𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Allah gafarta menene hukuncin
Wanda sha'awa tama yawa kuma bayason kallon batsa amma zuciyarsa ta kasa masa
sai da ya kalla yake samun sukuni bayan kuma daga baya yazo yai nadama. Sannan
wace addu'a yakama ta ya ringa karantawa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Na farko dai wannan alama ce dake nuna Ƙarancin
tsoron Allah azuciyar masu yin haka. Sannan kuma da alamar cewa Zuciyarta tafi Ƙarfinta.
Allah Maɗaukakin Sarki ya gaya ma Annabinsa Dawud (alaihis
salam) cewa : "... Kuma kada kabi son zuciya balle ta ɓatar dakai kan hanyar ALLAH.
Hakika waɗannan da suke ɓatarwa daga kan hanyar ALLAH, garesu akwai
azaba mai tsanani saboda abin da suka manta na ranar hisabi".
Kuma acikin suratu Yusuf (alaihis salam) Allah ya
ce "hakika ita zuciya lallai mai yin umurni ce ga mummunan abu".
Allah shi ne ya halicci Ɗan Adam kuma ya sanya
sha'awa ajikinmu domin ya jarrabemu ya bayyanar da bayinsa masu tsoronsa da
kuma waɗanda suka
karkace daga kan hanyarsa._
Kuma ya kafa mana dokokin da zamu bi domin mu
rabauta anan duniya da kuma ranar Ƙiyamah. Don haka Allah yace ma Annabinsa (sallal
Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) :
وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ ...
"ka gaya ma muminai mata su runtse DAGA
idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu".
Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga Matayen
Muminai, bayan kuma ya gargadi Mazaje Muminai.
Kuma Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (rta) Yace
Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :
"HAKIKA SHI KALLO, WANI KIBIYA NE MAI DAFI
DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS. DUK WANDA YA BARI DON TSORONA, ZAN CHANZA MASA DA
WANI HASKE (WATO HASKEN IMANI) WANDA ZAI JI DANDANONSA ACIKIN ZUCIYARSA".
(Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy juzu'i na 10 hadisi
na 10,362).
Kallon batsa bai halatta ba. Kuma cewa wai sha'awa
ce tayi miki yawa ba zai zama uzuri karɓaɓɓe
agun Allah ba. Don haka kiji tsoron Allah ki rika tuna ranar gamuwarki dashi.
Ki kiyaye dukkan gabobin jikinki daga saɓa masa.
Allah Maɗaukakin Sarki yana bada labarin ranar Alkiyamah.
Yace :
"AWANNAN RANAR DA ZAMU YUMƘE
(SANYA RUFI) BISA BAKUNANSU, KUMA HANNAYENSU NE ZASU ZANYAR DAMU, KUMA ƘAFAFUWANSU
SUNA SHAIDARWA BISA ABIN DA SUKA KASANCE SUNA TATTATAWA (NA LAIFUKA)".
Kiji tsoron ranar tonon asirai, ranar da Allah zai
nunoki (kamar a vedio) gaki nan sanda kike aikata ayyukan sharrin da kika
aikata.
Idan zaki tuba kiyi cikakkiyar tuba irin wacce
Allah yake so. Ba wai tubar Mayaudara ba.
Addu'ar neman shiriya kuwa babu kamar fatiha. Ki
rika karantawa tare da halarto girman Ubangiji. Allah mai gafara ne mai rahama.
Shi keda ikon shiriya da kuma yin gafara ga bayinsa.
Allah ya gafarta mana baki ɗaya, Aameen.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.