1) Kwaikwayo da ƙinsa: Yadda dawwamammen kwaikwayo yake alama na kishi haka guje masa gaba daya kan zama wata alamar dake nuna kishin, wato yadda mace za ta kishiyarta na yin wani abu sai ta fara kwaikwayonta koda ba za ta amfana da abin da take kwaikwayo ba, wasu matan ƙiri-ƙiri suke yi, misali in da wata za ta ga kishiyarta na sayar da gyada sai ta fara sayarwa ita ma, ba kasuwancin ne a gabanta ba ginshiƙi ne na kishi, yadda ake gane hakan kuwa sanya gasa a ciki wajen fuskantar masu sayan kayan, domin ba za ta iya boye abin da yake cikinta ba zai fito ta lafuzzanta yadda za ta riƙa gaya wa musu ita ga yadda take sana'arta a zo wurinta.
Ko ba haka ba ma za ta iya fitowa ta tsaya inda za
ta fara ganin masu sayen kayan kafin su ƙarasa wurin kishiyar ta karbe, wani sa'in
ta jefa wasu 'yan maganganu kafin ta wuce kishiyar, duk abin da za ta yi ƙoƙarinta
kawai wancan ta tanka. Hakan ba zai ishe ta ba sai ta ƙara da gaya wa maƙwabta
cewa kishiyar tata na baƙin cikin ta fara irin sana'ar ne kuma an fi son a
zo wajenta, bayan ba wani abu da yake gaskiya a ciki. Buƙatarta ta dena wannan
sana'ar ya zama ita kadai take yi. In ma kishiyar ta saduda ta bar mata sana'ar
ta yi tunanin wata ta dauko don dai a zauna lafiya, yadda kowa da sana'arta
daban, ba yuwuwa zai yi ba.
Matuƙar dai za ta ƙyalla ido ta ga kamar an
fara gane ta kuma ana zuwa a saya, tsab ita ma za ta fara kawo wannan kayan,
don burinta ba zai cika ba sai ta ga ta rufe kishiyar gaba daya ba wace ake
maganarta sai ita, fatarta ta karbe komai kishiyar ta dawo ƙasanta,
sabanin yadda masu sana'a iri daya kan yi in sun zauna a wuri guda, kowa kasuwa
kawai yake nema ba ruwansa da wani. Ko a wannan ma mu maza muna da rauni babba
ba ma iya yin abin da ya dace, da a ce za a sami tsayayyen namiji dake kallon abin
da yake faruwa a gidansa kuma ya tsaya tsayin daka kan cewa kowa ta sana'arta
ba ruwanta da abin da dayar take sayarwa tsab zai magance matsalar, amma da
wahala mu iya yin hakan.
Sai dai mu zuba musu ido ko mu yi ta yadawa wance
ce da laifi wance ta cika ƙorafi. Akwai abin da ake fadakarwa ne wanda ya
kamata maza su fahimta, in aka dubi kasuwa za a ga cewa galibin masu sana'a iri
daya a wuri guda suke zama, wani lokaci ma sukan yi kasuwarsu daban, kowa ke buƙatar
nau'in wannan kayan can zai tafi, kuma kowa a cikinsu yana samun arziƙinsa
ba tare da tsangwama ba, koda yake Allah SW kan fifita wani a kan wani amma za
ka taras babu irin wannan kishin, koda kuwa mata ne ke kasuwancin ba maza ba.
Dalilin haka kuwa don sana'ar an gina ta ne tun asali a kan kasuwanci ba a kan
kishi ba, shi ya sa ba su nufin junansu da wani mummunan abu.
Zan ba da misali: Jiya na ga wani abin mamaki a
wurin wasu 'yan mata 'yan shekara 13-14, suna sayar da mangwaro, na kira daya daga
cikinsu sai na ga sauran biyun sun taso gaba daya, na ce "A'a ga wace na
kira" da kanta ta ce ai haka muke yi malam ba komai duk wanda ya yi maka
ka saya. Duk da haka nata kawai na duba na ba ta kudin, sai ta ce a raba za ta
ba da na kaza wata dake kusa da ita ita ma ta ba da na kaza, ta gefen kuma in
sun sake samun wani sai ta bayar. Tsakani da Allah ban yi niyyar saya da yawa
ba, amma da abin ya ba ni sha'a na saya, ban kai gida ba na yi kyauta da wasu.
Wannan nau'i na kwaikwayo ba a kasuwanci kawai ya
tsaya ba, harda kwalliya, misali yadda wancan take daurin kallabinta, ko saka
jan-baki ko gazal, da ma irin ƙyallen da take sanyawa, ko irin dinkin da ake yi
mata da sauransu. Za ka taras wata hatta turaren da ta ji kishiyarta na sakawa
sai ta sayo shi ta saka. Maganar gaskiya yin hakan sam ba kuskure ba ne in ya
kasance irin wanda mijin yake so kenan, wannan wani fage ne da kowa za ta zu
ashutarta don kamo zuciyarsa da kula da ita, akwai lada akwai la'ada a yin
hakan tunda manufar kyautata wa maigida ce.
Amma kash! Ba haka abin yake ba, gasa ce
tsagwaronta, tunda wance ta sanya kaza ni mai zai hana ni saka irinsa? Irin
wannan kishi na kwaikwayo daban, akwai wani nau'in kuma wanda kishiya ba za ta
taba yarda su yi abu iri guda abikiyar zamanta ba, in wannan ta yi abu kaza ko
wancan wani abin za ta yi daban, kamar dai maganar zama wuri guda, yadda wata
ba ta ƙaunar a hada su, wata kuma ta ce ba ta yarda ba sai dai a hada su, kowa da
fuskar da take fitowa da ita wurin aiwatar da kishinta.
Misalin wannan in mace ta yi niyyar yin tuwo miyar
kuka, sai ta ji an ce kishiyarta ma abin da za ta yi kenan, in sha Allahu ba za
a ci tuwonnan ba. Wata ko makaranta maigidan ya saka su ba za ta tafi ba, gwara
ta mutu a jahila da dai su hadu a makaranta guda tare da kishiyarta. Sai nake
ganin da ma a saye da sayarwa suka yi hakan kowa ta kama gabanta ta riƙe da ƙarfi
Allah ya ba da sa'a, in da kishiyar za ta ce za ta sayar da kaza ita sai ta
kama wani abin daban, to amma da yake kishin sabanin abin da ake buƙata ne
ko tana saba mata a komai ba za ta saba mata a wurin kayan sayarwa ba. Shi
kishi kamar yaƙi ne, kullum mutum na kallon gazawar wanda yake
kishin da shi ne.
Akwai wace take ƙoƙari ganin yadda za ta baƙanta
wa abokiyar zamanta in mijin ya kawo abu sai ta ce ai ya kawo da yawa bayan
dayar na cewa ba ya isa, misali in dayar na amfani da manja kwalba daya a kwana
hudu, sai ta ce ita sati biyu za ta yi tana aiki da shi, don dai kawai maigidan
ya fahimci wancan zaluntarsa take yi. Shi ya sa Shari'a ta yi maza ta hana don kar
a riƙa zaluntar wata. Wannan duka ba kwaikwayo ba ne saba wa abokiyar zama ne
don a jefa ta rigima da maigidanta.
Har da haka akwai wace za ta riƙa
kallon abokiyar zamanta tana ganin yadda take ma'amalla da mutane, in ta ga
tana kyautata musu suna son ta sosai sai ita ma ta fara kyautata don samun
wannan soyayyar, yin hakan ba aibu ba ne, don ba abin da yake da kama da cutar
da wani a ciki. In dai gasa ta shi ciki ne, ya zama wata na yi don kare dayar
yadda ba za a ga haskenta ba gaba daya shi ne abin ƙi. Wata rana ogana a
wurin aiki ya so sayen fili zai yi makaranta, aka sama masa wani wuri mai kyau,
sai dai ya yi kusa da wata makaranta mai dalibai irin namu, sai ya ce "Ba
na shakkar za mu ƙwace masa dalibai. Ya yi shekaru da dama anan shi
aka sani, bai dace ba mu zo baƙi mu raba dalibansa mu kwashi wasu" shi kenan
kuma aka fasa sayen wurin.
A Nan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.