A cikin wani version na Waƙar Sarkin Yaƙin Banga, Sale Abubakar mai amshi 'Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo ginjimi, gamshik'an Amadu na Maigandi kai a Uban Zagi' da aka yi recording nata a filin da Malamin Waƙa, watau Makaɗa Sa'idu Faru ya yi wata hira za a ji cewa Marok'insa na cewa "Hey, a saurara, mai magana Ɗan Ige Sarkin Shaggu..." har zuwa ƙarshen zancen, to wannan ne Ɗan Ige Sarkin Shaggu Gusau. Na ɗauke shi wannan hoto ne a Unguwar su da ake kira Birnin Ruwa, Gusau, Jihar Zamfara a Ranar 22/07/2017 shekara 6 Cif ke nan (22/07/2023). Ya zuwa yau ya nan raye, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
Daga Taskar
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.