𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Macece take tukin mota saita kade mutum yaya za ta
yi azumin kaffara saboda mace tana al'ada duk wata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Kaffarar kisan kuskure ita ce: 'yanta baiwa da
biyan diyyah, ko azumin wata biyu ajere, wanda bai samu abun da zai 'yanta
baiwa da shiba ko yayi azumi sittin ajere ba, babu laifi agareshi, ba'a ciyarwa
akaffarar kisan kuskure abisa mafi rinjayen maganganun malamai.
Allah maɗaukakin sarki ya ce
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَنْ يَقْتُلَ مُؤْمِنًا إِلَّا خَطَأً ۚ وَمَنْ قَتَلَ مُؤْمِنًا خَطَأً فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ وَدِيَةٌ مُسَلَّمَةٌ إِلَىٰ أَهْلِهِ...
Bai halatta ga mumini yakashe ɗan'uwansa mumini ba saifa inda kuskure,
duk wanda yakashe mumini tahanyar kuskure kaffararsa shi ne ya 'yanta baiwa
mumina dakuma diyyah dazai mika ga ahlin wanda yakashe.
...
ۖ فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً مِنَ اللَّهِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Duk wanda bai samuba sai yayi azumin wata biyu
ajere dan tuba ga Allah, Allah yakasance masani mai hikima.
Saboda haka idan azumin wata biyu yahau kan mace
mai al'ada, Saita fara azumin tana cikin azumin sai jinin Al'ada yazo mata, to
azuminta nawata biyun bai yankeba, zata sha azumin sannan saita rama kwanakin
datayi hailar, saita dora lissafi tacika wata biyun, domin haila wani
al'amarine da Allah yadorawa mata ita, bata da iko akai, wannan ijma'ine
atsakanin malamai.
Ibnu ƙudama rahimahullah acikin Almugni ( 8/21) ya ce
" malamai sunyi ijma'i akan mace mai azumin
wata biyu ajere, idan haila tazo mata kafin ta kammala, zata rama kwanan hailar
idan tai tsarki, domin haila baza'a iya kauce mata acikin wata biyu ba, saidai
idan zata jinkirta harzuwa tadaina hailar, wannan kuma zaikai ga azumin yashiga
garari bazata samu damar yin saba"
Misali ace zatai azumin kaffarar awatan muharram
da safar kuma kowanne acikinsu hailarta kwana bakwai ce, to zata sha azumin waɗannan kwana bakwai ɗin nakowanne wata, saita ramasu dazarar
watan safar yakare, babu jinkiri saitayi azumi goma sha huɗu ajere, nafarkon watan rabi'ul Auwwal.
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.