Ticker

6/recent/ticker-posts

Dattijo Alhaji Nuhu

Dattijo Alhaji Nuhu

Dattijo Alhaji Nuhu ke nan wanda mahaifansa daga  Kano suka tafi wannan Kasar ta Burkina Faso fiye da  shekaru 200 da suka wuce, a Ouagadougou aka haife shi. Attajiri ne  daga harkar noman kayan marmari na lambu(Orchard) wanda ta hanyar  ne ya mallaki ƙaddarori masu yawan gaske a ƙasar musamman gidaje da filaye. Ya baiwa al'ummar Hausawa da sauran Kabilu Musulmai da ba 'yan ƙasar ba wani makeken fili a Zango dake Birnin Ouagadougou kyauta suka gina Masallacin Juma'a. A lokacin da Marigayi Thomas Sankara ya yi juyin mulkin da ya zamo sanadiyar zaman shi Shugaban Ƙasar, ya soma gyara fasalin tsarin Birnin Ouagadougou sai wannan Masallacin ya faɗo cikin wuraren da za a rushe. Al'ummar da suka mallaki wannan Masallacin suka yi mashi ke ƙorafi akai sai ya naɗa kwamitin da zai gano silar samuwar wannan wuri idan ba ta haramtattar dukiya ne aka samar dashi  ba ya yi masu alƙawalin ba zai rushe shi ba, za a zaud'a daga gefen shi. Sanin silar dukiyar Alhaji Nuhu ne sanadiyar tsirar Masallacin(2017 ne na ziyarci ƙasar)

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments