An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964).
Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.
Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam
Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi
ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa
Kano.
Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a
shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda
asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh
Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara
ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai
girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci
daya a shekara ta 1980.
Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar
Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening
Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da
haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu.
Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan
makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen
larabcin da yamma.
Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983.
Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984,
kuma ya kammala a shekara ta 1988.
A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a
jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul
Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993.
Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala
karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take
Khartoum, Sudan.Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen
karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan
Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da
wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin
Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa.
Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin
masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar
Bayero ta Kano.
Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh
Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar
da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul
Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin,
Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy.
Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam
Rabi'u Umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah
Usman G/Kaya da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani da
Malam Ali Yunus Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da
Malam Anas Muhammad Madabo.
Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin
rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja'afar
Islamic Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar
juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan
ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a
masallacin Juma'a na Dorayi.
Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da
aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla
a kansa.
Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan
suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi.
Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da
gidan aljanna. Ameen summa Ameen.
Daga Taskar
Daga Aliyu Adamu Tsiga
©Zuma Times Hausa
1 Comments
Allah yaji kanshi da rahama Allah yasa nazama kamar malam Ameen
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.