𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ko ya halatta Mutum ya sayi kayan amfanin
gona ya ajjesu da nufin idan sunyi tsada ya fito dasu ya sayar??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dangane da hukuncin sayen kayan amfanin gona kamar
irin su: Rīɗī,
Gēro, Sha'ir, Dawa, Wake, Gyaɗa,
Gurjiya, Masara, Shinkafa, da dai sauran makamantansu, Mutum ya sayesu ya ajje
da nufin idan sun ƙara kuɗi sai ya fito dasu ya sayar, to wannan dai shine
abinda ake ƙira da suna "Ihtikari" a Larabci idan har ya cika Sharuɗɗan kasancewa hakan, Alal-Hƙiƙa an
samu Saɓanin Malamai
dangane da hukuncin "Ihtikari" zuwaga maganganu kamar guda biyu:
1- Ƙauli na farko shine, mafi yawa daga cikin
Malamai-Fuƙaha'u waɗanda
acikinsu sun haɗa
harda Mazhabin Malikiyya Hanabila Zahiriyya da kuma wani sashe na Mazhabin Shafi'iyya,
duk sun tafi akan cewa "Ihtikari" Haramun ne, daga cikin Dalilansu
sun kafa Hujja da wannan Hadisi na Mαnzon Aʟʟαн( ﷺ ) da yake cewa:
" ﻻ ﻳﺤﺘﻜﺮ ﺇﻻ ﺧﺎﻃﺊ " ( ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ )
MA'ANA:
Babu mai yin Ihtikari sai mai kuskure (Saɓo/Zunubi)
Da wannan Hadisi da kuma wasu makamantansa waɗannan Malamai suka kafa Hujja dasu cewa
haramun ne.
2- Ƙauli na biyu kuma shine, Mazhabin Hanafiyya da
kuma wani sashe na Mazhabin Shafi'iyya sun tafi akan cewa "Ihtikari" Makaruhi ne ba haramun ba,
to Sai dai mafi yawan Malamai sun rinjayar da cewa Haramun ne domin sun ɗauki hanin da Mαnzon Aʟʟαн( ﷺ ) Yayi acikin Hadisan da cewa Hani ne da yake
nuna Haramci.
To amma akwai waɗansu Sharuɗɗa waɗan da dole sai in dasu ne Sannan hukuncin
"Ihtikari" yake iya hawa kan Mutum. ''Misali:''
Sharaɗi ne
ya kasance lokacin da za a sayi wannan kayan ya zama dama lokaci ne da kayan
abinci yayi ƙaranci a gari yana wahala, sai kuma a ka samu wasu Mutane sukaje Kasuwannin
garin suna sayewa suna ɓoyewa
da nufin nan gaba yaƙara wahala ta yadda zai yi tsada sosai daga nan
sai su fito da shi suna sayarwa, ta yadda Mutanen gari zasu ƙara
shiga cikin wani mawuyacin hali da tsanani mai yawa, to gaba ɗaya Malaman Muslunci sunyi Ijma'i akan
cewa wannan Haramun ne Ƙaulan-Wahidan, danhaka ya zama wajibi akan Hukuma
ko wani Shugaba ya tilasta waɗancan
Mutane domin su fito da wannan kaya a sayarwa da talakawa cikin sauƙi.
Amma idan ya kasance ba a lokacin da kayan abinci
yake wahala ba ne yazama akwaishi a wadace kamar Misalin a lokacin "Kaka
ne" Mutum yaje ya sayi amfanin gona ya ɓoye da nufin nan gaba idan ya ƙara kuɗi ya fito da shi ya sayar to wannan kam ba
ya cikin "Ihtikari" saboda Kasuwanci ne danhaka babu laifi ya halatta
ayi, Sannan kuma shi kansa manomi a wannan lokacin babbar buƙatarsa
itace azo asayi wannan kayan abinci da ya noma saboda shima ya samu kuɗaɗen da zai je yayi buƙatunsa dasu,
Hakanan daga Sharuɗɗan "Ihtikari" dole ya kasance
amfanin gonar da aka ɓoye ɗin dama sayensa a kayi da kuɗi da nufin a ɓoye, amma in da kyauta aka bawa Mutum ko
kuma ya samu ta hanyar gado ko ya noma a gonarsa, ko kuma ya saya da nufin ya
ajje amtsayin abincin da zai riƙa ciyar da iyalinsa na tsawon wani lokaci, to duk
wannan ya halatta ayi, danhaka koda Mutum ya ɓoye to ba "Ihtikari" ba ne,
To amma Malamai sunyi Saɓani dangane da cewa Shin Haramcin
"Ihtikari" ya taƙaita ne akan kayan abinci kaɗai ko kuma haramcin zai iya shafar dukkan
wani abu da al'umma zasu iya cutuwa idan aka ɓoye shi?
Mazhabin Shafi'iyya suna ganin cewa haramcin
"Ihtikari" ya taƙaita ne kaɗai akan kayan abinci da kuma tufafi musamman
alokacin sanyi yayinda Mutane suke cikin buƙatarsu, amma Mazhabin
Hanafiyya suna ganin cewa haramcin "Ihtikari" ya taƙaita
ne kaɗai
akan kayan abinci, yayinda su kuma Mazhabin Malikiyya suka tafi akan cewa
haramcin "Ihtikari" yana iya hawa kan dukkan wani abu da ya zama
larurar rayuwa ga al'umma ta yadda in da wannan abin zai yi ƙaranci
to Mutane zasu shiga takura da wahala, Malikiyya sukace abin da ya kamata a
kalla anan shine illar da tasa akayi hanin itace cutuwar da al'umma zasu yi.
Ko Shakka babu cewa maganar da Malikiyya suka tafi
a kanta maganace mai ƙarfin gaske, kuma itace maganar da mafi yawan
Malamai sukafi rinjayar da ita, na cewa "Ihtikari" yana iya shafar
dukkan wani abu da al'umma suke da buƙatuwa zuwa gareshi, danhaka ɓoye wannan abin alokacin da yake wahala da
nufin ya ƙara tsada haramun ne sakamakon cutuwar da mafi yawan al'ummar gari zasuyi,
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.