𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Ina fama da daukewa ni'ima wato
bushewan gaba ko da nasha abinda zai sani ni'ima baya yi sai akace mini sanyi
yana yin haka wato infection Sannan bana jin daɗin saduwa ta aure ko kaɗan shine nakson ataimaka mini da magani
Idan amafarki zaiji ina gamsuwa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Walaikumusalamu warahmatullah.
Gaskiya de yar'uwa a bayaninki dai babu infection a
ciki. Wannan Matsala ce ta mijin dare da kuma daukewar Ni'ima bayan haihuwa.
Amma ga Hanyoyin da zakibi ki samu waraka In shã Allah. Yanda za ki Kori mijin
dare In shã Allahu:
zaki samu:
-man habbatussauda
-Man zaitun
-Man tafarnuwa
-Man hulba
-Kisdil Hindi.
-shazabu.
saiki haɗasu waje guda ki samu Jan miski ki Dora akan wuta
yadan soyu sai ki haɗa da
sauran mayukan ki garwaya sosai ki dinga shafawa musamman inkinzo kwanciya.
ki samu nono sai ki Dora shi a wuta yafatasa sosai
sai ki samu man zaitun Alhawaj ki tofa ayoyin ruƙya a ciki sai ki zuba
cikin nonon kisha.
Ki samu ganyen magarya guda bakwai sai ki dandaƙe su
ki saka akofi sai ki sa ruwa kitofa ayoyin ruƙya a ciki sai ki sha
kuma ki shafa jikinki duka dashi. Ki dinga yi harse kinsamu sauƙi.
Ya kamta ku gane duk wani magani daya shafi jinnu
haƙuri akeyi da kuma juriya haƙuri kan yin maganin da kuma jurewa akan duk wani
Abu da maganin yasa mutum Domin se andaure lokaci ana yi se azo arabu da shi sedai
kuma lokacin da mutum yafara maganin zaiga canji sosai kaman Ciwon jiki ko
gabobi, jiri, amai da sauransu.
Jan hankalin shine duk wani abinda mutum zaiji
daga jikinsa in har zai jure yana amfani da maganin zai dace in Shã Allah bawai
yau in an yi an ji Ciwon jiki sosai se ace ai maganin ma ƙaramin ciwo ya yi se a
dena. Wannan ciwon shine alamun dacen, dan wani har suma da aman Jini yake
yi in har cutar ta yi tsanani a jikinsa kar ki dauka ko Kece ke cutuwa haka suma
aljannu ke ji shiyasa suke wahalar da mutum dan ya tsorata ya dena.
DAWO DA NI'IMA GA MATAR DATA HAIHU
Rashin ni'ima bayan haihuwa kuma ki samu goron
tula kina cinsa kaman guda biyu safe da yamma.
Sannan ki haɗa wannan hadin musamman ce ga macen datayi jego:
Ki samu Zuma, nono, kanunfari da dabino.
Kinemi dabino masu kyau ki gyara ki cire
kwallayenta se ki dauko nono ki zuba dabinon da kanunfari a ciki sai ki barsu
su jiƙa a ciki na dan wasu mintuna sai ki markadasu a blender sai ki sa Zuma a
ciki kisha akalla cikin ƙaramin Kofi safe da yamma. Kina haka in son samune
har 6 weeks.
Sannan ki samu zogale danye ki markada a blender
ki matse ruwan saiki sa Zuma mazarkwaila da madaran shanu ko peak sai ki daka
kanunfari ki zuba a ciki kisha.
Sannan ki samu yayan bagaruwa da ganyenta da kuma
ganyen magarya da kanunfari ki haɗa ki
tafasa su inya dan huce sai ki shiga ciki ki zauna kaman minti 15 sai ki fita
kullum kina haka sau ɗaya.
Wayannan sune yakamata macen data haihu ta yi dan
dawo da ni'imarta.
Allah ta'ala yasa mudace
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
1 Comments
Malam assalamu alaikum,Malam kayi magana akan maganin bushewa da namijin dare to ni bansan ayayoyin rukyarba Malam afuwan wlh inada karancin ilmi nagode
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.