𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene Hukuncin Barka Da Sabuwar Shekarar
Musulunci, Da Turawa Mutum Sako Kanayi Masa Addu'ar Alkhairi Da Albarka
Asabuwar Shekarar Daya Shiga?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Shaik Usaimeen rahimahullah ya ce Idan wani yafara
yi maka barka da sabuwar shekara ka amsa masa, amma kada kafara yiwa kowa
wannan shi ne dai-dai awannan mas'alar da wani zaice maka inai maka barka
dasabuwar shekara zakace: masa Inaima barka da sabuwar shekara Allah yabamu
alkhairi yasanya mana albarka acikinta, saidai kada kafara yiwa mutane domin
ba'a samu koda mutum ɗaya
cikin magabata Nakwarai sunaiwa juna barka da sabuwar shekarar musulunci ba,
Saidaima Su salaf basa daukar muharram amtsayin farkon shekarar musulunci, sai
azamanin kalifancin Umar bin khaddab Allah yakara yarda dashi.
Imamu Ahmad bin hambal rahimahullah ya ce Bana
fara yiwa koya barka da wani idi cikin idukan musulmai amma idan wani yafara
yimun ina amsa masa domin amsa gaisuwa wajibine, Amma fara yiwa wani barka ba
sunnah bace da'akai Umarni da ita, kuma baya cikin abun da aka hana.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.