Ticker

6/recent/ticker-posts

Azumi Nawa Ake Yi A Watan Muharram?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam Don Allah malam azumi nawa akeyi a wannan watan na Muharram?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikum Assalam To 'yar'uwa ana so mutum ya zage dantse wajan yin Azumi a wannan watan, saboda fadin Annabi : "Mafificin Azumi bayan Ramaān shi ne Azumi a watan Muharram" kamar yadda Muslim ya rawaito.

Amma Wanda ya fi muhimmanci shi ne na ranar goma ga wata, sai kuma na ranar tara, Annabi yana cewa: "Azumin ranar goma ga wata yana kankakare zunubin shekara ɗaya" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1162), sannan yana cewa: "Idan na rayu zuwa badi zan azumci ranar tara ga MUHARRAM".

 Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments