Ticker

6/recent/ticker-posts

Hattara Jama'a Ragon Layya Na Nema Kuɓuce Mana Fa

Hattara Jama'a Ragon Layya Na Nema Kuɓuce Mana Fa

Ƙarfi da yaji fa nema ake a zamanantar da aure. Kuma alamu na nuna cewa kullum abin daɗa lalacewa zai yi indai aka biyewa wannan tafarkin shagalar. Yanzu ma abin ya soma ta6ar6arewa yana daɗa sukurkucewa.

Manzonmu SAWS ya ce in mutum ya zo neman aure a hannunku wanda addininsa da dabi'unsa suka yi muku to ku aura masa y'arku. In kuka ƙi yin haka, to fitinah da fasadi ne za su wanzu a doron ƙasa.

Sannan ya sake nusar da mu cewa a sauƙaƙa a tausayawa a tallafi juna wajen yin aure don auren zai yi kyau ya yi ƙarƙo ya kuma yi albarka. Sai dai maimakon yin hakan, mun biyewa son zuciya da ganganci sai hana aure muke yi. Ga shi yanzu mun tsinci kanmu a halin ƙaƙanakayi.

Da farko dai mun ce ƙwarya ta bi ƙwarya wato talaka ya auri talaka, mai kuɗi sai mai kuɗi. Wanda wannan ya sa talauci ya samu gurbin zama ya yi katutu a cikin al'umarmu. Kun ga wannan yana ɗaya daga cikin abubuwa da ke hana mutane da yawa aure.

Sai ka ga masu kuɗi suna facaka iya son ransu a wajen hidima da shagalin biki don kece raini, a ya yi da talakan ango ke neman kashe kansa don yin lefe. Su kuma iyayen amarya sun kasa yiwa y'arsu kayan ɗaki. Aure nawa aka ɗaga ko aka fasa saboda wannan dalilin?

Ko kuma ace kyakkyawar mace, fara, doguwa girkin manya ce don haka ahir ɗin matashi ko talaka ya nemeta da aure. Alhali kuwa arziƙi na Allaah ne kuma Ya yi busharar arzurta bayinSa muddun za su yi auren da kyakkyawan zato. Guda nawa Ya yi kuma mun gani?

Ban da lefe da kayan ɗaki, ga yinin biki da yin gara da suka damu kusan kowa, yanzu Kuma sai ga shi an shigo da wasu sabbin badaƙala irin su kama "Event Center", gayyatar mawaƙan da taurarin Kannywood, bada kyaututtuka (subiniya), yin anko da dai ƙarerayi kalakala.

Duka wannan fa ba su isa ba sai aka ƙirƙiro wasu sabbin sana'o'i ta yiwa amare kwalliya (makeup), aka shigo da masu bada umarni a fagen biki (MC), ga masu ɗaukan hoto da bidiyo, ban da masu yiwa wajen taro kwalliya (dakwareshan), sai y'an shafa labari shuni.

Kowanne fa a cikin waɗannan sharholiyar kuɗi za a tanadar don gudanar da su kuma angon da iyayen amarya kowa da kasonsa a waɗannan jidali. In aka yi rashin sa'a akan abu ɗaya daga cikin waɗannan almubazarancin sai ka ga an fasa auren ko kuma zumunci ya lalace.

Ban fa yi zancen su dilka da lalle da kitso da ire-irensu ba. Kar kuma a yin zancen gidan da za a zauna. Ango daga zaman shago a kofar gida a sa shi ya kama hayan gida mai ɗaki uku kan kuɗi dubbai a sabuwar unguwar da ba tsaro ga shi bai da ko abin hawa.

Fi sabilLaahi ya za a yi aure ya kai da bantensa an yi shi a cikin irin waɗannan tsarabe-tsarabe, takura da ƙunci? Ba dole y'an mata su kasa auruwa ba. Ba dole zawarawa su cika gari ba. Ba dole zina, luwaɗi da maɗigo su fantsu su yi yawa a tsakaninmu ba.

Annabi Muhammad SAWS ya yi gaskiya wAllaahi. Kuma ya yi mana kashedi da jan kunne amma da yawa muna gani bai iya ba mu muka iya. To sakamakon rashin yi masa biyayya wa ke kwana a cikin tashin hankali, takaici da tashin-tashina? Al'umarmu. Yan mata, samari da iyaye.

To ina mafita kuma me ye abin yi?

In muka lura da kyau Annabi SAWS ya bamu wasu sharuɗa don tabbatar da cewa linzamin aure bai ƙwace mana ba a al'umance. Kamata ya yi mu koma kan tafarki madaidaici. Mu sawwakewa kan mu yin aure. Mu kakka6e duk wata bidi'ar da ta shafi aure kuma take Mana illa akai.

Kuma lallai ilalla kowa ya nemi sana'a sannan a auri mata 2, 3 ko 4 amma wanda ba zai iya adalci tsakanin su ba ya haƙura ya yi zamansa da mace ɗaya. Hakazalika duk wani mai laruwa ko ra'ayi ba a ce dole ba ya zauna da mace ɗaya Allaah SWT Ya albarkaci zamansu lafiya.

Daga ƙarshe kira za mu yi da a yi hattara a kiyayi kasancewa kamar mutumin da ya yi sake ragon layyarsa ya ku6uce masa a ranar Idi ko ranar yanka aka zo ana a tara a tara ragon ya kasa kamuwa ya gudu aka kama ana cigiya ba a gan shi ba aka zo ana da na sani. Don da alamu mun doshi wajen.

Allaah dai Ya kiyaye, amin.

©2023 Tijjani M. M.

Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

Post a Comment

0 Comments