𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Ina wuni mallam. ina da wani
saurayi, ina sonshi sosai kuma ina son kasancewa tare da shi, sai dai kuma
hankali na bai kwanta da shi ba ɗari
bisa ɗari,
kuma ina jin tsoro. Please, mai ya kamata in yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu
To Yar'uwa Haƙiƙa Zaɓar Miji Ko Saurayi Ba ƙaramin
Tashin Hankali ne ba Agun Budurwa Musamman Ma Wacce Ta san Abun da Take yi Ta
San Kuma Meye Rayuwar Aure.
Sakamakon abu ne a duhu sai wacce Allah s.w.t yasa
tayi dace tasami nagari. Dan haka yar'uwa sai kin natsu sosai wajen Zaɓar miki ko saurayi ga yadda za ki yi:
Kiyawaita Addu'a Akan Allah Ya baki Miji Nagari
kamar a sujjadah, da sauransu. kizama budurwa tagari akarankanki sai Allah Ya
baki miji nagari don ba yadda za'ayi kisami miji nagari alhalin ke ba tagari ce
ba. Daganan Ki yi Amfani Da Wadannan Shawarwarin;
👉ki zaɓi me
tarbiyya ta addinin musulunci koda bai da tarin ilmin addin sosai.
👉ma'abocin addini wato me aikata ibada bisa koyi da manzon Allah ﷺ daidai gwargwadon iyawarsa.
👉 Me kwazo wajen neman halal ɗinsa
ba malalaci ba dan malalaci bai iya kare mutuncinki addininki, buƙatinki,
inkuwa basu to ba aure ingantacce.
👉kisami me sonki dan Allah, bawai don kina da kyau, ko wani abu ba, don aure
ba son gaskiya zaman gundura ne da wahala.
👉kisami wanda kema kina sonsa sosai don aure ba so ana rasa tausayi da jinƙai.
👉kisami wayayye, wanda ya san mutuncin 'ya mace, ya san rayuwa, yana da
kyakkyawar mu'amala da mutane.
Yar Uwa Dazarar Kin Sami Miji Mai Irin Wannan
Halaye Ke kam Kin yi Dace, Kinsami Aljannar Duniya. Don zai baki kulawa sosai,
za ki sake za ki huta agidansa, sannan wayewarsa zaisa yana barin ki aikata
wasu abubuwa na al'ada, zamani, wayewa matuƙar bai saɓa addini ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.