Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hirar Batsa (Sez-Chat)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalmu alaikum, Malam wallahi na Shiga bala'i Ka taimakeni😭 Nidai mutum ne Wanda Allah ya jarabceni da karfin sha'awa Kuma ban taɓa yin zina ba To Amma wannan WhatsApp ɗin ya haɗani da mutanen banza an shigar dani wani group na batsa hotunan banza da videos ɗin banza Duk ina ganinsu Rana ɗaya sheɗan yayi tasiri a kaina wlh Malam wata yarinya da muka haɗu da ita har hoton farjinta ta turomin nima na tura mata nawa, Sai da na Riga na aikata hakan Abin yaketa damuna Na tuba Malam Allah zaiyafemin kuwa? Sannan kuma Malam wane abu zan dage dayi Wanda Allah bazai kamani da laifin ba Wallahi nayi nadama.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To itadai hirar da akeyi ta batsa atsakanin Namiji da Mace ta hanyar Ƙiran Waya ko rubutaccen saƙo, ko tura tsiraicin juna kamar yadda akafi saninta da sunan Sez-Chatting, ko Shakka babu wannan wata Musibace da Fitina wacce ta addabi Al'ummar wannan Zamani damuke cikinsa, tun daga kan Maza har Mata, masu aure da marasa aure, kuma wajibine akan masu wannan aiki suyi gaggawar tuba zuwa ga Allah.

Azaba mai radadi da wulakantarwa ta tabbata bisa budurwar da saurayi da suke SEZ-CHAT (chatting na batsa) indai har basu tuba. koda kuwa ya kai mata sadaki, Allah zai kwashe albarka gareshi shi da ita, Kuma yana daga cikin hanyar da zata kaika zina.

Zina dai wani aiki ne da Allah Ya hana dukkan musulmai aikatawa, kai ba ma aikata zunan ba, hatta kusantar ta ma Allah madaukakin sarki Ya hana. Allah Ya gargademu a cikin Alkur’ani mai tsarki cewa ‘kada ku kusanci zina. sannan kuma manzon Allah Yace ‘mazinaci bayayin zina alokacin da yake cikin imani.

Maganar yafewa Kuwa: Allah yana yafe kowanne zunubi da bawa ya ke aikatawa, idan ya tuba, amma banda shirka wato hadashi da Wani bawansa wajan bauta. Kamar yanda Ayoyi da hadisai ingantattu da dama Suka nuna, Amma akwai sharudan tuba:

1. Dena zuzunubi.

2. Nadama Akan saɓon​​.

3. Ya Ƙudurci niyyar, bazai sake aikata aikin ba.

 ​​​​Idan aka rasa ɗaya daka cikin ukun nan tuba bai tabbata ba. Sannnan kuma banda hakki mutane iyaka hankinka tsakaninka da Allah. Sannan kuma kadege da neman gafarar Allah, ka nesanci duk abin da zai kai ka ga aikata zantukan da zasu tada maka sha'awa, Sannan ka lizimci azumin lafila saboda sha'awa da take damunka, da ya waita istgfari.

Allah ya tsaremu.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMZMrWDz1y7sYye2znU

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments