8} Mace da kanta kan san tana da baƙin kishi, don na sha jinsu suna fadi da bakunansu cewa azababben kishi ne da su, wata in ka je nemanta za ta gaya maka ita fa ga yadda take, tarihi ya dauko mana cewa Ummu-Salama ta ambata wa Annabi SAW haka a lokacin da ya je nemanta, sai ya ce zai yi mata addu'a, kenan tun wannan lokacin an san mata kan fahimci yadda suke, kuma a wannan hadisin an gano cewa addu'a kan magance masifaffen kishi. Tarihi ya nuna mana matsayin da Annabi SAW ya ajiye Ummu-Salama, wanda hakan ya taimaka wurin shawo kan halin da take ciki.
Tunda mace takan iya gano kanta, to ya zama dole
ta lalubo hanyoyin da za ta ƙarfafa alaƙarta da wasu, masamman maigidanta, ta nemi
yin sulhu da shi ta wurin kauda kai daga dukkan sha'anoninsa, tare da
sadaukarwa cewa namiji nada damar yin aure a duk lokacin da ya ga dama, kuma
jin dadinta da kwanciyar hankalinta na bayan amincewa ne da abin da yake so. Ya
kamata ta gano cewa in kwanciyar hankalin da natsuwarta ba su ba ta abin da
take buƙata ba, tashin hankali ba zai taba ba ta ba.
Daganan sai ta yi damarar fuskantar duk
matsalolinta nanan gaba masu alaƙa da maigidanta ko abokiyar zamanta masamman kan
al'amuran da suka shafi kishi, mu fahimci cewa kishinnan ba halittace ga mace
ba, galibi al'ada ce a kan gaba wurin ingiza mace ta aikata abin da za ta zo
daga baya tana da-na-sani. In ba haka ba mu dubi rayuwar turawa yadda mace ko
tana da aure za ta iya saduwa da wani ta kuma iya gaya wa maigidanta a matsayin
mai gaskiya, sai dai ya bata rai ko ya nuna rashin jin dadinsa, amma in ta kama
shi da wata, ya zama cin amana na ƙarshe wanda in ba a yi sa'a ba yana iya balgace
auren gaba daya, Turawa kenan.
A ƙasashenmu kuwa ko mace ta kama namiji da wata sai
dai su yi rigimarsu amma ba abin da zai sami auren, sabanin a ce shi ne ya kama
ta da wani. Ba wannan ne kadai ba, mace a duk inda take halitta daya ce,
fahimtarmu anan kishin mata na bayan al'ada ne ba halitta ba, don kuwa wata za
ta iya kashe kishiyarta a ƙasashen goshin Afurka, wato Somalia, Eritrea,
Jibouti zuwa Ethiopia matuƙar za su zauna a garuruwa kusa da juna. Mu kuwa
anan Nigeria sai mu hada su gida guda, ƙila su hadu a falo, kuma ba abin da zai
faru sai wanda ba za a rasa ba, al'adar ce ta sha bamban, amma halitta daya ce.
A kan wannan, in dai a matattararmu mun sani mace
ba ta iya hana mijinta ƙara aure to abu mafi inganci shi ne ta samo
hanyoyin da za ta zauna lafiya da amaryarta, na farko dai ta huta da tashin
hankali tsakaninsu, kuma ba ta da wata ƙullalliya ita da maigidanta. Abin da ya
kamata ta gane duk lokacin da mace za ta yi fada da amarya to kai tsaye da
wanda ya kawo ta take yi, na sha ganin matan da suka ta da hankulansu sosai a ƙarshe
sun bar wa amaren gidan. Duk dadewar da mace za ta yi a gidan miji matuƙar za
ta yaƙi da abin da yake so to da shi take yi, wannan fadar kuwa koda shi kadai ne
ya fi ƙarfinta bare kuma su yi mata taron dangi.
Ba yadda mace za ta sami zama lafiya da kishiyarta
sai ta saukar da kanta ƙasa, ta nuna mata yarda har a ma'amallarta da ita,
kwanaki na ga wata mata a asibiti tana zaune da kishiyarta, ita ke yi mata
komai, kishiyar za ta haihu ne, wata matar ba za ta taba bari kishiyar ma ta
san za ta haihu ba, sai dai ta ji labari daga baya in ta haihu, akwai wani gida
da na ga matan sun fi yarda da junansu sama da bare, suna ganin asirinsu anan a
rufe yake, dukansu suna sana'a, kuma kowa a cikinsu tana sayar wa kishiyarta da
kaya in ba ta a gida, kayan da wannan ke sayarwa da ma wancan ba ta da shi,
wannan nau'i ne na fahimtar juna.
Matsalolin farko gaskiya maza ke jawowa, yadda
suke maida abu mai mahimmanci a matsayin ƙaramin abu, in mace ta yi sai a ce kishi
ne kawai, a maimakon a tsaya a duba shi a nemo masa hanyoyi kala daban-daban da
za a yi maganinsa, da farko dai kai namiji kar ka taba yarda da wani abu
sunansa kishi, kar ka ba da damar da za a maida maka da gida fagen fama, duk
macen da za ta yi wani abin da zai nuna kishi komai gaskiyarta ka taka mata
burki. Wace za ta yi rigima da abokiyar zamanta ka dauki mataki a kansu duka,
kamar dai yadda muka karanta a baya, hanyoyin da uwayemmu suka bi kenan wajen
shawo kan gidajensu.
Duk in ka ga abin da ba ka gamsu da shi ba ka zuba
ido to ka tabbatar ka saka dan ba kenan da za a ci gaba, sai kuma yadda hali ya
yi, kishi ya wargaza gidaje da dama, ba inda aka sami baƙin kishi gidan ya zauna
lafiya. Babban kuskuren da namiji zai yi shi ne ya riƙa daukar maganar wannan
yana kai wa wancan, wato munafukin mata, irin wadannan mutanen da ya kamata su
tsare gidajensu su suke wargaza shi da hannunsu. Zancen gaskiya duk namijin da
ya san abin da yake yi zai fahimci cewa rabuwan kan mata ba alkhairi ba ne ga
tarbiyyar yara, koda maigida yana jin dadin abin da yake faruwa na gasa a
tsakaninsu ya tabbatar akwai wani tasiri maras dadi da zai koma wa tarbiyyar
yaransa anan gaba.
A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.