"Haba Mamman Janar Manaja!
Mamman ƙanen Ubale mai Zango"
– Muhammadu Ganga-Ganga a waƙar Ammani Manajan Neja.
Wannan shi ne Marigayi Alhaji Ammani Inuwa Fagge. Bayan aikin da ya yi na Manajan Niger Club ya yi shuhura a siyasa a Kano. Ya rike muka in shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano a zamanin Jamhuriya ta biyu. Haka nan daga baya ya shugabanci jam'iyyu daban-daban a matakin jiha. Allah ya gafarta wa magabatanmu. Amin.
Daga Zauren:
Makaɗa Da Mawaƙa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.