Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Bushewar Ni'ima Da Mijin Dare

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Ina fama da daukewa ni'ima wato bushewan gaba ko da nasha abinda zai sani ni'ima baya yi sai akace mini sanyi yana yin haka wato infection Sannan bana jin daɗin saduwa ta aure ko kaɗan shine nakson ataimaka mini da magani Idan amafarki zaiji ina gamsuwa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumusalamu warahmatullah.

Gaskiya de yar'uwa a bayaninki dai babu infection a ciki. Wannan Matsala ce ta mijin dare da kuma daukewar Ni'ima bayan haihuwa. Amma ga Hanyoyin da zakibi ki samu waraka In shã Allah. Yanda za ki Kori mijin dare In shã Allahu:

zaki samu:

-man habbatussauda

-Man zaitun

-Man tafarnuwa

-Man hulba

-Kisdil Hindi.

-shazabu.

saiki haɗasu waje guda ki samu Jan miski ki Dora akan wuta yadan soyu sai ki haɗa da sauran mayukan ki garwaya sosai ki dinga shafawa musamman inkinzo kwanciya.

ki samu nono sai ki Dora shi a wuta yafatasa sosai sai ki samu man zaitun Alhawaj ki tofa ayoyin ruƙya a ciki sai ki zuba cikin nonon kisha.

Ki samu ganyen magarya guda bakwai sai ki dandaƙe su ki saka akofi sai ki sa ruwa kitofa ayoyin ruƙya a ciki sai ki sha kuma ki shafa jikinki duka dashi. Ki dinga yi harse kinsamu sauƙi.

Ya kamta ku gane duk wani magani daya shafi jinnu haƙuri akeyi da kuma juriya haƙuri kan yin maganin da kuma jurewa akan duk wani Abu da maganin yasa mutum Domin se andaure lokaci ana yi se azo arabu da shi sedai kuma lokacin da mutum yafara maganin zaiga canji sosai kaman Ciwon jiki ko gabobi, jiri, amai da sauransu.

Jan hankalin shine duk wani abinda mutum zaiji daga jikinsa in har zai jure yana amfani da maganin zai dace in Shã Allah bawai yau in an yi an ji Ciwon jiki sosai se ace ai maganin ma ƙaramin ciwo ya yi se a dena. Wannan ciwon shine alamun  dacen, dan wani har suma da aman Jini yake yi in har cutar ta yi tsanani a jikinsa kar ki dauka ko Kece ke cutuwa haka suma aljannu ke ji  shiyasa suke wahalar da mutum dan ya tsorata ya dena.

DAWO DA NI'IMA GA MATAR DATA HAIHU

Rashin ni'ima bayan haihuwa kuma ki samu goron tula kina cinsa kaman guda biyu safe da yamma.

Sannan ki haɗa wannan hadin musamman ce ga macen datayi jego:

Ki samu Zuma, nono, kanunfari da  dabino.

Kinemi dabino masu kyau ki gyara ki cire kwallayenta se ki dauko nono ki zuba dabinon  da kanunfari a ciki sai ki barsu su jiƙa a ciki na dan wasu mintuna sai ki markadasu a blender sai ki sa Zuma a ciki kisha akalla cikin ƙaramin Kofi safe da yamma. Kina haka in son samune har 6 weeks.

Sannan ki samu zogale danye ki markada a blender ki matse ruwan saiki sa Zuma mazarkwaila da madaran shanu ko peak sai ki daka kanunfari ki zuba a ciki kisha.

Sannan ki samu yayan bagaruwa da ganyenta da kuma ganyen magarya da kanunfari ki haɗa ki tafasa su inya dan huce sai ki shiga ciki ki zauna kaman minti 15 sai ki fita kullum kina haka sau ɗaya.

Wayannan sune yakamata macen data haihu ta yi dan dawo da ni'imarta.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

1 Comments

  1. Malam assalamu alaikum,Malam kayi magana akan maganin bushewa da namijin dare to ni bansan ayayoyin rukyarba Malam afuwan wlh inada karancin ilmi nagode

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.