Ticker

6/recent/ticker-posts

Kabushi/Kabewa

Kabushi/Kabewa ke nan ɗaya daga cikin cimakar Hausawa domin ana dafa shi a haɗa da ƙuli-ƙuli da kayan yaji da magi da gishiri ya ɗan yi ruwa-ruwa a sha /a ci, ko a yanka shi a saka cikin miya domin ya ɗaure ta ya kuma ƙara mata zaƙi. Ko akwai wani /wasu daga cikin Masartan Baka na Hausa da suka waƙe /ko ambace shi a cikin Waƙoƙin su kuwa? Allah ya dawo muna da dawamammen zaman lafiya a Ƙasarmu, ya bamu lafiya da abun da lafiyar zata ci, ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Ɗan Anache ya ce:
Gwamma da kat taho,
Wane ɗan garkin banawa,
Baban wane ya sha kabewa ya yi nauyi,
Ko tahiya ya kai sai shi daddahe tsara tai"....

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments