Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Yana Chatting Da Tsohuwar Buduwarsa, Bayan Ta Yi Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya taimaki Dr, mijina ne suke chat da wata matar aure, wadda tsohuwar budurwarsa ce a baya sama da shekara 20 da wani abu ta yi aure, suna turawa juna hotuna, shin malam wata shawara da nasiha ya kamata na yi masa? Saboda kubutar da su ga fadawa halaka. Allah ya taimaki mallam ya kara fahimta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, Ki yi masa nasiha da tsoran Allah, sannan kuma ki nuna masa cewa: Inda matarsa ce ba zai so ayi irin wannan mua'malar da ita ba.

Yin chatting irin wannan da matar aure yana iya kaiwa zuwa zina, musamman da alama har yanzu kuna son juna, Allah ya hana duk abin da zai kusantar zuwa Zina a suratul Isra'a'i.

Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai. Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye Shi, wanda ya saɓa masa zai haɗu da Shi a madakata.

Dayanku ba zai yi cikakken imani ba har sai ya sowa ɗan'uwansa abin da yake soma kansa.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu Acikin Wannan Group...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments