Ticker

6/recent/ticker-posts

Abin Da Ake Dubawa Idan Saurayi Yazo Neman Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

A Matsayina Na Mahaifi, Me Ya Kamata In Duba Idan Wani Yazo Da Nufin Neman Auren 'Yar Mu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To Ɗan'uwa matakin farko shi ne a matsayinka na uba ya kasance kana da karfin iko a cikin gidanka wannan kuma baya samuwa sai fa idan matarka ta kasance mace mai addini, ba mai burin abin duniya ba, wannan shi ne zai baku dama a matsayinku na iyaye ku iya bawa ýaýanku tarbiyya ta addini, tare da fahimtar dasu fifikon addini da kyawun ďabi'u Akan dukiya da 'kyale 'kyalen duniya da sauransu.

Acikin hadisi Annabi yayi muku wasiyya ku iyaye cewa: IDAN WANDA KUKA YARDA DA ADDININSA DA 'DABI'UNSA YA ZO MUKU (NEMAN AURE) TO KU AURA MASA IDAN KUMA KUN 'KI TO ƁARNA DA FASADI ZASU WANZU A BAYAN 'KASA [Tirmizi, Ibn majah].

Wannan ita ce wasiyyar manzon Allah gareku iyaye a matsayinku na iyaye idan samari sunzo neman auren ýar ku, Kar ku duba Dukiyarsa ko nasabarsa kyawunsa Addininsa, Abin da ake dubawa shi ne ďabi'unsa Bawai ababen mure rayuwar duniya ba, Addini da ďabi'u sune manya manyan abubuwan da ake dubawa Sabida haka ingantacciyar a'kida da kyakkyawar mu'amala sune ma'aunin da Annabi yayi mana umarni dasu yayin da zamu aura ko zamu aurar, kema a matsayinki na budurwa ki fifita addinin saurayin da yazo wajenki da kyawawan halayensa matukar dai kina son jin daɗin zaman auren.

Misali da ace samari biyu zasu zo neman auren ýarku ďaya saurayin yana da dukiya da nasaba da kyawu, Amma kuma bashi da addini da kyawun ďabi'u, Shi kuma ďaya saurayin bashi da dukiya da nasaba da kyawu Amma yana da Addini da kyawun ďabiu to shi yafi cancanta ku bashi ýar ku matukar yana da sana'ar da zai iya daukan nauyin ciyar da ita shayar da ita da tufatar da ita da kula da lafiyarta koda kuwa  bashi da gida da mota matukar dai yana da ikon kama musu hayar muhallin da zasu zauna tare da daukan dawainiyarta gwargwadon ikonsa.

Abu na gaba kuma Bayan kun aminta da ďabiun saurayin to sai ku bawa yarinyar hakkinta ma'ana sai ku basu dama su fahimci juna ita da saurayin Sannan kuma sai ku koya mata ISTIKHARA Ma'ana sallar neman za'bi domin ta nemi za'bin Allah game da saurayin ta hanyar rokon Alkahirinsa da neman tsarin Allah daga sharrinsa.

Amma idan saurayi yana da kuɗi da kyawu ko nasaba Ga kuma Addini to wannan kuma shi yafi Domin Dukkan ababe Huďun nan Ababe ne da ake bukatarsu a rayuwar aure, Abin da ake so dai kada a bi son duniya cikin lamarin aure Amma idan Addini da duniyar sun samu to haka aka fi so

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RzgCwA3JFiEKl8j5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments