Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Sami Raka'a Ɗaya A Sallah Jam'i Mai Raka'a Huɗu, Ya Zan Ciko Sauran?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, idan ana jam'i sai mutum ya rasa raka'a uku, guda ɗaya kawai ya samu, ka ga kuma ya yi tahiya kafin a sallame tun da sai da suka sallame ne ya tashi ya cika sallah, to malam don Allah yaya ya kamata in yi game da tahiya, tun da na yi a raka'a ta farko ya zan ciko sauran?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, wanda ya sami liman yana raka'a ta qarshe a sallah mai raka'a huɗu, to  kenan zai yi zaman tahiya sau uku a sallar, zaman tahiya na farko ya zama masa tilas ne saboda kasancewar limaminsa yana raka'a ta qarshe ne, shi kuma a lokacin yana raka'arsa ta farko ne. To idan liman ya sallame, sai shi kuma ya miqe ya kawo raka'arsa ta biyu, sai ya zauna ya yi tahiya, bayan ya gama tahiya sai ya miqe ya ciko raka'o'i biyu, sun zama huɗu kenan, sai ya sake zama ya yi tahiya, sannan ya yi sallama.

Idan an lura za a ga ya yi tahiya sau uku kenan, to wannan ba matsala ba ce, kasancewar ya riski liman a raka'a ta qarshe ne ya tilasta masa yin hakan.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments