Kîshi Rahama Ne Ko Azaba // 51

    11) Sai kuma 'yancin fadin ra'ayi a kan wace take kishi da ita, da irin kalmomin da take jefawa wadanda ita ba za ta so a yi amfani da a kanta ba, mu dubi kayan sakawa, za ta ce "Wance ana ba mu kudi mu sayi kaya amma sai ta rage ta sayi masu arha" ko "Ba ta iya zaben atamfofi masu kyau ba" koda a ce maigidan yake sayo musu ya ba da dinki sai ta yi maganar cewa ba ta iya daurin dankwali ko zane ba, ko ta ce hijabin da take sakawa bai yi daidai da atamfar dake jikinta ba, ƙoƙarinta dai a ce amaryar ba ta iya wanka ba.

    Ta kowani irin yanayi mace me yawan kishi ba za ta iya zama haka kawai ba tare da tsokale-tsokale ba, da maigidanta zai yi maganar cewa lallen wata ya yi kyau, ko ba ta kushe ba gobe za ta yi nata, kuma dole sai ya ba, idan ya yi shuru to dama ba lallen yake magana ba mai lallen ce, tasu da shi ta ƙullu kenan. Duk wata kwalliya da za ta yi dole sai ta ji ra'ayinsa a kai, masamman in ta ga yana kallon na wata. Da zai ga wani hoto ya ce daurin ya yi wa matar kyau, ka ba ta 'yan sa'o'i ƙalilan za ta je ta yi wanka ta yo irin wannan daurin don jin me zai ce?

    Matar aure ji take a duniyar maliki-yaumiddini ba wata mace kamarta a wurin mijinta, kuma ba za a taba samu ba har abada, don haka maigidanta ba zai yi maganar kowa ba sai tata. Abin tambayar anan: Shin masu irin wannan baƙin kishi suna kaiwa ga muradinsu ko akan sami akasi? Amsar dai akan samu, an sha ganin uwargida na bala'i kan ba wanda ya isa ya kawo diyarsa gidanta, takan niƙi gari ma ta je gidan wace za a auro ta ci musu mutunci son ranta, ba tare da ta damu da abin da zai biyo baya ba, buƙatarta kawai a ga abin da zai iya faruwa matuƙar suka kawo diyarsu gidanta ko suka bari ta auri mijinta. A ƙarshe akan yi auren ita kuma ta bar wa amaryar yaran ta sa ƙafa ta yi gaba.

    12) Ƙoƙarin sanin bayanai a kan kishiya ma wani yanki ne na babban kishi, yadda za ta riƙa bin diddigi sai ta san komai nata fari da baƙi "Wai da gaske ne baban wance a bazawara ya auro uwarta?" Ba wannan ce tambayar ba, ya aka yi ta zama bazawara ne? Wata takan so zuwa duk wani sha'ani na kishiya ko za a yi abin kunya a gabanta, duk kuma inda mata za su taru suna gulma za ta yi ƙoƙarin zama a wurin ko za ta yi tsuntuwar zance. Duk wadannan bayanan da take tarawa tana adana su ne idan an dan sami sabani a tsakaninsu ta juye mata su gaba daya.

    Akwai matan da sam-sam ba su damu da abin da za su ji a daya bangaren ba, in ma ta ji ana tsegumin wancan da cewa tana da mugun kishi ko wani abu mummuna takan tashi ta bar wurin, ba za ta bari a yi musayar yawu da ita ba, irin wadannan matan da wahala ka ji suna ƙoƙarin sanin wani abu na kishiya, ba su da wata manufa ta maida mata da wani martani. Wata za ta ce maka "Dole ka san halin da abokin zamanka yake ciki don ka san yadda za ka zauna da shi" a daidai wannan lokaci ba ta son kishiyar tata ta san wani abu game da ita ko ya yake kuwa, da magana kenan.

    Wasu na danganta kishi da cewa tsananin buƙatar mace ne da shimfida ke sa ba ta buƙaci rayuwa ita kadai a gidan mijin, amma da za ka yi hira da mata za ka iske wata kan yi wata biyu ma maigidan nata bai waiwaye ta ba, haka kuma take haƙuri da shi ba tare da ta nemi a raba auren ba, kenan ba wannan ne dalilin kishinta ba, ban ƙi ba in yana cikin dalilai, amma ba shi kadai ne ba, in mata na maganar shimfida ma za ka yi mamakin kasancewarsu da wasu mazan, wata za ta rantse maka da Allah ta kwashe sama da shekara biyu mijinta bai waiwayi shimfidarta ba kuma tana zaune da shi.

    Na zanta da wani mai sayar da maganin maza na gargajiya ya tabbatar min da cewa galibin masu karbar magungunan mata ne, ba tare ma da sanin mazansu ba, akwai likitan da ya tabbatar min da cewa mata na karbar magungunan ƙara ƙarfin maza a wurinsu, kenan maza na da rauni tun farko, ƙila wannan kadai ba zai zama jigon da mace za ta yi rigima da kishiyarta ba. Wasu na ganin kwadayin abin duniya ne, tana son a bar musu gado ita da yaranta. Wannan har na kusa amincewa da shi sai kuma na ga ba matan masu sukuni kadai suke yin kishi ba har da matan wanda bai da komai ma, zancen gaskiya in ka ga kishi ya yi tsanani ma a gidan da babu ne, suna tare wuri guda kowa na ganin kai-koman dayar.

    A inda duk suke da abin yi, kowa take da bangarenta na daban, ta shagala da kasuwancinta, da wahala ta tuno kishiyar da wani abu, a nan ma ban ƙi gado na daya daga cikin manyan dalilai ba amma shi kadai ne ba. Wasu kan ce "'Yan abubuwan da maza kan riƙo ne yayin dawowa gida" da haka ne ba za a sami kishi a gidan da komai yake a wadace ba. Zan so a dauki kishi a matsayin dabi'a ta mace kawai, don ko kafin auren ma suna abinsu, ka ga kuwa ba wata maganar shimfida, ko ta gado bare kuma tsarabar kasuwa.

    Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

    **************************
    Daga:  Baban Manar Alƙasim
    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.