Cite this article as: Muhammad, A. (2023). Nason Al’adu Cikin Adabi: Nazarin Abincin Hausawa Na Gargajiya A Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 159-166. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.018.
Tsakure
Hausawa suna da abincinsu na gargajiya iri daban-daban da suka gada daga iyaye da kakanni, waɗanda suka riƙe a matsayin cimakarsu ta yau da kullum. Babban muradin wannan muƙala shi ne, ta fito da yadda ire-iren abincin Hausawa na gargajiya ya yi naso cikin rubutattun waƙoƙin Hausan. An ɗora aikin ne a kan ra’in nason al’adu a cikin adabi. Bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu da muƙalu da fasahar sadarwa ta zamani suna daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattara bayanai na wannan bincike. A waƙoƙin da aka nazarta, an gano ire-iren abincin Hausawa na gargajiya iri daba-daban har guda hamsin da tara da suka yi naso cikin rubutattun waƙoƙin da aka yi nazarta.
Fitilun Kalmomi: Abinci, Al’ada, Adabi, Waƙoƙi
1.1 Gabatarwa
Kowace al’umma ta duniya da ke rayuwa bisa doron ƙasa sun keɓanta
da wasu nau’o’in abinci waɗanda suka riƙa a matsayin cikamar rayuwarsu ta yau
da kullum. Wasu daga cikin nau’o’in abincin akan cire su ne kai tsaye a ci,
yayin da wasunsu kuma sai an yi musu wata ɗawainiya kafin a ci. Sai dai kuma
abincin da wata al’ummar ta riƙa a matsayin cimakarta, ba shi wata al’ummar ta
riƙa ba. Ma’ana abincin da Larabawa ko Turawa ko Yarbawa ko Barebari ko Igbo
suka riƙa a matsayin cimakarsu, ba shi al’ummar Hausawa ta riƙa a matsayin nata
cimakar ba. Don haka ne ma, Hausawa suke cewa, abincin wani gubar wani. Wato
abincin da wani ya ci ya zauna lafiya, wani idan ya ci shi ba zai kwana lafiya
ba. Bisa wannan bayani za a iya fahimtar cewa, kowace al’umma tana da irin nata
abinci da ya keɓan ta da ita. Amma a dalili na cuɗanya da juna akan samu
musayar cimaka tsakanin wannan al’umma da waccan. Abin nufi, wata al’ummar
takan ari nau’in abincin wata al’umma kuma daga bisani ta mayar da shi tamfar
nata. Wannan dalili ne ya sa Hausawa suka tasirantu da nau’o’in abinci daga
wasu al’ummu daban-daban da ya bambanta da nasu na asali. Misali: fufu daga
nau’o’in abincin al’ummar Igbo. Teba daga al’ummar Yarbawa da alkubus daga
al’ummar Larabawa da kuma biski daga al’ummar Kanuri da sauransu. Ire-iren waɗannan
nau’o’i na abinci da wasunsu a yau sun shiga cikin rukunin nau’o’in abincin
Hausawa.
Masana da manazarta irinsu: Gusau (2009) da Magaji (2009)
Fatahiyya (2009) da Mu’azu (2006) da sauransu, sun gudanar da ayyuka mabambanta
a game da abin da ya shafi abincin Hausawa na gargajiya. Sai dai ayyukan nasu
sun yi hannun riga da wannan aiki ta wasu fuskoki kamar yadda za a gani nan
gaba. Kafin nan a muƙalar an kawo muradun bincike da dabarun bincike da ra’in
da aka dora aikin a kai da ma’anar abinci da matakan samun sa da nau’o’insa da
ajujuwansa sai kuma aka duba yadda wasu marubuta waƙoƙin Hausa suka kawo waɗannan
nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya a wasu waƙoƙin da suka rubuta.
1.2 Dabarun Gudanar da Bincike
Daga cikin hanyoyin da aka yin amfani da su wajen gudanar da
wannan aiki akwai: bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu da muƙalu
da kuma fasahar sadarwa ta zamani. sannan an kai ziyara ɗakunan karatu domin
kalato bayanai da ɗakunan suka tanada.
1.3 Ra’in da aka Ɗora Aikin a Kai
An ɗora wannan aiki ne a kan mazahabar ra’i ta Nason Adabi a
Al’adun Al’umma. Ita wannan mazahaba tana daidaita hikima ta isar da saƙo da
ma’ana ko ƙaramin saƙo ko harshen magana da ayyuka na gyara rayuwar al’umma ta
yau da kullum. Haka kuma mazahabar tana biyar sawun yadda al’umma take ƙoƙarin
bayyana abin da ya shafe ta (Gusau, 2015:49). Abincin Hausawa na gargajiya abu
da ya shafi al’ummar Hausawa don haka Hausawan ba su yi shiru a kansa ba, suke
ta ƙoƙarin bayyana shi cikin baitocin waƙoƙinsu. Wannan dalili ne ya sa aka yi
amfani da wannan ra’i wajen gudanar da aikin
2.0 Abinci Hausawa Na Gargajiya
Ƙamusun Hausa, (2006:1) ya bayyana ma’anar abinci da cewa:
“duk abin da ake ci don maganin yunwa”. A taƙaice za a iya cewa, abinci ya ƙunshi
duk wani nau’in abin ci ko sha sarrafaffe ko maras sarrafawa da akan yi amfani
da shi domin magance yunwa ko don yin maganin kwaɗayi.
2.1 Matakan Samun Abinci
Akwai matakai daban-daban da Hausawa suke bi wajen sama wa
kansu cimaka. Muhimman matakan su ne: farauta da noma da kiwo.
2.1.1 Farauta
Domin sama wa kansu abinci, Hausawa sukan shiga daji su
farauto namun daji su dafa su ci. Daga cikin ire-iren namun da sukan farauto
akwai: gada da bareyi da zomaye da kuregu da barewu da sauransu. Haka kuma,
sukan shiga ruwa domin farauto namun da ke cikin ruwa irin su: kifaye da
tsuntsayen ruwa da sauransu.
2.1.2 Noma
Bayan farauta har wa
yau, Hausawa sukan yi noma don samar da abincin da za su kai bakin salatinsu. A
shekara Hausawa sukan yi noma iri biyu: noman tudu da na kwari (noman damuna da
na rani). Mafi akasarin abubuwan da sukan shuka a lokacin damuna abubuwa ne da
suka danganci hatsi da dawa da maiwa da riɗi da wake da sauransu. A noman rani
kuwa, sukan shuka abubuwa ne da danganci mabunƙusa ƙasa da kayan haɗin miya da
alkama da shinkafa da sauransu.
2.1.3 Kiwo
Kiwo ma yana ɗaya daga cikin matakan da Hausawa sukan bi wajen
sama wa kansu abincin da za su ci. Daga cikin dabbobin da suke kiwatawa akwai: ƙananan
kamar kaza da agwagwa da talatalo da zabuwa da tunkiya da akuya da sauransu.
Sukan yanka ire-iren waɗannan dabbobi domin su samu naman da za su ci a yayin
da buƙatar hakan ta taso musu.
2.2 Ire-Iren Abincin Hausawa Na Gargajiya
Hausawa suna da ire-iren abinci daban-daban da suke amfani
da su wajen kashe yunwar cikinsu. A wannan takarda an kalli nau’o’in ne ta
fuskoki kamar haka: abinci mai ruwa – ruwa da abinci mai tauri da taɓa-ka-lashe
da tsirai da ‘ya’yan itatuwa.
2.2.1 Abinci Mai Ruwa-Ruwa
Wannan nau’i na abinci ya ƙunshi duk wani abin da za a ci ba
mai nauyi ba kamar: koko da kunu da fura da nono da fate-fate da rambo da
madara da sauransu. Abinci irin wannan yawanci akan sha shi ne ko a lasa.
2.2.2 Abinci Mai Nauyi
Shi kuma wannan nau’i na abinci ya bambanta da wanda aka yi
bayani a baya, domin shi irin wannan abinci ya danganci duk wani nau’i na abin
da za a ci mai nauyi kamar: tuwo da ɗanwake da tubani da waina da dashishi da
tsala da gurasa da sauransu.
2.2.3 Taɓa-Ka-Lashe/Maƙulashe
Shi kuma irin wannan abinci, ya shafi wani nau’in abinci da
ake ci don ƙwalama kamar nama da sauran abubuwan marmari irin su: tsire da
balangu da soye da ragadada da kilishi da daƙuwa da nakiya da tsattsafa da
gireba da kambusa sauransu.
2.2.4 Tsirai da ‘Ya’yan Itauwa
Wannan nau’in abinci kuma, ya ƙunshi duk abubuwan da za a
cira ba tare da an sarrafa ba a ci ko kuma a sarrafa a ci. Mafi akasarin wannan
nau’i na abinci akan shuka shi ne ko a dasa. Wannan kuwa ya haɗa da: ‘ya’yan
itatuwa da ganyayyaki kamar: zogale da rama da ingidido da yaɗiya da tafasa da
yakuwa da gwaiba da mangwaro da gwanda da kankana da lemo da aduwa da taura da
tsada da ɗinya da ƙwara/kaɗanya da sauransu. Sai kuma abubuwan da suka danganci
tsaba/ƙwaya irin su: gero da alkama da shinkafa da wake da gyaɗa da riɗi da
sauransu.
2.2.5 Mabunƙusa Ƙasa
Shi kuma wannan nau’i na abinci shi ne kamar irin su:
dankali da gwaza da makani da rogo da doya da sauransu.
2.3 Azuzuwan Abincin Hausawa
Hausawa suna da ajujuwan abinci daban-daban da suka haɗa da:
abinci mai gina jiki da abinci mai sa kuzari/ƙarfin jiki da abinci mai ba da
maiqo da abinci mai ƙara ruwan jiki da kuma abinci mai ƙara lafiyar jiki
2.3.1 Abinci Mai Gina Jiki
Wannan ya shafi ajin nau’o’in abinci kamar: nama da kifi da
wake da ƙwai da makamantansu.
2.3.2 Akwai Abinci Mai Sa Kuzari/Ƙarfin Jiki
Shi kuma wannan aji na abinci ya shafi nau’o’in abinci irin
su: hatsi da dawa da shinkafa da tuwo da rogo da dankali da makamantansu.
2.3.3 Abinci Mai Ba Da Maiƙo
Wannan kuma ya shafi ajin abinci ne kamar: gyaɗa da riɗi da ƙwara/kaɗanya
da makamantansu.
2.3.4 Abinci Mai Ƙara Ruwan Jiki
Wannan aji na abinci kuma, shi ne wanda ya shafi nau’o’in
ruwa kamar: ruwan rafi da na rijiya da na kogi da na wasu ‘ya’yan itatuwa da
makamantansu.
2.3.5 Abinci Mai Ƙara Lafiyar Jiki
Shi kuma wannan aji na abinci ya shafi nau’o’in abinci ne
irin su: zogale da rama da ingidido da salak da goruba da karas da yalo da
yakuwa da dabino da makamantansu.
3.0 Nason Abincin Hausawa Na Gargajiya cikin Rubutatun Waƙoƙin
Hausa
A nan an yi ƙoƙarin kawo baitoci ne daga rubutattun waƙoƙin
Hausa waɗanda suke ɗauke da ire-iren abincin Hausawa daban-daban da wasu
marubuta waƙoƙin Hausa suka ambato. Kamar yadda aka yi bayani a baya, Hausawa
suna da ire-iren abinci da suka danganci ruwa-ruwa da masu nauyi da maƙulashe
da kuma ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa. Ire-iren waɗannan nau’o’i na abinci ne
aka zaƙulo daga wasu baitoci na wasu rubuattun waƙoƙin Hausa, aka yi tsokaci a
kansu tare da bayanin ajin kowannensu. Misali: Mu’azu Haxeja a cikin waƙarsa ta
Tutocin Shaihu da Waninsu, ya kawo tuwo da miya. Duba abin da yake cewa a
wannan baiti da ke ƙasa:
Abin ga ko da gaskiya,
Kura ta iske tunkiya,
Ta ce su je su tsariya,
Akwai tuwo akwai miya,
Su yi shagali na duniya”
(Waƙar Tutocin Shaihu da Waninsu, bt.52)
Idan aka duba ɗango na uku, za a ga mawallafin ya ambato
tuwo da miya waɗanda dukkansu nau’o’i ne na abincin Hausawa. Tuwo na ɗaya daga cikin
ire-iren abincin Hausawa da ya danagnci nau’in abinci mai nauyi. Sannan yana ɗaya
daga cikin ajin abinci mai sa kuzari. Ita kuwa miya mahaɗi ce ta tuwo. Wato
tuwo ake gutsira a dangwali miya sannan a ci. Saboda haka, ita ta danganci
nau’in abinci ne mai ruwa-ruwa.
Haka shi ma Malam Salihu Kwantangora a cikin waƙarsa ta Hana
Zalunci, ya ambato wannan nau’i na abincin Hausawa. Duba wannan baiti da ke ƙasa:
“Kwasshaƙe ciki da tuwon zulmu,
Zai ɗibgi wuta a cikin qunci”.
(Waƙar Hana Zalunci, bt. 7)
Idan aka duba ɗango na farkon wannan baiti da aka kawo a
sama, za a ga mawallafin ya ambato ita wannan kalma ta tuwo, Wanda ya ƙara
tabbatar mana da cewa tuwo na ɗaya daga cikin abnicin Hausawa.
Har wa yau, a wata waƙar tasa, Malam Salihu Kwantagora yana cewa:
“Da me shin akan yi fate ne da dambu?
Yara ga wata ‘yar tambaya.
Da gero da dauro akan yi hura,
Sa’annan akan yi kunun tsamiya.
Da me shin akan yi daƙuwa don mu ci?
Da me matanmu suke nakiya?
Da me, a saninku ake alale?
Muke ci, muke lashe baki niya”.
(Waƙar Al’adun Gargajiya, bt.42-45)
Idan aka lura da waɗannan baitoci da aka kawo na sama, a
baiti na farko ɗango na farko za a ga mawallafin ya kawo kalmar fate da ta
dambu. Fate na daga cikin nau’in abinci mai ruwa-ruwa kuma yana cikin rukunin
ajin abinci mai ƙara ruwan jiki. Shi kuwa dambu yana cikin nau’in abinci mai
nauyi kuma yana cikin ajin abinci mai sa ƙarfin jiki/kuzari. A baiti na biyu
kuwa, mawallafin gero da dauro da hura da kunun tsamiya ya ambato. Da gero da
dauro suna daga cikin nau’in abinci da ya danganci tsirai da ‘ya’yan itatuwa,
kana suna ajin abinci mai sa ƙarfin jiki/kuzari. Fura da kunun tsamiya kuma,
suna cikin nau’in abinci mai ruwa-ruwa. Sannan suna ajin abinci mai ƙara ruwan
jiki. A baiti na uku kuma, mawallafin ya ambato daƙuwa da nakiya ne. Dukkansu
suna cikin nau’in abinci da ya danganci maƙulashe/taɓa-ka-lashe. Daƙuwa tana
ajin abinci mai ƙara mai a jiki, yayin da ita kuma nakiya take ajin abinci mai
sa kuzari. Haka kuma, a baiti na huɗu mawallafin alale ya kawo wadda ta danganci
nau’in abinci mai nauyi kuma tana ɗaya daga cikin ajin abinci mai gina jiki.
Malam Hamisu Yadudu Funtuwa, shi ma ba a bar shi a baya ba
wajen kawo ire-iren abincin Hausawa a tasa waqar. Duba wannan baiti da aka kawo
a ƙasa:
“Giya ce abincinta safe da yamma,
Ba ta buƙatar tuwo ko rama,
Wai ita ta riƙa sai alkama,
Sai alkubus wata sa’a da nama,
Ruwan shanta ma sai takan sa zuma”.
(Waƙar Uwar Mugu, bt. 24)
A ƙoƙarinsa na bayyana irin abincin da karuwa take ci da
wanda ba ta ci saboda ƙasaitta, Malam Hamisu a wannan baiti da aka kawo a sama,
ya kawo nau’o’in abinci har guda takwas da suka haɗa da: giya da tuwo da rama
da alkama da alkubus da nama da kuma ruwa da zuma. Ruwa da zuma da giya duk waɗannan
suna daga cikin nau’in abinci mai ruwa-ruwa. Giya ta shafi ajin abinci mai ƙara
ruwan jiki. Yayin da ita kuma zuma ta shafi ajin abinci mai ƙara lafiya. Rama
da alkama kuma, suna cikin nau’in abinci da ya shafi tsirai da ‘ya’yan itatuwa.
Sannan sun danganci ajin abinci mai ƙara lafiyar jiki. Akubus kuwa yana cikin
rukunin abinci mai nauyi kuma yana ɗaya daga cikin rukunin ajin abincin da ke
sa kuzari/ƙarfin jiki. Sai kuma nama, wanda yake cikin nau’in abinci na taɓa-ka-lashe
ko maƙulashe. Sannan yana cikin ajin abinci mai gina jiki.
Muhammad Rabi’u Ibrahim a waƙar da ya yi ta yabon Sheikh
Ngibrima, ya ambaci wasu nau’in abincin Hausawa inda yake cewa:
“Idan an ba su kurɗi na abinci to tsab da su,
Sai su soke su je su
gidan Ngibrima sui nak da su,
Su sha furarsu da nono ga kuma estaran sukari”.
(Waƙar Yabon Sheikh Ngibrima, bt. 33)
A wannan baiti da aka kawo na sama, idan aka duba ɗango na ƙarshe,
za a ga mawallafin ya ambaci fura da nono waɗanda su ma nau’o’i ne na abinci da
Hausawa suke amfani da su a matsayin cimakarsu. Fura da nono a haɗe suna rukunin
abinci mai ruwa-ruwa. Fura ita kaxai tana shafi nau’in abinci mai nauyi. Sannan
tana cikin ruknin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin jiki. Yayin da nono kuma
yake cikin nau’in abinci mai ruwa-ruwa kana yana dangin ajin abinci mai qara
ruwan jiki.
Shi ma Malam Mu’azu Haɗeja a tasa waƙar ta Tutocin Shaihu ya
kawo irin wannan nau’i na abinci. Duba wannan baiti da ke ƙasa:
“Garin da babu zalimu,
Kazaure birnin Adamu,
Uban Gudaji Karimu,
Wurin fura gun damu,
Ba yunwa balle tsiya”.
(Waƙar Tutocin Shaihu da Waninsu, bt. 11)
Idan aka duba ɗango na huɗun wannan baiti da aka kawo a
sama, za a ga mawallafin ya ambato kalmar fura, wadda aka nuna a baya cewa ita
kaɗai ba tare da an dama ta da nono ba, tana ɗaya daga cikin abincin Hausawa da
ya danganci abinci mai nauyi kuma tana rukunin abinci mai sa kuzari/ƙarfin
jiki.
Aƙilu Aliyu, a tasa waƙar da ya rubuta mai suna Al’adun
Gargajiya, ya kawo wasu daga cikin nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya. Duba
waɗannan baitoci da ke ƙasa:
“Ko abinci irin namu,
Babu shi ga waɗansunmu,
Taliyarmu tubaninmu,
Mu muke da dawon damu,
Ban da mu, shin wa adda.
Samɓara, madidinmu,
Mandaƙo, rummacenmu,
Alkubus, ga dambunmu,
Ga fate, ɗanwakenmu,
Gaskami duk mu adda.
Mu muke da gudun-ƙurna,
Shi abincin manya na,
Ga kaɗan nan na zana,
Don saboda mu amfana,
Kyautatar magana shaida”.
(Waƙar Al’adun Gargajiya, bt. 57-58)
Idan aka lura da baitin farko na waɗannan baitoci da aka
kawo a sama, ɗango na uku da na huɗu, za a ga mawallafin ya ambato nau’o’in
abincin Hausawa guda uku da suka haɗa da: taliya da tubani da kuma dawo a ɗango
na huɗu. Dukkansu nau’i ne na abinci mai nauyi kuma suna cikin ajin abinci mai
sa kuzari/ƙarfin jiki. Sannan a baiti na biyu tun daga kan ɗango na farko har
ya zuwa na biyar ba inda mawallafi bai ambaci wani nau’i na abincin Hausawa na
gargajiya ba. A ɗango na farko ya kawo samɓara da madidi. A ɗango na biyu kuma,
ya kawo mandaƙo da rummace. A ɗango na uku da na huɗu kuma ya kawo alkubus da
dambu da fate da ɗanwake. Sannan a ɗango na biyar sai ya kawo gaskami. Su ma waɗannan
nau’o’i ne na abinci mai ne kuma suna cikin rukunin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin
jiki. A baiti na uku ɗango na farko kuma, mawallafi wani nau’in abinci da ake
kira da gudun-ƙurna ya ambato. Shi wannan nau’i na abinci ya shafi abinci ne
mai ruwa-ruwa kana yana cikin ajin abinci mai ƙara ruwan jiki.
Har wa yau, a wata waƙar tasa mai suna Daddaɗan Daɗi Saniya,
ya ƙara kawo mana wasu nau’o’i na abinci da Hausawa suke amfani da su. Duba
wannan misalin da aka kawo a ƙasa:
“Madara, kindirmo daƙashi,
Kangar da cikwi daga saniya”
(Waƙar Daddadan Daɗi Saniya, bt. 19)
A ɗango na farkon wannan baiti da aka kawo, mawallafi ya
kawo mana nau’o’in abinci har guda uku da suka haɗa da: madara da kindirmo da
daƙashi. Madara da kindirmo nau’i ne na abinci mai ruwa-ruwa kuma suna ajin
abinci mai ƙara ruwan jiki. Daƙashi kuwa yana cikin nau’in abinci mai nauyi
kuma yana ɗaya daga cikin ajin abinci mai gina jiki.
Shi ma Muhammad Balarabe Umar a tasa waƙar da ya yi a kan
abincin Hausawa, ya jero sunayen abincin daban-daban. Ga abin da yake cewa:
“Kunu da koko muna da fura,
Da kowannenmu yake ƙauna.
Fate-fate har madidi,
Akwai su dambun Hausawa.
Waina, Ɓula kana ga gauda,
Da alkubus, cincin nawa.
Kana ka sa alkaki, sai,
Su nakiya mai gamsarawa.
Da shasshaka da ƙwaxo, ƙosai,
Akan yi domin saidawa.
Rogo ka sa doya, makani,
Muna da wake mai yalwa.
Gwanda ka sa gwaiba, yalo,
Karas abincin Hausawa.
Da dankali da aya da gyaxa,
Cikin abincin Hauawa.
(Waƙar Abincin Hausawa, 7-14)
A waɗannan baitoci da aka jero, mawallafin ya ambato wasu
nau’o’i na abincin Hausawa da suka dangancin nau’in abinci mai ruwa-ruwa kamar:
kunu da koko da fura da kuma fate-fate. Dukkansu kuma suna ajin abinci mai ƙara
ruwan jiki ne. Haka kuma, mawallafin ya kawo waina da ɓula da gauda da dambu da
alkubus da ƙosai da wake da suka shafi nau’in abinci mai nauyi. Da waina da ɓula
suna ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin jiki. Sannan rogo da doya da makani da
dankali su kuma suna cikin nau’in abinci da ake kira mabunƙusa ƙasa. Sannan
suna rukunin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin jiki. Gauda da ƙosai da wake kuma
suna ajin abinci mai gina jiki. Kwaɗo na asali kuma, yana cikin nau’in abinci
da ya danganci tsirai da ‘ya’yan itatuwa ganin cewa ya shafi ganyayyaki kuma
yana daga cikin ajin abinci mai ƙara lafiyar jiki. Har wa yau mawallafin ya
ambato gwanda da gwaiba da yalo da karas da aya da gyaɗa waxanda suka danganci
nau’in abinci da ya shafi tsirai da ‘ya’yan itatuwa kuma suke cikin rukunin
ajin abinci mai ƙara lafiyar jiki. Sai dai gyaɗa tana ajin abinci mai ba maiqo.
Haka shi ma Isa Mukhtar a tasa waqar ta abinci, ya lissafo
mana wasu nau’o’in abincin da su ma Hausawa sukan yi amfani da su a matsyin
cimakarsu. Duba waɗannan baitoci da ke ƙasa
“In ka huta har kai bacci,
Tumu da ɗata, rogo da muruci.
Kunu da koko, kusku mun ci,
Kun ji abincin masu mutunci.
Zogale, dinkin, ba bambanci,
In na ga sunasir ai sai na ci”.
(Waƙar Abinci, bt. 8-10)
A baiti na farko, ɗango na biyun waɗannan baitoci da aka
kawo na sama, za a ga mawallafin ya ambato tumu da ɗata da rogo da muruci. Tumu
da ɗata suna cikin nau’in abinci da ya danganci tsirai da ‘ya’yan itatuwa. Ta
fuskar ajin abinci kuwa, tumu yana ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin jiki. Data
kuma, tana cikin ajin abinci mai ƙara lafiyar jiki. Rogo da muruci sun danganci
nau’in abinci mabunƙasa ƙasa. Rogo yana rukunin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin
jiki. Muruci kuma yana cikin rukunin ajin abinci mai ƙara lafiyar jiki. A baiti
na biyu ɗango na farko kuma, mawallafin ya kawo mana kunu da koko da kuskus ne.
Kunu da koko nau’in ne na abinci mai ruwa-ruwa kana suna cikin ajin abinci mai ƙara
ruwan jiki. Shi kuma kuskus yana cikin nau’in abinci mai nauyi, sannan yana ɗaya
daga cikin rukunin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin jiki. A baiti na uku ɗango
na farko kuwa, mawallafin ya kawo zogale da dinkin ne da suka danganci nau’in
abincin da ya shafi tsirai da ‘ya’yan itatuwa. Haka kuma suna cikin ajin abinci
mai ƙara lafiyar jiki. A ɗango na biyu kuma, sinasir mawallafin ya kawo wanda ya
shafi nau’in abinci mai nauyi kuma yana cikin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin
jiki.
3.0 Kammalawa
Marubuta waƙoƙin Hausa sai dai a ce musu sam barka. Saboda
irin rawar da suke takawa wajen fito da rayuwar Bahaushe. Domin babu wani ɓangare
na rayuwar Bahaushe da ba su taɓo ba. Kamar yadda aka gani, wannan muƙala ta yi
tsokaci ne a kan yadda ire-iren abincin Hausawa na gargajiya ya yi nason a
cikin rubutattun waƙoƙin Hausa. A waƙoƙin da aka nazarta an gano abincin
Hausawa na gargajiya daban-daban har guda hamsin da tara da suka yi naso cikin
wasu baitocin waƙoƙin Hausa. Wasu daga cikin ire-ien abinci suna rukunin abinci
mai ruwa-ruwa da mai nauyi da taɓa-ka-lashe da mabunƙusa ƙasa. Yayin da wasunsu
kuma suka shafi rukunin abinci da ya danganci tsirai da ‘ya’yan itatuwa. Haka
kuma, an fahimci cewa abincin da marubutan suka kawo a cikin waƙoƙiin nasu sun
shafi azuzuwan abinci daba-daban. Wasu suna rukunin ajin abinci mai sa maiƙo,
wasu mai gina jiki, wasu kuma, suna cikin ajin abinci mai sa kuzari/ƙarfin
jiki. Yayin da wasunsu suke cikin rukunin ajin abinci mai ƙara ruwan jiki. Haka
kuma, akwai waɗanda suka shafi ajin abinci mai ƙara lafiyar jiki. Daɗin daɗawa
an gano wasu nau’o’in abincin da ba na Hausawa ba ne amma a yau Hausawan sun riƙe
su tamfar nasu. Waɗannan kuwa sun haɗa da: alkubus da alkaki da alale da kuskus
da sinasir da sauranasu.
Manazarta
Abdul-Qadeer, M. (2012). “Gudummawar Matasa Goma Wajen Bunƙasa
Rubutattun Waƙoƙin Hausa Jihar Yobe”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Jami’ar
Bayero.
Aliyu, A. (1978). Fasaha Aƙliya Zaria: NNPC.
Funtua, A. I. da Gusau, S. M. ed. (2010) Al’adun da Ɗabi’un
Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printers and Media Concepts.
Wali, M. N. S. (2007). Waƙoƙin Hausa Tsari na Uku. Zaria:
NNPC
Gusau, M. S. (2009) Jirwayen Cimakar Hausawa A Waƙoƙin Baka
na Hausa. Napoli: Universita Degli Di Napoli “L’orientale, Dipartmento Di Studi
Ricerche Su Africa E Paesi Arabi.
Gusau, M. S. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarken Adabin da
Al’adu Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited
Junaidu, I. (1981). Abokin Hira 1 Ciza Ka Busa. Zaria:
Longman Nigeria Limited.
Kwantagora, S. (1979).Yula Waƙoƙin Yara. Ibadan: Oxford
Uveresity Press.
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero, Wallafar
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello
University Press ltd.
Magaji, A. (2009) Hikimomin da Suke Ƙunshe a Yanayin Cin
Abincin Hausawa Napoli: Universita Degli Di Napoli “L’orientale, Dipartmento Di
Studi Ricerche Su Africa E Paesi Arabi.
Haɗeja, M. (1976). Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja. Zaria: NNPC.
Muhammed, A. I. Y. (1982). Waƙoƙin Hikimomi Hausa. Zaria:
NNPC.
Mukhtar, I. (2005). Bayanin Rubutacciyar Waƙar Hausa. Abuja:
Countryside Publishers Limited.
Umar, M. B. (2007). Waƙoƙin Don Yara. Zaria: NNPC.
Rataye
Jerin wasu Sunayen Abincin Hausawa na Gargajiya da Binciken
Gano tare da Bayanansu
Alale: Abinci wanda ake yi da ƙullin wake, ana haɗa ƙullin
da mai a turara cikin leda
Alkaki: Abinci mai zaƙi da ake yi da ɓarjen alkama wanda aka
kwaɓa; ana murza shi a cura kamar tufkar igiya, ƙawanya-ƙawanya sannan a toya
shi cikin ruwan zuma ko dafaffen ruwan sukari.
Alkama: Wani irin tsiro dangin shinkafa, wanda ake shukawa a
fadama ana yi mata bayi, qwayoyinta kusan girmansu ɗaya da na shinkafa sai dai
launinta ƙasa-ƙasa ne; ana abinci iri-iri da ita kamar su alkubus da funkaso da
sauransu; da ita ake yin fulawa.
Alkubus: Wani irin abinci da ake yi da ƙwaɓaɓɓen garin
alkama wanda aka turara sosai ya tashi kamar burodi, ana cin sa da miya,
musamman taushe ko miyar yauƙi.
Aya: Wani irin tsiro mai kamar kajiji; yana da ‘ya’ya masu
zaƙi da garɗi da ake soyawa ko a jiƙa a ci; ana kuma yin daƙuwa da ita .
Ɓula: Wani irin tuwo da ake ajiyewa a ruwa.
Cincin: Wani irin abinci da ake yi da garin fulawa a haɗa da
ƙwai da sukari a soya da mai.
Cukwi: Abin ci busasshe wanda ake yi da madarar raƙumi.
Dambu: Abincin da ake yi ta hanyar turara garin hatsi a haɗa
shi da ganyen rama ko zogale da albasa d.s.
Dankali: Tsiro dangin
mabunƙusa ƙasa mai yaxo da dunƙulallun saiwoyi da ake haƙowa a ci ɗanye ko a
dafa.
Dawo: Curin fura.
Doya: Ɗaya daga cikin
cimaka mabunƙusa ƙasa, wadda ta yi kama da rogo amma ta fi rogo girma.
Dinkin: Sabon tohon
ganyan ɗinya ko na yaɗiya wanda akan dafa don a kwaɗa a ci
Daƙashi: Nonon da yake zuwa da farko bayan haihuwar akuya ko
tinkiya a soya a sa gishiri a ci.
Daƙuwa: Wani abinci
da ake yi da gyaɗa ko aya wani lokaci haɗe da mazarƙwaila ko sikari
Ɗanwake: Abinci wanda
ake yi da garin wake ko na dawa da wake da rogo da aka kwaɓa da garin kuku da
kuma kanwa, sannan a cura dunƙule-dunƙule ana jefawa a ruwan zafi har ya dafu:
akan ci shi da mai da yaji ko da miyar taushe.
Ɗata: Wani kayan
lambu kore mai ɗaci-ɗaci da ya yi kama da yalo, wanda ake ci.
Fate-fate: Wani irin
abinci da ake yin sa ruwa-ruwa wanda ake haɗa shi da tsaki da yakuwa ko da
garafunu ko da albasa ko da wake wani lokaci har da nama.
Fura: Wani abin sha
da akan yi da gero ko shinkafa ko dawa wanda ake damawa da nono.
Gaskami: Wani irin
abinci dunƙulalle da ake yi da garin ɗorawa.
Gauda: Abinci da ake
yi da markaɗaɗɗen wake da ake dafa shi a ɓawon kalgo a ci da miyar taushe.
Gero: Wani irin hatsi
dangin maiwa wanda ake tuwo ko fura ko kunu da shi.
Gudun-ƙurna: Wani
irin ɗanwake da ake yi da alkama.
Gwaiba: Wata irin
itaciya wadda ake cin ‘ya’yanta masu zaƙi.
Gwanda: Wata irin bishiya doguwa mai ganye kamar na zurman,
tana ‘ya’yan da suka yi kusan girman kabewa, masu zaƙi da ake sha.
Gyaɗa: Wani tsiro mai
‘ya’ya a ƙasa, da ke cikin kwanso: ana amfani da ‘ya’yan don yin ƙuli-ƙuli da
man-ruruwa d.s. ‘ya’yan suna da garɗi, musamman idan an soya.
Kangar: Tsimin da ake
yi da saiwoyi tare da fitsarin shanu don sa nono ya yi daɗi.
Karas: Wani tsiro da
ya danganci kayan lambu mai ‘ya’ya dogaye wanda ake a ci ko a yanyanka a kwaɗa
shi tare da ganye musamman salak a ci.
Kindirmo: Daskararren nono da ba a kaɗa ko aka tuaƙ shi ba.
Koko: Abin sha da ake
yi da gasarar gero ko masara ko dawa a dama da ruwan zafi, daidai da kamu.
Kusku: Wani abinci ne
mai kama da burabusko da ake yi da dakakkiyar alkama.
Kunu: Abin sha da aka
yi da dakakken garin gero wanda aka haɗawa da ruwan tsmiya ko kanwa ko ɗorawa
ko gyaɗa, aka dama da tafashasshan ruwa.
Kwaɗo: Haɗa daddawa
ko ƙuliƙuli da gishiri da ɗan ruwa da dafaffen ganye a cakuɗa a ci.
Ƙosai: Abinci wanda
ake yi da markaɗaɗɗen wake a toya da mai.
Madara: Nono sabon
tatsa
Madidi: Wani irin
abinci da ake yi da ƙullin shinkafa ko gero ko dawa d.s. A naɗe shi da ganyen
dawa,
Makani: Wani irin abinci dangin mabunƙusa ƙasa mai kama da
gwaza.
Mandaƙo: Dafaffen
rogo da aka kirɓa haɗe da ƙuliƙuli.
Miya: room-romo da ake kaɗa wa kuka, ko kuɓewa ko karkashi
ko kuma a zuba masa ganye kamar yakuwa ko alayyahu ko lalo a haɗa da tuwo ko
shinkafa a ci.
Muruci: Tsiron saiwar
giginya da ake dafawa a ci.
Nakiya: Garin
shinkafa da ake haɗawa da ruwan zuma ko sukari a kirɓa sannan a cura shi dunƙule-dunƙule;
wani lokaci akan haɗa da kayan yaji.
Nama: Tsoka, watau
curarren abu mai laushi da ya rufe qashi wanda shi kuma fata ta rufe shi, a
jikin dabba ko tsuntsu ko mutum da makamantansu.
Nono: Ruwan da ake samu daga cikin hantsar macen mutum ko
dabba daidai da madara.
Rama: Wani irin tsiro
mai doguwar sanda wanda ake dafa gayensa a yi kwaɗo, kuma ana amfani da ɓawonsa
wajen yin igiya yanta.
Rogo: Wani tsiro
wanda ake cin saiwarsa ɗanya ko dafaffiya; da shi ake yin kwaki.
Rummace: Kwaɗon rama
da garin gero.
Ruwa: Abu garai-garai
maras launi ko ƙanshi, wanda ake sha don kashe ƙishi; kuma ana wanka da wanki
da dafa abinci da wanke-wanke da shi.
Samɓara: ƙatuwar
marmarar tuwo.
Sinasir: Wainar
shinkafa mai faɗi maras kauri da ake ci da miya ko zuma.
Shasshaka: Tuwon
shinkafa da ake curawa a yi masa gurbi a sa mai da yaji a ci.
Taliya: Wani irin
abinci da ake yi da kwaɓaɓɓen garin alkama ko fulawa a mirza shi ya zama siriri
kamar tsinke a busar da shi, wanda idan an dafa shi yake zama kamar tsutsa.
Tubani: Abinci dangin ɗanwake mai tsawo, da aka ƙunsa shi a
cikin ganye ko takarda kafin a dafa.
Tumu: Sabon gero da
aka gasa kafin ya bushe don cin marmari.
Tuwo: Abinci da ake
yi da garin dawa ko gero ko masara ko kuma aka yi da shinkafa aka tuƙa a
tafashasshen ruwa, aka kwashe. Ana ci da miyar kuɓewa ko kuka ko kuma yakuwa.
Waina: Abincin da ake
yi da ƙullin gero ko dawa ko masara ko shinkafa a toya a ci da miya ko sikari.
Wake: Wani tsiro da
yake yaɗo mai ganye kamar na rogo; yana da ‘ya’ya ƙanana cikin kwanso.
Yalo: Gauta maras ɗaci.
Zogale: Wata bishiya
da ake shukawa ko dasawa a gida ko a gona, wadda ake tsigar ganyenta ana dafawa
a kwaɗanta a ci ko a yi dambu ko fate-fate ko ayi miya da shi.
Zuma: Wani ruwa da
ake sha mai zaƙin gaske wanda ake samu daga wani ƙwaro dangin ƙuda, sai dai shi
yana da ƙari wanda yake harbi da shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.