Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mai Naqudar Da Sallah Ta Kuɓuce Mata Za Ta Rama?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum, Malam tambayata ita ce: haihuwa na yi bayan sallar La'asar, ban yi sallah ba saboda lokacin ina ciwo, amma an tabbatar da haihuwa ce, sai dai ba wata alama, shin ya matsayin sallah ta take zan ramata yanzu ko kuwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, duk macen da sallah ta kuɓuce mata saboda naquda, to hukuncinta ɗayan biyu ne:

1. Idan lokacin da take naqudar, ya haɗa zafin ciwo da kuma jini yana fita, to ba za ta rama sallar da ta kuɓuce mata ba, domin sallar ta faɗi a kanta, saboda wannan jinin za a lissafa shi ne a matsayin jinin haihuwa, wato Nifási.

2. Idan kuma zafin ciwon ne kaɗai ba tare da jini ba, to sallah ba ta faɗi a kanta ba, kuma za ta rama sallar da ta kuɓuce mata bayan jinin nifasi ya yanke mata.

Allah ne mafi sani.

 Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments