Ɓarna Ba Ki Da Daɗin Ji, Balle Gani: Tsokaci A Kan Matsayi, Da Tasirin Ɓarna A Mahangar Ga Al’adar Bahaushe

     

    Daga
    Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad

    SASHIN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR SULE LAMIƊO, KAFIN HAUSA, JIHAR JIGAWA, NIJERIYA
    07030803404
    Email: muazusaadukudan299@gmail.com

    Tsakure

     Wannan nazari zai dubi ɓarna matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe. Maƙalar zata kawo bayanai tare da fito da rawar da sanda take takawa a yanayin zamankewar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar ɓarna tare da ire-irenta, fagagen da ake yinta, da dalilan yinta, da masu yinta. Nazarin zai kawo irin yadda zamantakewar Bahaushe ta ɗauki ɓarna muninta da kuma sakamakonta, kamar a wajen harkar neman abinci ko sana’a, da magani da sauransu. Haka kuma za a kalli irin yadda Hausawa kan yi kasuwancin sanda a tsakaninsu. Ban da wannan za a dubi irin halin damuwa da wasu masu riƙe sanda kan shiga idan suka buƙaceta ba su samu ba. Maƙalar zata kawo jirwayen sanda a adabin Bahaushe na baka, daga ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

    1. 0 Gabatarwa:

    Wannan maƙala na da ƙudurin yin nazari a kan ɓarna matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe. Maƙalar zata kawo bayanai tare da fito da irin kallon da ake yi mata tare da rawar da ɓarna take takawa a yanayin zamankewar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar ɓarna tare da ire-irenta, da fagagen da ake yinta, sannan da dalilan yinta, da lokutan aukuwarta ko aikatata, da wuraren faruwarta da kuma masu yinta. Tun daga mutane, da dabbobi, da tsuntsaye, da ƙwari da tsutsotsi da kuma wasu abubuwa marasa rai. Bugu da ƙari wannan nazari zai hararo irin yadda zamantakewar Bahaushe ta ɗauki ɓarna, muninta da kuma sakamakonta, tare matsayin masu yinta, kamar a wajen harkar neman abinci ko sana’a, da magani da sauran harkokin yau da kullum. Haka kuma za a kalli irin yadda Hausawa kan yi, ko kuma a dubi irin halin damuwa da wasu mutane kan shiga idan suka ji ko suka samu labarin an yi masu ɓarna ballanta kuma a yi a gabansu wato su gani da idonsu. Wannan dalili ya sanya na yi wa maƙalata take da cewa: “Ɓarna

     Ba Ki Da Daɗin Ji, Balle Gani” Maƙalar zata kawo dukkan bayanai ta mahangar Bahaushiyar al’ada, sannan kuma da jirwayen ɓarna a adabin Bahaushe na baka, daga ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

    1. 2 Ma’anar Ɓarna:

    Ayuba(2015:67)ɓarnace-ɓarnace, Lalata abu da gangan, ta’adi, ɓata abu da yara kan yi wajen wasa ko ƙiriniya, ɓatawa mutum rai. Lalata abu a sababin ruwan iska, wuta.

    B. U. K. (2006:64)ta’adi ,faɗa tsakanin dangi, kuskure wajen karatu musamman karatun ƙur’ani, lalata. Birai sun yi ɓarna, wuta ta yi ɓarna a gona.

    Bargery, G. (1993:89)Lalata, ko ta’adi, ko ribar da fada tsakanin dangi, almubazzaranci. [1]Encater Dictionary sata ko lalata, ko gusar da ingancin, ko amfanin abu, ko gurbata wani abu. [2]

    Bisa la’akari da bayanai daga wasu masana kai tsaye ana iya cewa: Ɓarna na nufin lalata ko ɓata wani abu daga matsayinsa na daidai zuwa matsayinsa na rashin daidai. Ko illata wani abin amfani, bisa kuskure ko kuma da gangar watau ana sane don mugunta.

     inda zai zama sai dai a zubar ko a rasa shi gaba ɗaya.

    1. 3 Faɗaɗa Ma’ana Ɓarna:

    Bahaushe kan ɗauki Kalmar ɓarna ya faɗaɗa ma’anarta daga asalin ma’anarta ta farko zuwa sabuwar ma’ana, a inda an san cewar ɓarna a aikace take, in an yi ta, ana ganinta a zahiri. Kuma a mafi yawa, abu mai rai kan yi ɓarna, amma sai Bahaushe ya faɗaɗa ma’anar ɓarna ga wasu marasa rai, da waɗanda ba a iya gani. Kamar Iska da Ruwa da Wuta da Zamani.

    1. 4 Ire-Iren Ɓarna:

    1.      Akwai ɓarna ta gajeren lokaci, ita ake kira “Ƙaɗa’an”, ko “Zubar-kago”.

    2.      Akwai ta dogon lokaci.

    3.      Akwai kwatsam, sai dai haƙuri (Ɓarin miya a yashi).

    4.      Akwai Ɓarna tura haushi.

    2. 0 Dalilan Da Kan Jawo Ɓarna:

    A Bahaushen tunani, an yi imanin cewa, komai ba ya rasa sanadi. Kamar yadda Ɗangoma mai Garaya yake cewa:

    “Ba zan ƙi dalili ba,

    Dalilin Aure tsarance”.

    Bisa wannan dalili, ya sa al’adar Bahaushe ta rarrabe dalilan ko ayyukan da kan yi sanadin aikata ɓarna.

    1.      Karambani.

    2.      Wauta.

    3.      Gaggawa.

    4.      Ganganci.

    5.      Fushi.

    6.      Gardama (Jayayya).

    7.      Kuskure.

    8.      Tsautsayi.

    9.      Ƙyuiya.

    10.  Son ganin Ƙwaƙwaf.

    1. Karambani: A wani lokaci karambani kan haifar da ɓarna, mutum bai iya abu ba, ko bai san kan shi ba, ko ba a sa shi ba, saboda karambani sai ya aikata wani abu, sai ya zama ɓarna. Shiyasa Bahaushe ya ce, “Karambani gajere, kowa ya taɓa shi zai yi tsawo. An fi irin wannan a wajen Yara.

    2. Wauta: A wani lokaci, wauta kan jawo ɓarna, sai a aikata ɓarna saboda ƙarancin hankali.

    3. Gaggawa: Gauƙa ko ci-da-zuci tare da ƙosawar saurin samun sakamako, kan sauya a aikata ɓarna.

    4. Ganganci: Akwai ɓarnar da kan faru wajen yin abu da gangan, an san abin ba zai yiwu ba, amma sai a ce, “bari mu gwada mu gani”, sai ta ɓaci kuma a zo ana nadama.

    5. Fushi: Aiki cikin fushi ko magana cikin fushi kan yi sanadiyar a aikata ɓarna.

    6. Gardama (Jayayya): Duk inda aka samu mutum biyu (2) ko fiye da haka suka yi jayayya a kan wani al’amari, to matuƙar ba a samu daidaito ba, aka yi aikin, to ana iya samun ɓarna. Kamar yadda Alhaji Musa Ɗanƙwairo ke cewa:

    “Gardama ma-tsirar sababi,

    An bar gama ta ran wani bai ɓaci ba”.

    7. Kuskure: Rashin iya abu ko manta yadda ake yin shi, ko kauce wa wani umarni. Shi ma irin wannan kan sa a aikata ɓarna.

    8. Tsautsayi: Akwai ɓarnar da kan faru a dalilin tsautsayi, mutum ya saba yin abu, kuma ya ƙware, ya san kan shi, amma sai a samu tsautsayi. Haka kuma, wata ɓarnar ta faru, amma ba ta bayyana ba, sai wani na taɓawa sai ta bayyana. Sai a ce wane ne, to a nan ya taka sawun ɓarawo.

    3. 0 Masu Yin Ɓarna:

    Babu shakka, aiki ba ya yin kan shi sai ga mai yin shi. Haƙiƙa akwai masu aikata ɓarna kamar yadda al’adar Bahaushe ta keɓe su, sun haɗa da:

    1.      Mutane.

    2.      Dabbobi.

    3.      Ƙwari / Tsutsotsi.

    4.      Tsuntsaye.

    5.      Wasu abubuwa.

    Bisa wannan zai sa mu lura cewar, abubuwan da kan aikata ɓarna akwai masu rai da marasa rai.

    1. Mutane: Ta fuskar mutane, akwai Yara. Shi ne a kan ce, “Hannun Biri ba ka zama kurum”. An danganta birin da yaro, saboda wasu ɗabi’u, kamar karambani da kwaikwayo, wanda kan sa su aikata ɓarna. Wani abin ya ga manya na yi, amma saboda ya kwaikwaye su sai ya aikata ɓarna, kamar abin da ya shafi Abinci ko na kayan aiki. Yaro,da mahaukaci,da mata.

    2. Yaro Da Ɓarna: Ɓarna na nufin lalata, la'anta, ko ɓata wani abu da hannu ko ƙafa ko wani ƙarfe. Tana iya yiwuwa a fasa ko huda ko yaga ko kuma a rusa da sauransu. Bahaushe na alaƙanta ɓarna da yaro ne, saboda wasu dalilai kamar haka: -1. Ƙarancin hankali da tunani 2. Son ganin ƙwa-ƙwaf. 3. Kwaikwayo. 4. Karambani. 5. Tsautsayi

    1. Ƙarancin Hankali Da Tunani: Bahaushe ya yi imani cewar lallai yaro fama da qaranci ko kuma raunin hankali da na tunani, kuma ba ya tunanin abin da zai je ya dawo. Bisa wannan dalili ne ya sa bahaushe kan ce yaro mai varnar rashin dalili. Haka kuma da zarar tunanin da zuciyar ta riya masa sai ya aikata. Zai iya xaukar abu komai amfaninsa ya fasa.

    2. Son Ganin Ƙwa-ƙwaf: Hujjoji marasa iyaka da suka tabbatar da haka, cewar yaro akwai shi da son ganin ƙwaƙwaf, wannan ya sa komai yaro ya ji ko ya gani, sai ya tambaya ko ya tava, balle kuma aka ce babu wani babba da zai tsawatar masa. Mafi yawa yara kan so su san mene ne wannan? Da me aka yi? Mene ne a ciki? da sauransu. A wani lokaci varnar yaro kan tafi tare da wayau ko shekarunsa. Wani yaron idan ya yi varna ya kan gudu, ko ya voye saboda kar a yi masa faɗa, akwai inda yaro bai gudu kuma bai voyewa, yana iya faɗa cewar shi ne ya yi kaza, saboda bai san daraja da amfanin abin ba, shi dai ya ga abin da aka haɗa aka yi.

    3. Kwaikwayo: Al'adar Bahaushe ta jingina varna ga yaro,bisa dalilan kwaikwayo. Allah Ya yi yaro da son kwaikwayon abin da ya ga ana aikatawa. Yaro da biri akwai su da kwaikwayo. A wani lokaci yaro ganin kwaikwayon abin da ya ga ana yi kan ja shi ga varna, kamar ɗaukar wani abin aiki garin ya kwatanta abin da wani yayi, sai abin ya fashe ko ya karye. A wasu lokutta yaro kan cutar da kansa a dalilin yin varna, misali wajen aikata wani abu da ya ga wani ya aikata.

    4. Karambani:Kowa ya san yara iyayen karambani ne, wannan dalili ne ya sanya ake alaqanta varnar yaro da karambani. Akwai wata karin magana mai cewa: “hannun biri baka zama kurum” wannan magana ba da biri ake yi ba kai tsaye ba a'a, da yaro ake yi saboda zai yi wuya a ajiye wani abu a gaban yaro, ko kuma ya tarar an ajiye bai tava ba. A wani lokaci daga tavawar ne sai varnar ta auku. A kan ɗorawa yaro ɓarna ne ko da ba shi ya yi ba, saboda an san shi da karambani har akan ce:”yaro taɓa ba a saka ba” ko “karambana ko ka ga dokin sarki”.

    5. Tsautsayi: Tsautsayi na nufin, wani abu ya faru da mutum bisa kuskure ba tare da ya yi niyyar aikata abin ba. Bahaushe na ganin cewa wani lokaci wata ɓarnar na aukuwa ne bisa tsautsayi, ma'ana yaro ba da gangar ya yi ba. Ko da yake ba a cika amincewa da wannan dalili ba, bisa dogaro da sanin waɗancan dalilai na karambani ko kwaikwayo, amma kuma wani lokaci a kan karɓi uzurin. A ƙarshe ana iya cewa ɓarnar yaro na faruwa ne bisa waɗannan dalilai da suka gabata da ma wasu da ba a kawo ba.

    3 Mahaukaci: Shi kuma Mahaukaci, a kasancewarsa ba shi da hankali, kan sa ya aikata ɓarna. Wannan ya sa ake kauda kai da ɓarnar da ƙaramin Yaro ko Mahaukaci ya yi, amma idan Mahaukaci ya je yana ba da labarin ɓarnar da ya yi, to sai danginsa su biya wannan ɓarnar.

    Mata: Ana danganta ɓarnar Mace bisa waɗansu dalilai kamar haka: 1. Kuskure. 2. Tsautsayi.

    3.      Ganganci.

    1. Ta Kuskure: Shi ne ta iya abin, sai mantuwa ta sa ta yi kuskure.

    2. Ta Tsautsayi: Wannan shi ne , ta iya abin kuma ba ta manta ba, sai a samu wata ƙaddara ta gitta a aikata ɓarna bisa tsautsayi. Ana cewa, “Rugum kwaram ɓarin mai ɗaki, in ka ji shiru ita ta yi abinta”. Haka kuma ana cewa: “Kwaram haɗa kaya”.

    3. Ganganci: Akwai ɓarnar da kan faru, wadda mace ta yi cikin ganganci, musamman idan ta yi aiki cikin fushi, kamar lokacin da baƙonta (Jini) zai zo, ko kuma tana wanki (al’ada). Ko tana da yaron ciki, ko ta yi faɗa da mijinta, ko an yi, ko za a yi mata kishiya. Kamar wata Waƙar Dandali ko Gaɗa, inda ‘Yanmata ke cewa:

    Amshi: Iye

    Mai waƙa: An yi mata kishiya tana watsi da hatsin tuwo

    Amshi: Iye

    2. Dabbobi: Dabbobi, halittu ne masu ƙafafu huɗu na gida da na daji”[3] “dabbobi, dukkan halitta mai ƙafa huɗu”. [4] “ wasu, halittu ne masu ƙafafuwa huɗu jikinsu lulluɓe da gashi”. [5] ‘dabba’ muna nufin dukkan abu mai rai ne in ka ɗebe tsire-tsire, watau ba nufi muke dabbobin gida da daji kaɗai ba, amma har tsuntsaye da su macizai da kwaɗI da kifaye. [6]

    Babu shakka al’adar Bahaushe ta danganta ɓarna daga wasu dabbobi na gida da na dawa, manya da ƙanana. Su ma ɓarnarsu tana iya faruwa a dalilai kamar haka:

            i.            Faɗa a tsakaninsu.

          ii.            Dalilin neman abinci ko abin sha.

       iii.            Dalilin gyara muhallinsu.

       iv.            Ko Barbara a tsakaninsu.

    Faɗa Da Taƙaddama

    Ma’anar faɗa: Rigima da tashin hankali tsakanin mutum biyu ko fiye. Gwabzawa jiki da jiki don rikici, ko yaƙi da makami tsakanin mutane. Faɗa na nufin saɓani ko rashin jituwa, wanda kan jawo husuma har zage zage a wani lokaci har da doke- doke a tsakanin mutane ‘yan adam. To su ma dabbobi akan samu irin haka a tsakaninsu, duk da yake ba sa magana ana ji a asarari. Dabbobi su ma sukan yi faɗa, wannan kuwa na faruwa ne bisa wasu dalilai. Kamar yadda Bahaushe ke cewa ko tsakanin harshe da haƙori ma akan saɓa. To haka yake su ma dabbobi ba su tsira ba. Wannan kuwa na faruwa ko da a jinsi ɗaya ne yasu-yasu, ko da bare na wani jinsi baƙo ko da Ɗan adam.

    Barbara: Bahaushe na da wani tunani, game da rayuwar dabbobi da alaƙarsu da barbara. Bahaushe na ganin dabbobi kan yi barbara ne a wurare daban-daban, kuma a lokuta daban-daban, sannan bisa dalilin hakan sukan yi barna. Dabbobi kan yi faɗa ne, a wani lokaci a wurin kiwo don cin abinci, ko shan ruwa, ko a wurin kwana, watau muhalli ko kuma a wurin hutawa. Dangane da lokuta kuma da dabbobi kan yin faɗa ya danganta ne da irin jinsunsu. Wasu dabbobin sukan yi faɗa ne da dare, wasu kuma da rana suka fi yin faɗa. Wasu kuma sai lokacin da suka haihu, waɗanda su ne suka fi yawa. Babban dalilin da kan sanya su faɗa, shi ne don kare ƙananan ‘ya’yansu, wanda kan iya jawo ɓarna. Ta fuskar dalilai kuwa da sukan sanya dabbobi faɗa, ana iya cewa sukan yi faɗa ne a wani lokaci, saboda nuna fin ƙarfi, ko ƙwatar kai ko kare kai. A wani lokaci kuma saboda neman abinci. A wani lokaci kuma saboda zumunta kamar faɗan taron dangi. Akwai faɗan tsana, a wani kuma saboda ramuwar gayya, amma wasu dabbobin faɗa ɗabi’arsu ce, haka Allah Ya haliccesu, don halinsu ke nan. Duk a ƙarshe faɗa kan yi sanadin ɓarna.

    Dabbobi kan yi faɗa a tsakaninsu. Wannan yana faruwa ne a tsakanin dabbobi. Na gida ɗaya yasu-yasu ko da kuwa jinsinsu iri ɗaya ne. Misali tsakanin tumaki, kamar inda akan samu faɗa tsakanin rago da rago sukan yi karo da juna. A wani lokaci saboda tunkiya mace, ko kuma tsakanin tunkiya da tunkiya don abinci. Bugu da ƙari, ƙananan dabbobi, su ma ba su tsira ba. Kamar ƙadangaru kan yi faɗa da junansu. Haka macizai su ma sukan yi faɗa ya su-ya su. Bayan wannan kuma akwai wasu dabbobin da ba jinsi ɗaya ba, sai dai zaman gida ɗaya ya haɗa su, kamar kare da mage, haƙiƙa ba’a shiri. Don haka ake samun faɗa a tsakaninsu. Haka kuma tsakanin mage da maciji, ko bushiya da maciji. Faɗan karnuka a tsakaninsu yafi aukuwa ne a wurin barbara, saboda karya mace, ko kuma a wajen farauta watau kama abinci kamar nama.

    Neman abinci: Tabbas kiwo, ko ruwa kan sanya wasu dabbobin faɗa a tsakaninsu, ko da wani baƙon jinsi da ya yi kutse. Wannan kuwa ya haɗa dabbobin gida da na daji. Misali tumaki da awaki sukan yi faɗa a wurin cin dusa a wurin cin abinci. Haka su ma na daji, kamar zaki, ko damusa, ko kura da sauransu. Wasu dabbobi yunwa ce kan sanya su zama mafaɗata don su samu abinci. Dangane da Dabbobin dawa da Bahaushe ke alaƙanta su da ɓarna, sun haɗa da Biri da Kurege da Jauji da Gyazbi da Yanyawa da Kura da Dila da kuma Giwa. Kowanne daga cikinsu su kan yi ɓarna bisa waɗancan dalilai. Amma Biri shi ne jagoran ma-ɓarnata a dabbobi, kamar yadda Amadu Doka Kaduna mai Kukuma yake cewa:

    “Kun ga fa ɓarna iri iri ce,

    Kun ga Yanyawa ta zo ta tona,

    Ta tsinta ta kai wa ‘ya’yanta,

    Sannan Kurege ya zo ya sata,

    Ya ɗiba ya kai ga raminsa,

    Shi kuma Jauji ya zo ya ɗiba,

    Ya ɗiba ya kai shi raminsa,

    To kun ga sun taru sun yi ɓarna.

    Amma an bar babban Biri da shi da mai gona,

    Komai za ka yi ringa yin tunani.

    Haka kuma Alhaji Musa Ɗanƙwairo yana cewa:

    A zuba ɓarna, jan Biri bai ɗara bika ba,

    Tsula na nan, ɗan ƙaraminsu,

    To shi ma yana da ƙarya gero.

    Akwai Karin Magana mai cewa: Laifin ba na yanzu ba ne wai an jefi biri da rani.

    Hannun biri baka zama kurum. , giwa ki ci mai gona na nan, giwa kin wuce kora da kara.

    Biri: Biri ya zama kamar shugaba a wannan fuskar, saboda biri ne kawai aka sani da ɓarna ta ban haushi da mamaki da rainin wayo. Bahaushe ya nazarci wannan halin biri, sai ya yi masa kirari da cewa; biri mai ɓarnar a faɗa, sannan ya lura da yanayin ɓarnar da biri kan yi, idan ya shiga wurare daban-daban.

    A wata hira da Malam Ashana Ɗankama Kano, cewa ya yi:

    Biri a Gonar Auduga: Bahaushe ya lura da cewa idan biri ya shiga gonar auduga, musamman wadda ta fara yin gululu. Wai sai biri ya ce ko ba za’a ci ba, bari a tsinke ko a ba da haushi, sai kawai ya fara tsinke gululun audugar nan yana zubarwa.

    Gonar Dawa: Idan biri ya shiga gonar dawa musamman in ta fara yin ciki(gululu), wai sai ya ce wannan wane ne take yiwa fushi, sai ya rinƙa kakkaryewa yana zubarwa, har sai ya gaji.

    Gonar Gero: Idan biri ya shiga gonar gero, musamman wanda ya fara zare kai amma bai yi ido ba, wai sai biri ya ce ‘bari mu ji ko da zaƙi?, sai kawai ya fara karye kan geron ta wajen sullen karan, yana yi taunawa yana jefarwa har sai ya gaji ko ya ji motsin wani mutum.

    Gonar Yalo : Idan biri ya shiga gonar yalo, sai fara da yin tsalle, sannan sai yace’da manya muke harka ba ruwan mu da taratsagutsa, shi ma mara zaƙi jifa mukai da shiya. wannan dalili ne yasa biri ɓarna a gonar yalo fiye da ko’ina. [7]

    Wannan ya sa ko an yi mutummutumi an sa a gona, sai dai ya hana wasu dabbobin ɓarna, amma ban da biri. Wannan yasa Musa Ɗanƙwairo a wata waƙa mai suna:Bello shiri nai yai kyau bai ya da gudun Arna ba, yake cewa:

     Jagora: Mutummutumi mutumin banza,

     Ko ka yi shi ka kai gona,

     ba za ya tsare komai ba,

     Ɓarnar da akai sai an yi,

     Don ba za ya tsare komai ba.

     Gindi:Bello shiri nai yai kyau ,

     Bai ya da gudun Arna ba.

    Ɗan waƙa da ya gabata ya nuna cewa mutum-mutumi kamar shigar burtu ne da ake yi wa wasu dabbobi, saboda a hana su yin ɓarna a gona. Biri shi kuwa, sanya wannan alamar ta mutum-mutumi a gona ba ya hana shi yin ɓarna. Dabarar da biri yake yi kuwa, ita ce, da ya shiga gona wadda aka sa mutum-mutumi, sai ya gwada ya ga mutum ne ko a’a ?. Da zarar ya gwada ya ga bai yi motsi ba, sai kawai ya cigaba da ɓarnarsa.

    Dabbobin Gida:

    . Babu shakka al’adar Bahaushe ta danganta ɓarna daga wasu dabbobin gida, manya da ƙanana.

     Akwai Akuya da Mazuru da Ɓera da Gafiya da dai sauransu. A dangane da Dabbobin Gida babu kamar waɗannan da aka lissafa dangane da abin da ya shafi abinci da muhalli, ɓarnarsu a bayyane take dare da rana, Su ma ɓarnarsu tana iya faruwa a dalilai kamar haka:

    Akuya: Bahaushe ya ɗora wannan hali na ɓarna ga akuya, wannan yasa har ya yi mata kirari da cewa: 1. Taɓa ƙofa mai asirin sata. 2. Jar akuya mai kai ga yara ɓarnar.

    Haka kuma Bahaushe ya lura da yanayin ɓarnar da akuya kan yi, sannan kuma ya rarraba ta kamar haka: Idan akuya ta tarar da dannin kara (shinge), wanda aka yi shi a tsaye, sai ta sanya ƙahonta ta huda don ta shiga. Haka kuma, idan dannin a kwance a ka yi shi,sai ta yi rimi (miƙe ƙafafun gabanta sama), a inda ta kan tsaya bisa ƙafafunta na baya, saboda ta yi ɓarna, sai ta danna ƙafafunta na gaba don ta shiga ta yi ɓarnawannan ya haifar da Karin maganganu kamar haka:

    v  Jar Akuya mai kai ga yara ɓarna.

    v  Taɓa ƙofa mai abincin sata.

    Dangane da haka ne Alhaji Musa Ɗanƙwairo ke cewa:

    Da Burgu da Zomo da Kurege,

    Kowanne hali ya kai bambam,

    Zomo shi ka rami cikin ƙunƙu,

    Kurege shi ya ranar gaba,

    Ya yi ɓullo nai can da ban,

    In an ragaɗa in fice wa ta.

    Ya ƙara da cewa a wata Waƙar:

    Mage kin wahal da mata,

    Suna ta jere kina ta rusawa,

    Mage farauta ta kai cikin ƙorai,

    Mage ja’ira shege kan nan kama da ɗan ƙoƙo.

    Akwai misali a wani rubutaccen zube da aka samu jirwayen ɓarnar akuya a ciki, kamar haka:

    Labarin Nahana Sarkin Rowa.

    “A wani gari wai shi Tanga,an yi wani mai rowa, sunansa Na-hana. Wanda ba taɓa ganin ya ba wani ko ruwan sha in ya bi ta gidansa ba. Da anininsa ya ɓace masa,gwamma ka mare shi sau biyu. Yana da awaki da tumakai ƙwarai da gaske ko shi ma bai san iyakarsu ba. Ran nan ya dawo daga kiwo, sai wata akuyasa ta sa kanta cikin tukunya kai ya ƙi fita. Na-hana ya yi ya yi, ya kasa jawowa. Ga shi kuwa ba ya iya fasa tukunyar, don yana ganin ɓarnar kuɗi ne. Bisa dole ya kira Mahauta suka yi cinikin akuya ya sayar, yace su yanka su cire kan su ba shi tukunyarsa. Mahauta yanka akuya amma suka kasa cire kan akuyar daga tukunya. A maimakon haka sai tukunya ta fashe Na-hana ya yi baƙin ciki ƙwarai. Ga sayar da akuya da arha ga asarar tukunya ta fashe, sai da ya yi kuka har da hawaye. Tun daga ran nan bai ƙara ajiye a ƙasa ba, kullum sai bisa inda awaki ba su kaiwa saboda ɓarna. ” [8]

    Mazuru: shi ma gwani ne kuma ya yi fice a fagen ɓarna a wata fuskar kuma kwaɗayi, ko a maganganun yau da kullum da akan ce: 1. Mazuru cinye kaji. 2. Tuban muzuru, amma ga kaza a baki. Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a waƙarsa ta Sarkin Yawuri Mamman Tukur Mai martaba, cewa ya yi:

    Jagora:Babban mazuru can haka,

     Sai tumbiɗar kaji yakai,

     Shi ba shi jin tsoro haƙo.

     Sarkin Tukur Baban Hassan

    Gindi: Mamman Tukur Mai martaba,

    Dangane da ɓera da kurege da gafiya, su ma suna da ɗabi’ar ɓarna a wurin Bahaushe, amma su a matsayin tsumi da tanaji yake. Don kuwa in har suka samu kayan abinci sun dinga ɗiba ke nan har sai inda ƙarfinsu ya ƙare. Musamman gafiya idan ta samu buhun gyaɗa ko kalwa, ɓata na ɓatawa ta ɗebi ɗiba zuwa a matsayin tana tattalin abinci.

    Gafiya: Tana iya kwana tana ɗibar kayan abinci tana tarawa, a wani wuri na musamman da ake kira “horonhoromi”, wani rami ne wanda ya yi kama da rumbu ko sito. Akwai wasu maganganun azanci masu cewa:

     1. Tarin gafiya tarin banza.

    2. Gafiya tara ba don ki ci ba,

    3. Gafiya ta tsira da na bakin ta.

    4. Gafiya ki kwana tari da asuba a buge ki.

    Ƙwari Da Tsutsotsi:

    Bahaushe na danganta ɓarna da wasu ƙwari da tsutsotsi. Wannan ɓarna kan shafi gida inda Bahaushe kan zauna, da kuma Gona inda noma, ko rumbu gun adana abincinsa.

    Ɗabi’un Ƙwari A Tunanin Bahaushe

    Bisa la’akari da yadda ƙwari ke gudanar da rayuwarsu, sai Bahaushe ya alaƙanta wasu ɗabi’u na mutum ga ƙwari. Akwai ƙwarin da Bahaushe ya alaƙantasu da mugunta ko cutarwa, su ne kamar cinnaka da sauro da barbaje da rina da ƙwarƙwata da kuɗin cizo. Haka kuma, akwai waɗanda suka danganta da kwaɗayi, su ne kamar ƙuda da shazumamu da kwarkwasa da kyankyaso da tsatso. Bayan haka, akwai waɗanda ake alaƙantasu da kishin mace da sha’awa musamman gamaɗiɗi (ƙwaron rimi). Ban da wannan kuma akwai waɗanda ake dangantasu da kiyashi, gizo-gizo da zanzaro. Akwai masu zumunci da haɗin kai da biyayya ga shugaba, su ne kamar zuma da tururuwa da gwano da zago da sauransu. Akwai jarumai masu jan hali, su ne gwano da zago kiyashi da zirnaƙo. Akwai masu alaƙa da ƙazanta, su ne kamar ƙuda da kyankyaso da ƙwarƙwata da kuɗin cizo da bi-tsami da dai sauransu.

    5. 0 Kammalawa:

    Ƙarshen tika-tika tik, komai yai farko, dole ne yai ƙarshe, don haka wannan tsokaci dangane da bayanai da suka gabata bisa ga nazarin ɓarna matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe. Haƙiƙa an kawo bayanai masu dama da ka yi ƙarin haske tare da fito da irin kallon da ake yi wa ɓarna tare da nuna matsayinta a yanayin zamankewar Bahaushe. Da farko an kawo ma’anar ɓarna tare da ire-irenta, da fagagen da ake yinta, sannan da dalilan yinta, da lokutan aukuwarta ko aikatata, da wuraren faruwarta da kuma masu yinta. Tun daga mutane, da dabbobi, da tsuntsaye, da ƙwari da tsutsotsi da kuma wasu abubuwa marasa rai. Haka kuma an hararo irin yadda Bahaushe ya ɗauki ɓarna, muninta da kuma sakamakonta, tare matsayin masu yinta,

    Bisa wannan dalili ne, yasa muka ɗan tsakuro wani abu daga cikin fage na al’adar Hausa, saboda ko ba a shafa ba maruru ya ɗara kaluluwa. Dukkan bayanan da muka yi, to ya zo ne a matsayin fitila abin haskawa da kuma jagora. Bahaushe dai yace; lomar hasafi tafi kaɓakin tsiya, ƙaramin goro yafi babban dutse, sai a yi haƙuri da abin da samu. Alhamdu lillahi.

    Manazarta

    Ayuba A. B (2015), Ƙamusun Hausa Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

    Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. Zaria: Amadu Bello University Press.

    Bunza A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere,

     Lagos.

     Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. Triunph Publication Kano.

    Ɗangambo A. (1983) Kitsen Rogo. Triumph Publication Kano. .

    Ɗahiru B (2007) Tafsirin Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.

    Imam A. (1937) Magana Jar ice na 1, da 2, da 3. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

    Ƙamusun Hausa(2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano:Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.

    Madauci I. (1963) Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

    Bello A. (1980)The Hausa Dialect Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

    Yahaya Y. I. (1988)Hausa A Rubuce;Tarihin Rubuce-Rubuce cikin Hausa.

     Northern Nigerian Publication Company Zaria.



    [1]Dubi Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary na Bargery, G. P. (1993) Ahmadu Bello University Zaria. Shf 89

    [2] Encater Dictionary

    [3] Abraham, R. C. (1947)Dictionary of the Hausa Language,

    [4] Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006),

    [5] Bargery, G. P. (1934) a Hausa-English Dictionary & English Vocabulary London Oxford University Press.

    [6] East da Imam (1949) a littafin Ikon Allah, Northern Nigeria Publication Company Zaria

    [7] Hira da Malam Ashana Ɗankama Kano a Rediyon Jihar Kano 23/5/1998

    [8] Dubi littafin Ka yi ta karatu na 4 (1972) Muhammadu Ingawa da Jean Boyd shf—37-38.

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.