Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi Rahama Ne Ko Azaba // 47

2) Riya da dora wa kai aiki: Abin da ya fi fitowa sarari kenan a duk lokacin da mace ta so yin kishi, a zahiri ba don Allah take yin wasu abubuwan ba, tana yi ne tare da boye kishi a zuciyarta, ƙoƙarinta a ga baƙin kishiyarta, in ma ta rasa abin da za ta jingina wa kishiyar sai ta ƙirƙiro wani abin ta kambama shi don ta isa ga abin da take so, bari na kawo abin da ya faru a gabana ba labari aka ba ni ba a wata jaha can mai nisa: Uwargida ta kawo wa baƙin mijinta abinci ta ajiye musu, tana dan jan su da labari tana ƙoƙarin su ci. Bayan ta fita don ta kawo musu wasu abubuwan da za su ƙara, saboda a tunaninta abin da ta kawo musu bai ishe su ba.

Nan take amaryar ta zo da zafinta tana fada tana cewa "Jahilci bai yi ba wallahi, ta ya za ka yi baƙi ka wulaƙanta su? Wadannan fa baƙin mijinka ne, ka kawo musu abinci amma ka saka musu cokalin ƙarfe? Ni wallahi ba yadda zan ba wa baƙon da nake girmamawa abinci da cokalin ƙarfe, ko na rasa na roba zan nemo a maƙwabta" ban san ya aka ƙare ba amma na san a garuruwansu ba sa ma'amalla da cokalin roba ko kadan, hasali ma rashin girmamawan ne a ba su cokalin roba su ba yara ba, amaryar dai ta jefar da cokalin ƙarfen ta saka musu na roba.

Mace mai baƙin kishi kan yi haba-haba da mutane kamar daga cikin zuciyarta suke, bayan ba ta ma ƙaunar ganinsu, abin da take so kawai su yabe ta su ce ita mutuniyar kirki ce abokiyar zaman tata ce mutuniyar banza. a kan sami wace za a kintsa magana da ita kan 'yan uwan miji sai kishiyar ta saki jiki ta zartar da abin da aka shirya ita sai ta ƙi aiwatarwa ta dawo tana zagin wancan tana gaya musu gaskiya da ƙarya don ta bata ta a idonsu ta ce musu ai mutuniyar banza ce bayan tare aka shirya. In ta ga kishiyar ba ta da kudi sai ta yi maza ta yi wa uwarmiji farfesun kaza, ko ta sayo mata kayan dadi, ta yi ta haba-haba da ita yadda za ta ce ita ce diyar albarka tana kula da ita sosai, bare ma a ce tana da wasu 'yan abubuwa da ta gaza a kansu tsab za ta kwaso ta gaya wa uwar-mijin, buƙatarta rigima ta shiga tsakaninsu.

Akan yi hakan ne don wani lokaci in ya zo da kuskure uwar-mijin na iya kiran danta ta kwashe ƙarya da gaskiya na abin da aka fada mata ta gaya masa, sai a fara samun sabani tsakaninsa da matar. Koda yake uwarsa ta fada masa amma kintsa mata aka yi, da yawa in ka ga mata masu mugun kishi suna haba-haba da mutane sama da yadda aka saba gani ba don Allah suke yi ba, dora wa kai ne don kaiwa ga wani buri dake zuciyarsu na son a saki abokiyar zamansu, ko saka ta a halin ni-'ya-su. In aka lura ba sa yin hidimar baki rufe sai sun fado ƙoƙarinsu a fili gami da sukar kishiyar.

Ƙiri-ƙiri za ka ji wata na ce wa 'yan uwan miji "Wai kuwa wance ta ba ku kazar da ta soya jiya? Kun dai san wallahi da ni ce na yi aikin dole sai kun ci kazannan don dalilin dan uwanku muka samu" idan da za ka yi bincike mai zurfi za ka tarar tare suka ƙulla cewa a hana su, amma da suka zo gabansu sai ta tsame kanta ta tura wa abokiyar zamanta. A hali irin wannnan dole ta kiyaye, ta fahimci wace take zaune da ita, ta karanci hanyoyin da take bi don ta baƙanta ta a gaban maigidansu ko 'yan uwan mijinsu, a ƙarshe ta fara bin hanyoyin da suka kamata don ƙwatar kanta daidai gwargwado.

Ita dai kar ta shiga gasar da ta fi ƙarfinta, kar ta yi niyyar rama mummunan aiki da mummuna, a maimakon haka ta riƙe gaskiya kuma ta dena bin wancan sau da ƙafa don kar ta kare mata rami sai ta zo dab da shi ta yi tsalle ta tsallake ita kuma ta fada ciki, ta riƙa binta a hankali kuma nesa da nesa yadda za ta riƙa ganin duk wani abin da zai iya cutar da ita. Matar da take jefa abokiyar zamanta a irin wadannan ramukan ba ƙaramin kishi ba ne da ita ba, buƙatarta ta ƙarshe ita ce ta kore ta a gidan.

Su ma 'yan uwan mijin zai yi kyau su sa ido sosai don za su iya gano kyautar da aka yi ta a kan kishi da wace aka yi don Allah, galibin kyautar kishi ba mai ci-gaba ba ce, mai yi na samun abin da take so za ta juya musu baya, kamar kyautar 'yan siyasa ce da suke yi don azabe su, sun ci ko ba su ci ba zaben na wucewa shikenan, haka mai kyauta don kishi, tana samu ta kori wancan komai ya dawo hannunta za ta fara tunanin yadda za ta ba wa kanta kariya ta tabbatar da abinnan ya ci-gaba da zama a ƙarƙashinta. Da wahala mace ta mallake miji ka ga tana shiri da 'yan uwansa.

Ta zare zaren kenan, wata da sassafe za ta kama hanyar dakin uwar mijin ta share mata daki, ta wanke mata kaya, ta dafo mata abinci ko ba ita ce da girki ba, ƙoƙarinta kawai a ce ita ce ta ƙwarai a ba ta kula ta masamman. To wannan dan ƙaramin bom ne aka dasa, domin idan uwar ta fara gaya wa danta irin kyautatawar da take mata, da kuma nuna rashin kular da dayar ke yi zai so mai son uwarsa, dayar kuma in ba a bi a hankali ba tabbas za ta bar gidan ba tare da ta shirya ba. Don maigidan na fara ganin baƙin iyalinsa magana ta lalace kenan.

A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments