Ticker

6/recent/ticker-posts

Dattijo Alhaji Nuhu

Dattijo Alhaji Nuhu
Dattijo Alhaji Nuhu ken an wanda mahaifansa daga Jihar Kano suka tafi wannan ƙasar ta Burkina Faso fiye da shekaru 200 da suka wuce. Shi a Ouagadougou aka haife shi. Attajiri ne sosai daga harkar noma musamman kayan marmari na lambu(Orchard) wanda ta hanyar su ne ya mallaki ƙaddarorin masu yawan gaske a ƙasar musamman gidaje da filaye. Ya baiwa al'ummar Hausawa da sauran Kabilu Musulmai da ba 'yan ƙasar ba wani makeken fili a Zango dake Birnin Ouagadougou kyauta suka gina Masallacin Juma'a. Shi ne ya gina masallacin da kuɗinsa. A lokacin da Marigayi Thomas Sankara ya yi juyin mulkin da ya zamo sanadiyar zaman shi Shugaban Ƙasar, ya nemi ya gyara fasalin tsarin Birnin Ouagadougou sai wannan Masallacin ya faɗo cikin wuraren da za a rushe. Al'ummar da suka mallaki wannan Masallacin suka yi mashi ke ƙorafi akai sai ya naɗa kwamitin da zai gano silar samuwar wannan wuri idan ba ta haramtattar dukiya ne aka samar dashi  ba ya yi masu alƙawalin ba zai rushe shi ba, za a zaud'a daga gefen shi. Sanin silar dukiyar Alhaji Abdu ne sanadiyar tsirar Masallacin
Ya zuwa yau, Asabar 08/07/2023 Alhaji Nuhu ya na nan raye a cikin iyalinsa, a Ouagadougou, Babban Birnin Ƙasar Burkina Faso. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com

Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 


Post a Comment

0 Comments