𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam dan Allah a rabe min, idan
mutun ya samu jam'i raka'a ta uku ko ta karshe yaya zai ciko sauran, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salamu. Dangane da cika sallah ga
masbuqi (wanda bai sami duka raka'o'in sallah tare da liman ba), akwai fuskoki
guda biyu da zai bi don ya ciko raka'o'in da suka kuɓuce masa, wato akwai wajahin QALA'I (ramawa),
da kuma ITMAMI (cikawa).
1. QALA'I (RAMAWA):
Wannan siffa ce ta rama raka'o'in sallah kamar
yadda suka kuɓuce wa
mutum ba tare da canji ba. Misali mutumin da ya riski sallar Isha'i raka'a ta
uku da ta huɗu,
kenan raka'a ta farko da ta biyu sun kuɓuce masa, kuma dama su ana karanta Fatiha da sura
ne a bayyane a cikinsu, to lokacin da liman ya sallame, to idan wannan masbuqin
ya tashi zai rama raka'o'in can biyu na farko da suka kuɓuce masa, zai rama su ne tare da karanta
Fatiha da sura a bayyane kamar yadda suka kuɓuce masa, daga nan sai ya zauna ya yi
tahiya, ya yi sallama, wannan shi ne siffa ta qala'i (ramawa). To yanzu sai mu
je siffa ta itmami.
2. ITMAMI (CIKAWA):
Ita kuma wannan siffa ce ta ciko raka'o'in da suka
kuɓuce wa mutum a sallah ba
kamar yadda suka kuɓuce
masa ba. Harwayau, misali a sallar Isha'i, mutum ne ya riski raka'o'i biyu na
qarshe tare da liman, bayan liman ya sallame, lokacin da ya tashi zai ciko waɗancan raka'o'i biyu, zai ciko raka'o'i
biyun nan ne tare da karanta Fatiha kaɗai ba tare da sura ba a asirce, daga nan sai ya
zauna ya yi tahiya ya yi sallama. Wato zai sanya raka'a ta uku da ya riski
liman yana yi a matsayin raka'a ta farko a wajensa, raka'ar liman ta huɗu a matsayin raka'a ta biyu a wajensa, su
kuma raka'o'i biyun can da ya ciko a matsayin raka'a ta uku da ta huɗu a wajensa.
Wannan ita ce siffar cika sallah ta itmami, kamar
yadda ya tabbata a wajen malaman Fiqhu daga hadisan Annabi ﷺ
Duk da cewa akwai saɓani a tsakanin malaman Fiqhu a kan wanne
ya kamata a yi, to amma duk siffar da mutum ya ɗauka ya cika sallarsa da ita ta yi.
Domin duka nau'o'in hukuncin biyu hadisai sun
tabbatar da su. Bukhari a hadisi mai lamba 636, Muslim kuma a hadisi mai lamba
602.
Kuma duk sauran salloli ma haka hukuncin nasu yake
ga masbuqi (wanda liman ya tsere masa).
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
1 Comments
Shin mutum ne yake da zabin cikawa zai ko rukunin sallah ne zai tabbatar da wane zaai? Wasalam
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.