Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Bushewar Ni'ima

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu... Malam Don Allah mene maganin bushewar ni'ima ga mace kuma mai yake kawo wannan matsalar ga mata. an ce wasu matan jifa ne ko girma. Da gaske ne? Allah ya karo ilimi da hakuri da dalibai ya kuma bamu lada. Amin

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Malamai masanan kiwon lafiyar jikin Ɗan Adam sun ce dalilan dake kawo bushewar ni'ima a jikin Mace suna da yawa. Amma daga cikinsu akwai:

1. Dalilin wani infection (kwayoyin chuta) acikin al'aurarta.

2. Rashin lafiya mai tsanani ko zazzaɓi mai zafi idan ba'a maganceshi da wuri ba.

3. Shan Miyagun kwayoyi.

4. Amfani da wasu allurai ko Magunguna masu Ƙarfi (Don tsai da haihuwa, ko magance Hawan jini, Diabates, etc).

5. Rashin samun isashen abinci mai gina jiki.

6. Rashin kwanciyar hankali.

7. Sihiri ko Shafar Aljanu (Musamman Jinnul Ashiƙ).

Idan ya zamanto ta dalilin rashin samun isassun kayan abinci ne (Musamman kayan Marmari da 'Ya'yan itatuwa) to da zarar an samesu an sarrafasu ana sha, za a samu chanji sosai.

Idan kuma ta dalilin shan wasu Kwayoyin magani ne ko allurai masu Ƙarfi, to da zarar anyi ma likita magana zai iya chanza yana yin magungunan kuma za a samu saukin matsalar.

Idan kuma ta dalilin rashin lafiya ne ko rashin kwanciyar hankali, to da zarar an samu chanji, lafiya za ta samu.

Amma abinda yafi janyo matsalar bushewar ni'ima ga mata (at least 80%) zaka tarar cewa JINNUL ASHIƘ ne. Shi wani irin Shaiɗani ne wanda idan ya shiga jikin Mace zai rika zuwa yana saduwa da ita afili ko amafarki, da siffar Mijinta ko saurayinta ko wani ɗan'uwanta.

To saboda zafin kishinsa akan wacce yake jikinta, shi yasa yake ɗauke mata ni'ima, ya sanya mata jin zafi, Ƙaikayin gaba, etc. Amma idan shine yazo mata amafarki za ta ji tana samun gamsuwa sosai fiye da yadda take samu da Mijinta.

Ba'a fita sosai daga matsalar har sai an maganceshi ya bar jikinta. Amma in ba haka ba, duk maganin Ƙarin ni'imar da za ta sha ba zai yi mata aiki ba.

Da fatan Allah yasa mu dace, Allah yasa haka ameen.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments