Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Rage Yawan Motsawar Sha'awa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalama alaikum dan Allah mlm wanine yake da zafin sha'awa kuma beda halin yin aure ko akwai maganin da zai ragemasa ita na islamic wanda baya da cutarwa

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalamu warahmatullahi

Daga cikin abubuwan dake rage yawan motsawar sha'awa ajikin Ɗan Adam, akwai :

1. Kiyaye dokokin Allah ta fuskar runtse idanuwanka daga kallon haram, ko karanta haramtattun abubuwa. Ko kuma furta haramtattun kalamai (Na batsa).

2. Yawaita yin azumi da nafilfil da kuma mayar da hankali akan abin da ya shafi lahira. Musmman mutuwa, Kwanciyar Ƙabari, da sauransu.

3. Yawaita shan Lemon tsami (Idan baka da Olsa). Ko kuma Jar kanwa ('Yar Ƙalilan).

4. SHAJARATU MARYAM : Bishiya ce wacce ake amfani da ita don magance matsalolin Mata. Amma Idan namiji yasha, tana cire masa sha'awa sosai daga jikinsa da zuciyarsa. Da ita ne Mutanen da chan, irin masu yawan ibadan nan suke amfani domin samar ma kansu cikakken hutu daga wannan.

Allah ta'ala yasa mudace.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPZfEeHb8CD1SWAkK

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments