwacin abinda ya faru ke nan da ginin da aka rusa a Filin Sukuwa. Shi wannan na kalle shi a daren da za a ruguza shi.

Wajen karfe 10 da y'an kai na dare na wuce har nake cewa a zuci kawai an samu filin sikuwa a yankarwa wani ya gina ofis mai kyau a wajen.

Na ce ko da shike ai ƙawata garine tunda filling ba komai ake yi da shi ba mai yiwuwa nan gaba ma duk layin a gine shi haka. Ashe...

Gari na wayewa shi ma na gani a Fesbuk an rushe shi matasa sun farwa wajen suna ta kwasar "ganima"! Na yi salati cike da mamaki.

Ashe ganina na ƙarshe ke nan da ginin. Shi fa ke nan har abada sai dai wani ginin amma ba shi ba. To ni "Kullu man alaiha fan!" na gani.

Wato sau da yawa muna tare da wasu mutane ko wasu abubuwan da suke da muhimmanci ko tasiri ko ma'ana a rayuwarmu amma ba mu damu da su ba don ko kallon kirki ba ma yi musu.

A ganinmu ko da yaushe za su kasance suna nan suna jiran sanda muka shirya kula su ko mu'amala da su ko neman kallonsu ma don mu nishadantu, kawai bagatatan sai wani abu ya faru mu zo mu neme su mu rasa.

Wannan ba karamin darasi ba ne ga dukkanmu wAllahi. Sau nawa hakan na faruwa gareka ko gareki? Kullum ka na sa rana ki na cewa bari sai gobe ba yanzu ba sai an jima can ba zato ba tsammani sai ka ji mutum ya rasu. Ba shi ba sake dawowa duniya.

A sannan ne za ka soma tunanin abubuwan da ka so ku yi tare kika so ki gaya mata kuka so ku nema a wajensa kuke son a ba ta da dai sauransu amma ina kun yi sake dama ta kufce muku.

A sannan ne kunci da takaicin yin jinkiri zai tayar maka da hankali ba kaɗan ba wAllaahi. Duk kuwa abin da za ka yi don gyatto al'amari ba zai yiwu ba ka na ji ka na gani ba an wuce wajen.

Don haka kowa ya yi hattara ya yi abinda ya kamata na kyautata mu'amalat da kowa da kowa ya sada zumunci ta kira ta bada hakuri a daidaita tsakanin juna a yafewa juna a nemi gafara da daɗaɗawa juna tun kafin mai aukuwa ya auku a zo ana da na sani.

Ni dai kun ji abinda wannan rusau ɗin ya nusar da ni. Don haka ina wane (.....) ya ke? Zan so mu gana don in roke shi gafara na yi masa laifi. Ina kuma wacce nake son in sanar da ita ina mutuwar sonta da aure kar in je mu gamu da fuju'a ban gaya mata ba... 💙😍💖

Sai wa kuma? Ina wane ya ke ne? Wai ya batun kuɗina da ke hannunsa ne? Ba zai biya ni ba ne sai na mutu ko? To ka sani magada za su zo neman haƙƙinsu kar dai ace da su an biya ni! Ba ka biya ni ba! Ehe!

©2023 Tijjani M. M.

Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

Post a Comment

0 Comments