Matsayin Rubutacciyar Waƙa Jiya Da Yau:
Assalamu alaikum, 'yan uwana marubuta da manazarta wakoki. Ina taya mu murna da zagayowar wannan rana ta: 21-03-2021, wato RANAR RUBUTACCIYAR WAƘA TA DUNIYA.
Kamar yadda aka sani, wannan rana, majalisar ɗinkin duniya ta kebe ta ne
domin yin bitar matsayin rubutacciyar waƙa: Jiya da yau da makomarta gobe.
Bahaushe ya fara dandanar zakin rubutacciyar waƙa tun
a wajen karni na 17. A wannan karni an sami rubutattun wakoki kamar na: Shi'ir
Hausa da Jamuyah dukkansu na Sheikh Ahmad Tila. Sai Tarihi El-Sudan, ita ma waƙa ce
ta Hausa da sunan Larabci ta Sheikh Abdulkadir Tafa.
Duk dai a karni na 17, an sami wakoki irin na su: Wali dan
Masani da Wali dan Marina a Katsina. Da sauransu.
A karni na 18, an ci gaba da samun marubuta wakoki irinsu:
Malam Muhammadu Bn. Muhammadu al-Katsinawi wanda ya shahara a wajen shekarar
1732.
A karni na 18 zuwa na 19, an sami bunkasar marubuta wakoki
irinsu: Malam Muhammadu na Birnin Gwari 1758-1878. Wanda yana daya daga cikin
wadanda ake alakanta shahararriyar waƙar nan ta GANGAR WA'AZU, zuwa gare shi.
Sannan akwai Shaihunnan Malamai irinsu: Malam Shitu dan
Abdurra'uf mawallafin waƙar Jiddul ajizi Ba'ajamiya, da Jimiyya, d.s.
Haka nan akwai wakokin madahu na masu jihadi irinsu: Shaihu
Usmanu bn. Fodiyo da kaninsa Abdullahin Gwandu da dansa Muhammadu Bello, da
Nana Asma'u da autansa Isan Kware, da sauransu.
A karni na 19 zuwa na 20, an sami fitattun marubuta wakoki
kamar su: Sarkin Zazzau Alu dan Sidi, da (DR) Aliyu na Mangi da (DR) Akilu
Aliyu da (DR) Alkali Bello Gidadawa da (DR) Mudi Sipikin, da Mal. Ummarun
Gwandu, da Malam Sa'adu Zungur a Bauchi, da Malam Mu'azu Hadeja da Abubakar
Ladan Zariya da sauransu.
A sakamakon kwazo da nuna kishi da kwazo na wadannan
Shaihunnan Malamai, an sami habakar rubutacciyar waƙa a kasar Hausa.
Rubutacciyar Waƙa A Yau:
A karni na 19-20, rubutacciyar waƙa na kamshin turare dan
goma. Bayan tumbatsar marubuta wakoki da aka sami, akwai litattafai da
wallafe-wallafe da suka shafi rubutacciyar waƙa da dama.
Misali, irinsu wakokin Imfiraji, da Fasaha Akiliyya, da
wakokin Mu'azu Hadeja, da Sababbi da tsofaffin wakokin Mudi Sipikin, da Baje
Kolin Hajar Tunani na Alkali Bello Gidadawa, da wakokin Sa'adu Zungur, da
wakokin Hausa, da sauransu.
Amma maimakon a karni na 21, a ce rubutun litattafai ya yi
tashin gwauron zabo, sai aka sami ci gaban mai Hakim rijiya. Rubuce-rubuce sai
ya koma a kafafen Sada zumunta ko social media. Wannan ya kawo koma baya a
fannin nazarin rubutacciyar waƙa.
Misali, a sakamakon dukafa wajen nazarin rubutacciyar
wakokin magabatanmu, mun rabantu da samun Farfesoshi a fannin rubutacciyar waƙa
kamar su: 1. Farfesa Dalhatu Muhammad 2. Farfesa Dandatti Abdulkadir 3. Farfesa
Abdulkadir Dangambo 4. Farfesa Bello Sa'id 5. Farfesa Haruna Birniwa 6. Farfesa
A.B Yahya 7. Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa da 8. Magaji Tsoho Yakawada 9. Farfesa
Bala Usman 10. Farfesa Zulyadaini, da sauransu.
Kusan dukkan wadannan Farfesoshi na fannin rubutacciyar waƙa, za
ka ga ayyukansu, ya jibanci ayyukan marubuta wakoki ne mazan jiya.
Matsalolin Da Rubutacciyar Waƙa Ke Fuskanta A Yau:
Zamani: A duk lokacin da wani abu ya yi tashin gwauron zabo,
ana da ran wata rana zai yo kasa.
Buga litattafai: Ta fannin buga litattafai, za ka iske kusan
dukkan litattafan magabata, kamfanoni ne suka buga su. Da wuya ka ji wani
marubucin waƙa
ya buga littafinsa da kansa.
Akwai kamfanoni masu buga litattafai irinsu: NNPC da Gaskiya
Corporation, da University Press da Alhudda-hudda da Amana da Ahmadu University
Press, da sauransu.
A yanzu wadannan kamfunan buga litattafai kusan in ce sun
daina karbar litattafai da suka shafi rubutacciyar waƙa domin bugawa.
A wannan karni na 21, litattafai da suka jibinci
rubutacciyar waƙa kalilan ne masu shi suka buga. Misali, Daurayar gadon fede waƙa, na
Farfesa Abdulkadir Dangambo, da Gadar zare na Dr. Awwal Anwar, da Salo asirin waƙa na
Farfesa AB Yahya, da Bayanin rubutacciyar waƙa na Farfesa Isa Mukhtar, da Nazarin
waken Hausa na Dr. Sulaiman A.S. Sarbi, da Guzurin marubucin waƙa na
Malam Nasiru G.Ahmad 'Yan Awaki sai Matakan Nazarin rubutacciyar waƙa na
Malam Sulaiman S.M.Mai Bazazzagiya.
Wani abin da ke ci wa rubutun rubutacciyar waƙa tuwo
a kwarya, shi ne rashin nuna goyon baya ga al'umma, da hukumomi.
A da idan gwamnati na bukatar fadakarwa, ko wayar da kan
al'umma a kan wani abu da ya shafi ci gaban al'umma, ana bukatar marubuta
wakoki su ba da tasu gudummuwa wajen rubuta kasidu a kan batun da ake bukata. A
yanzu ba a yin haka. A yau in ka ga haka, sai dai yabo ga 'yan siyasa.
A tarukan al'umma na cikin gari, a da a kan bukaci marubuta
wakoki su baje kolinsu. Wato su yi maraba da baki. A yanzu wannan ya yi
karanci.
A Jami'o'i kuwa, a da dalibai na da zummar nazatar
rubutacciyar waƙa. Amma a yanzu abin sai a hankali. Dalibai na guje mata
saboda sun shak'a cewa tana da wuya.
A jiya akwai gasa da Kungiyar Marubuta da Manazarta
Rubutacciyar waƙa ke shiryawa duk shekara. A karshen gasar ana ba da Kofi da
sauran kyaututtuka ga zakarun gasar. Wannan kan shajja'a mawaƙa wajen
dagewa na inganta wakokinsu.
Duk da yake a yanzu akwai yunkuri da ake yi domin farfado da
ayyukan da wancan kungiyar ke yi. A karkashin GAMAYYAR MARUBUTA DA MANAZARTA
RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA TA KASA, a bisa jagoranci Sulaiman S.M. Mai
Bazazzagiya.
Shawarar Yadda Za A Farfado Da Rubutacciyar Waƙa:
1. Kamfunan buga litattafai su dawo da karbar buga
litattafai na wakoki. Ko a sami wani sabon kamfani na buga litattafan Hausa.
2. Hukumomi su rika daukar dawainiyar buga litattafan Hausa masu
ma'ana. Kamar yadda ake yi a kasar Masar, da sauran kasashe. Wannan zai zaburar
da marubuta wakoki.
3. Jami'o'i da gwamnatoci su rika daukar dawainiyar shirya
gasar rubutacciyar waƙa. Ana ba da kyaututtuka ga zakarun gasar.
Alhamdulillah, a
yanzu wajen shekara hudu zuwa biyar, ana ta yunkurin karfafa ko inganta rubutun
kagaggun labarai. Akwai cibiyoyi da ke daukar wannan, kamar: B.B.C da Aliyu
Gusau Library, da gasar Dangiwa da na Darma Library, da gasar gajerun labarai
na Aminiya Trust da sauransu.
To a yanzu ya kamata a mayyazo zuwa ga rubutacciyar waƙa.
Kamar yadda aka sani ne, tubalan ginin adabin zamani uku ne: Rubutacciyar waƙa, da
Rubutun zube, da Wasan kwaikwayo.
Wadannan su ne tubala ko murahun adabin zamani. Idan ya
kasance a kullum ana ta gina kafa daya daga cikin murahun, sauran biyun na
zagwanyewa, ko an dora tukunyar ci-maka, ba za ta zauna. Dafuwar za ta tuntsure
ta kashe wutar murhun.
4. Marubuta wakoki su dage su hada kansu. Makwabcinka ko dan
kwadigo, ba za su maka kaftu, da noma, da cirbe, da girbi ba, a gonarka kamar
yadda za ka yi da kanka.
Godiya ga Malaminmu Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda bisa
jagorancinsa ne muke wannan tattaunawar.
Wata godiyar zuwa ga Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, bisa
gasar rubutattun wakoki da suka shirya a kan tsaro.
Ba za mu manta da gwamnatin jihar Bauchi bisa karrama daya
daga cikin magabatanmu, wato Malam Sa'adu Zungur. Na canza sunan Bauchi state
University, zuwa Sa'adu Zungur University.
Mun tattauna da Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dr. Aliyu
Tilde. Akwai shiri wanda suke yi na karrama marubuta wakoki a jihar Bauchi.
Muna matukar godiya bisa wannan albishir.
Daga:
Shugaban Marubuta Da Manazarta Rubutacciyar Waƙa ta Ƙasa
Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya
08067917740
21-03-2021
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.