Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'anar Kudu Da Arewa Da Ake Ambata A Wasan Dambe

Ɓangarorin dambe ne da ake rabawa gida gida. Yandamben arewa galibi sun fito ne daga jihohin Zamfara da Sakkwato da kabi da wani sashe na jihohin Naija da katsina amma haka bai hana a same su inda ake samun kudawa,misali,Nabacirawa da Bala Yaro da Sani yaron Mamman da Hussaini Ɗankwalle na Toronkawa wadanda yan jihar Kano ne da Kaduna da Katsina. Kurdawa kuma, ya ƙunshi yandamben da suka fito daga yankunan Kano har zuwa Maiduguri. Amma yanzu Arewa ko Jamus ta rabu biyu. Akwai arewatawa akwai gurumaɗa daga jihar kabi. Har wa yau,akwai yandamben da ake kira Daurawa, wanda mutanen Daura ne.

Daga:
Zauren Makaɗa Da Mawaƙa

Post a Comment

0 Comments