Bitar Ƙa'idojin Rubutun Hausa a Waɗansu Ƙagaggun Labarai
Umar Sunusi Zarewa
School of Secondary Education Languages
F.C.E (Tech.)
Gombe
08032702586
umarzsanusi@gmail.com
Da
Sani Adamu
Department of Languages and Cultures,
Federal University, Gusau, Zamfara, Nigeria
Phone Number: 07065411971
Gmail: adamufsk3501@gmail.com
Tsakure
Wannan
aiki ya mayar da hankali ne a kan ƙa'idojin rubutun
Hausa. Haka kuma ya bayar da muhimmanci ƙwarai a kan irin katoɓarar da wasu marubuta ke tafkawa a fagen amfani da ƙa'idojin
rubutu musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai na
Hausa. A yayin gudanar da wannan aiki, an yi amfani da gogaggun hanyoyin
tattara bayanai da suka haɗa da: Bitar ayyukan
da suka gabata, karance-karancen litattafan ƙagaggun labarai da
kuma taƙaitaccen nazari a kan ƙa'idojin rubutun
Hausa. Wannan binciken ya gano cewa ba a fagen amfani da ƙa'idojin
rubutun Hausa kaɗai ba, marubutan
sukan samu matsala ƙwarai musamman a wajen ginin jimla. Wannan aiki ya
tabbatar da cewa duk waɗannan kurakuran ana
samun su ne sakamakon mafi yawancin marubutan suna da ƙarancin
ilimi a kan lamarin da ya shafi ƙa'idojin rubutu. A bisa haka ne wannan muƙalar ke
ba da shawarar cewa, marubuta su yi ƙoƙari
wajen inganta iliminsu, musamman a fagen amfani da ƙa'idojin
rubutu domin hakan zai taimaka wa masu karatu wajen samun sauƙin
fahimtar saƙonnin da ke cikin littattafansu.
Fitilun Kalmomi: Ƙa’idojin Rubutu, Zube, Rubutu, Marubuta
1.0
Gabatarwa
Alamomin rubutu na
nufin ‘yan ɗigagga da zane-zane
da ake amfani da su yayin da ake rubutu. Ƙa'idojin rubutu kuwa
waɗansu dokoki ne ko
ladubba da aka gindaya da ya kamata mai rubutu ya kiyaye wajen rubutunsa
(Bunza, 2002:16).
Masana da dama, na
gida da na waje sun yi aiki tuƙuru wajen daidaita rubutun Hausa ta hanyar amfani da ƙa'idojin da suka dace. Masana kamar su: (Lepsius, 1862)
da (J.F. Schon da Prietzer, 1902) da (Mischlich, 1906) da (Westerman, 1911) duk
sun gudanar da ayyuka daban-daban dangane da ƙa'idojin rubutun Hausa. Haka kuma an gudanar da taruka
daban-daban domin gyara ƙa'idojin rubutun Hausa tun daga shekarar (1912) har zuwa
(1980).
Duk da irin wannan ƙoƙarin da masana suka yi bai hana samuwar kura-kurai a
cikin rubutu ba musamman a cikin littattafan ƙagaggun labaran Hausa, domin mafi yawan masu rubuta su
ilminsu ba mai zurfi ba ne. Za a tarar da masu aiwatar da rubuce-rubucen ba su
zarce takardar kammala firamre da sakandare ba. Idan kuma aka sami matakin
ilminsu ya zarce na sakandare, ba Hausa suka karanta ba asali. Idan kuma har
yanzu Hausar suka karanta, ba su fahimce ta ba sosai
Wannan muƙalar ta dubi irin kurakuran da masu rubutu cikin harshen
Hausa ke tafkawa a yayin da suke rubutu, musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai. Haka kuma za ta mayar da hankali wajen
fito da wasu daga cikin ƙa'idojin rubutun Hausa tare da bayar da ƙananan misalai a kan yadda ya dace a yi amfani da su a cikin
litattafan.
1.1 Ra'in Bincike
An ɗora wannan binciken ne a kan ra'in ƙwaƙƙwafi (Close reading). An ɗora wannan aikin bisa wannan ra'i ne sakamakon bin
diddigin da aka yi wa wasu litattafan ƙagaggun labarai na
Hausa domin fito da kura-kuran marubuta a cikin littattafan. Ra'in ƙwaƙƙwafi shi ne da ke nazarin rubutu ta ɓangaren amfani da kalmomi da jimloli da kuma ma'ana a
cikin rubutu. Ra'in yana nazarin abin da aka rubuta da kuma yadda aka rubuta
shi kamar yadda Snow, da Connor, (2016) suka ruwaito.
1.2 Dabarun Bincike
Domin samar wa wannan
bincike ingantaccen muhalli, an yi amfani da gogaggun hanyoyin tattara bayanai
da suka haɗa da:
a. Bitar ayyukan da
suka gabata
b. Karance-karancen wasu
littattafan ƙagaggun labarai
c.Taƙaitaccen nazari a kan ƙa'idojin rubutun Hausa
d. Bincike ta hanyar amfani
da yanar gizo
2.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Rubutu Da Ƙa'idojinsa
Rubutu wata hanya ce
ta isar da saƙo da ake amfani da shi a tsakanin al'umma. Wannan kuwa ya
samo asali tun lokacin da al'ummar idanun al’ummar Hausawa suka buɗe dangane da harakar rubutu a faɗin duniya. Rubutu na ɗaya daga cikin hanyoyin da al'ummar Hausawa ke isar da saƙonninta musamman ta hanyar wallafa litattafai, jaridu da
mujallu, da dai sauransu.
Dangane da ma'anar
rubutu kuwa, masana da dama sun ba da gudummuwa sosai. A bayanin Pavert
(1993:8) cewa ya yi "Rubutu wata dabara ce ta yin wasu alamomi da za su
wakilci magana". Shi kuwa Yahya (1988:1) ya bayyana cewa "Rubutu na
nufin yin amfani da zayyana wasu alamomi a kan takarda ko a kan wani abu mai
bagire don sadar da magana".
2.1 Ƙa'idojin Rubutu
Ƙa'idojin rubutu na nufin dokoki ko ladubba da ya kamata
mai rubutu ya kiyaye a lokacin da yake rubutunsa. Waɗannan ƙa'idoji ne ke gyara rubutu da sanya masa tsarin da zai ba
da dammar ya karantu (Sa'id, B. 2004). Wasu daga cikin waɗannan ƙa'idoji sun haɗa da:
1. Ƙa'idojin raba kalma
2. Ƙa'idojin haɗe kalma
3. Nuna mallaka
4. Alamomin rubutu
Waɗannan rukunnai da aka lissafa a sama su ne ke ƙunshe da dokokin rabawa da haɗe kalmomi a yayin da ake rubutu. Misali, kalmomin korau,
dirka, tsayayyen wakilin suna da dai sauransu. Haka kuma suna ɗauke da kalmomin doguwa da gajeruwar mallaka. Sannan kuma
suna ɗauke da dokokin da ke
bayani a kan yadda ake amfani da manya da ƙananan baƙaƙe a lokacin da ake rubutu. Haka kuma suna ɗauke da alamomin rubutu. Wasu daga cikin waɗannan alamomi sun haɗa da:
A. Ayar
tsayawa/alamar tsayi (.)
B. Waƙafi (,)
C. Waƙafi mai ruwa (;)
D. Alamar tambaya (?)
E. Alamar motsin rai
(!)
F. Ruwa biyu (:)
G. Alamar zancen wani
(" ")
H. Alamar zarce (...)
I. Karan ɗori (-)
J. Baka biyu ( ( ) ).
3.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Ƙagaggen Labari
Masana da dama sun
tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar ƙagaggen labari. Misali: (Yahaya 2016:2) Cewa ya yi "Ƙagaggen labari, labari ne da ke cike da zantukan hira da
nishaɗantarwa wanda ba da
gaske ya taɓa faruwa ba”. Yahaya
(1988:7) Ya bayyana tarihin rubuce-rubuce na ƙagaggun litattafai bai daɗe sosai ba, domin kuwa an same su ne bayan shigowar
Turawa masu yaɗa addinin kirista.
Turawa kamar irin su J.F Schon (1957) da sauransu.
3.Kura-kurai A Cikin rubutun Hausa
Ko shakka babu akan
sami kura-kurai da dama a cikin rubutu wanda hakan ba ƙaramin cikas yake haifarwa a wajen fito da ma'anar saƙo ba. Irin waɗanann kura-kuran akan same su a wajen ƙirar kalmomi, ginin jimla da kuma sauran wuraren da ke da
alaƙa da dokokin rubutu. Yanzu ga waɗansu misalai na jimloli da za a iya dubawa kamar haka:
1. Aminu bai je
makaranta ba.
2. Wanda bai ji bari
ba, ya ji hoho!
3. Wane ne ya zo?
4. Matarsa malama ce.
5. Waccan akuyar tawa
ce.
6. A bar shi ya je
karatu.
7. Wannan al'ummar
(Hausawa) suna da karimci.
8. An yi mini wasa da
hankali.
9. Alhaji ya wuce
buguzum-buguzum.
10. Kayan da aka
sarrafa ga su kamar haka:
Idan aka yi la'akari
da waɗannan misalan da aka
lissafa a sama za a ga cewar, ƙa'idojin rubutu sun taka muhimmiyar rawa wajen fito da
ma'anar waɗannan jimloli. Idan
da kuwa za a cire waɗannan ƙa'idojin to da rubutun na iya hargitsewa ta yanda ma'anar
ma za ta iya canzawa.
Ta wani ɓangare kuma za a iya kawo misalai na wasu jimloli da
rashin amfani da ƙa'ida kan iya haifar da sauyawar ma'ana ko kuma ya sanya
jimlolin su zama masu harshen damo. Misali:
1a. Ba shi ya ci (Let
him eat/give him to eat/allow him to eat)
1b. Bashi ya ci (He
was credited)
2a. Yaƙi ya je (He went for a war)
2b. Ya ƙi ya je (He refuse to go)
3a. Kin tafi kin bar
ni ? (Quetion)
3b. Kin tafi kin bar
ni. (Comment)
A nan ma idan aka
duba za a ga ƙa'idojin rubutu sun yi aiki sosai wanda idan da za a cire
su mai karatu ba zai samu fahimtar abin da ake nufi ba sosai.
3.2 Nazarin Kura-Kurai A Wasu Litattafan Ƙagaggun Labarai Na
Hausa
Ko shakka babu littattafan
ƙagaggun labarai na Hausa na cike da ɗumbin kura-kurai wanda har ya sa ake ganin wannan a
matsayin gazawar marubuta littattafan ƙagaggun labaran.
Samuwar irin waɗannan kura-kuran kan
juya akalar saƙon da marubuci ke ƙoƙarin isarwa zuwa wata kafa/kusurwa ta daban. Ga dai
misali a cikin wasu littattafai:
a. Fateema ta ce kusan
kullum abinda ke faruwa a gidanmu ke nan kullum sai ya daketa yace sai ta auri ɗan 'yar uwarsa, ita kuma ta dage bazata aure sa ba (Ribar
biyayya, 2021:1)
A cikin wannan zancen
za mu ga cewa ba a yi amfani da alamomin kyautata rubutu ba. Ya kamata a yi
amfani da alamar zancen wani. Haka kuma akwai wurare da yawa da ya kamata a
sanya alamar tsayawa (aya), amma ba a sanya ba. Sannan rubutun sam ba a yi
amfani da dokokin rabawa da haɗewa ba a cikinsa. Ga
wasu misalan kamar haka:
b. Tace yauwa gogo saisa
nake sonki mema zakiyi dashi bani ina miki komi ba barima nai miki shara sai
kiban kudin iloka (Matar Soja, 2022: 2)
A wannan misalin da
ya gabata za a ga cewar, marubucin wannan littafin ya tafka kura-kurai masu dama
a cikin rubutunsa, domin kuwa rashin amfani da ƙa'ida ya janyo sauyawar ma'anar wasu kalmomi kamar:
"Saisa", Bani" da kuma "Barima" waɗanda duk kalmomi ne da ke zaman kansu kuma suna ɗauke da ma'ana ta daban a cikin rubutun Hausa. Ga wasu
misalan kamar haka:
c. In ma ta yi mezanyi
da ita tacigaba da masifa inbaka santa meyasa baka saketaba yace baze yihuba
yarinyar kanen daddy ce fa (Rainon ta zan yi, 2014: 23)
A wannan misalin ma
za a ga cewa bayan cakuɗe rubutun da aka yi
ta hanyar rashin yin amfani da dokokin raba kalma, an kuma haifar da sauyin
ma'ana wajen rubuta jimlar "Yiwu ba" wadda marubucin ya rubuta kamar
haka: "Yihuba".Ga wasu misalan kamar haka:
d. Wayarta dake
gefene yafara ringing dasauri tasa hannu tadau wayar hade dasawa a kunne tana
fadin my one and only umma kin wune lafiya? daka dayan bangaren umma tace
muneera kizu gida muna da bukatar ganinki akwai magana mai muhimmanci dazamuyi
tana karasa fadan haka ta kashe wayar (Zaman Hostel, 2022: 1-2)
e. Yayan mahaifinta
wanda ake kira da baba bello shiya kalle muneera yace, muneera inaso kibude
kunnowanki da kyau sanan kuma ki saurareni da kunnen basira, inason kisan ciwa
abunda muka zaba miki a rayuwa har abada bazai taba zama cutarwa a garekiba
saidai yazama alheri, kallonshi takeyi cikin rudo domin bata fahimce inda ya
dosa ba (Zaman Hostel, 2022:3)
f. "Haba Ahmad
meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowanne ɗan'Adam da irin tasa ƙaddarar, na wani yafi na wani amma sam kai baka ɗauki kaddara ba" (A Gidanmu Take, 2020:1). A cikin
wannan misali da ya gabata za a ga samuwar kura-kurai da dama waɗanda da za a yi amfani da dokoki to da ana sa ran rubutun
ya kasance kamar haka:
Haba Ahmad! Me ya sa
ba za ka ɗauki ƙaddara ba? Ka sani fa kowane ɗan Adam da irin tasa ƙaddarar. Sai dai ta wani ta fi ta wani, amma kai sam ba
ka ɗauki kaddara ba.
g. Aiko zaki amayar da
kayan cikin kine (Babban gida, 2015: 2)
A waɗannan misalan da suka gabata na 'e' da 'f' sai dai a ce
Allah ya kyauta! domin kure da gazawar da aka samu a cikin rubutun har ya wuce
misali. Idan aka lura da kyau za a fahimci cewa mafi yawan kalmomi da jimlolin
da aka yi amfani da su a cikin rubutun an saɓa ƙa'ida sosai. Waɗannan kura-kurai duk suna faruwa ne sakamakon gazawar
marubutan wajen tashi tsaye domin neman ilimin da zai ba su damar inganta
rubutunsu. Ga wasu ƙarin misalai kamar haka:
h. ashraf yabiya tare
da sa hannu cikin aljihu ya ciro 'yan dari biyar guda shida sababbi (Shu'umin
namiji, 2019: 2)
A wajen rubutun
Hausa, kuskure ne a yi amfani da ƙaramin baƙi wajen rubuta sunan yanka kamar yadda waɗannan marubuta suka yi. A doka ana fara rubuta sunan
yanka da babban baƙi. Haka kuma a misalin da ya gabata na "h" an
samu kuskure a wajen rubuta kalamar "Aiko" da "Zaki" waɗanda kalmomi ne masu cin gashin kansu a Hausa.
Sanannen abu ne cewa
a rubutun Hausa ba a liƙa wa kalmomin dirka kowacce irin kalma walau a gaba ko a
baya. Duk inda kalmomin dirka suke suna fitowa ne su kaɗai. A waɗansu lokutan akan
sami masu rubutu su rinƙa rubuta su a cikin litattafansu kamar haka:
i. Alhaji ya ce
" Ba ita bace waccance "
j. Menene haka
Alhaji? (Maraicin Nawara, 2020: 17)
Idan aka lura za a ga
cewar duk an haɗe kalmomin na dirka
wato "Ne" da "Ce" wanda kuma hakan kuskure ne.
A wasu jimlolin kuwa
akan sami wasu marubuta masu amfani da kalmomin dirka a muhallin/wurin da ba su
dace ba. Wato sai su rinƙa sanya dirka jinsin namiji a muhallin da ya kamata a
sanya ta mace. Misali:
k. Ga ta fara, ga
idanu, idan ka gan ta sai ka ce Balarabiya ne (Shu'umin namiji, 2019: 8)
l. Nan take sai Amina ta tuna cewa wannan ai irin motar
Usman ne (Shu'umin namiji, 2019:8)
m. A bayan ɗakinsa ce ta ɓuya, wannan ne ya sa har Kadija ta fita ba ta gan ta ba
(Shu'umin namiji, 2019: 19)
Idan aka lura da waɗannan misalan za a ga cewa an samu kura-kurai na sanya
kalmomin dirka a muhallin da bai dace ba. Kuma hakan kuskure ne a cikin rubutu.
Alamar hamza waƙafi ne da ake sanyawa a saman gaɓar kalma (Ba a ƙasa ba) domin rabawa
a tsakanin gaɓar da ta ƙare da wasali da kuma maƙwaɓciyarta da ta fara da
wasali (Ba a amfani da wannan alamar a farkon kalmar da ta fara da wasali) Ana
amfani da wannan alama ne saboda dalili biyu: Na farko domin nuna cewa ba ɗaurin wasali ko tsawon wasali ake nunawa ba. Na biyu
kuwa, sauƙaƙa furuci, (Bunza, 2001:184-186 ). Misali: Mu'amala, sa'a,
,ɗabi'a,fara'a,Sa'adiyya,
da dai sauransu.
Marubuta ba su cika
amfani da wannan alamar hamza ba, hakan ya sanya suke sanya ta a inda bai dace
ba. Misali:
n. Da Magajiya da Ummi
Aisha suka dinga had'ata a dole ta hak'ura Ihsan ta karb'a (Ummi Aisha, 2019:
35).
A cikin wannan
misalin za a ga marubucin bai yi amfani da alamar hamza a kan yadda ya dace ba
domin kuwa bai sanya ta a muhallinta ba.
o. Daria sukai
dukkansu suka nufa wajen mai adaidaitasahun akai ciniki (Ummi Aisha, 2019: 35).
Bayan kwamacalar da wannan marubucin ya tafka, kuma za a ga cewar a rubutun
nasa ya yi amfani da kalmar "Daria" wadda sam ba kalmar Hausa ba ce.
4.0 Sakamakon Bincike
Sakamakon wannan
binciken ya yi daidai da hasashen binciken. Tun daga taken wannan aikin za a
fahimci cewa ana da niyyar bayyana gazawar marubuta litattafan ƙagaggun labarai na Hausa ta fuskar rashin amfani da ƙa'idojin rubutu yadda ya dace. A nan za a iya cewa
kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin kuwa
ko da aka duba wasu daga cikin litattafan ƙagaggun labaran, sai
ga shi an samu kura-kurai masu tarin yawa wanda har aka kawo misalan kaɗan daga cikinsu. Kura-kurai da ake samu a cikin rubutu
suna da tasiri ƙwarai wajen daƙushe daraja da ƙimar marubuta. Baya ga wannan matsala kuma, har ila yau
suna janyo sauyawar rubutu ta fuskoki da dama kamar haka:
1- Ta fuskar ma'ana
2- Ta fannin ginin
jimla
3- Ta fannin ƙirar kalma
4- Amfani da wasu
haruffa da babu su a harshen Hausa. Misali, "x".
Waɗannan matsaloli da aka kawo a sama suna da tasiri sosai
wajen janyo wa marubuta litattafan ƙagaggun labarai na
Hausa wasu abubuwa kamar haka:
1- Durƙushewar kasuwa.
2- Gazawa wajen cimma
manufa.
3- Gundurar da masu
karatu.
4- Rikitar da masu
karatu wajen ƙoƙarin fahimtar saƙo.
5- Cin amanar ilimi.
6- Lalata darajar
harshen Hausa da kuma sauran abubuwa makamantan waɗannan.
7- Amfani da kalmomin
da ba na Hausa ba a matsayin na Hausa.
Wannan ba abin mamaki
ba ne, domin kuwa bincike ya nuna cewa mafi yawa daga cikin marubuta litattafan
ba su da ƙwarewa sosai ta fannin ilimin da ya shafi ƙa'idojin rubutun Hausa da ma Hausar baki ɗaya. Haka kuma ba su tuntuɓar masana a yayin da suka gudanar da rubutunsu domin a yi
musu gyara. Suna ganin kowane gauta ja ne, wanda kuma bah aka abin yake ba.
4.1 Kammalawa
A cikin bayanan da
suka gabata na wannan muƙalar, an yi ƙoƙarin fitowa da ma'anar rubutu da ƙa'idojinsa. Haka kuma an yi gajeran sharhi dangane da
kura-kurai a cikin rubutun Hausa inda har aka bayar da wasu ‘yan misalai. Bayan
wannan kuma, an yi ƙoƙarin fito da wata ma'ana daga cikin ma'anonin ƙagaggen labari. Sannan kuma an bayar da misalai da dama
dangane da kura-kurai waɗanda aka zaƙulo a cikin wasu daga cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa. A cikin wannan aiki da aka
gabatar za a ga cewar, kura-kurai a cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa abu ne wanda ya kamata marubuta
su kiyaye, domin ta hanyar kiyayewar ne za su samu damar isar da saƙonninsu cikin sauƙi kamar yadda wannan
muƙalar ta yi bayani.
Manazarta
1. Adamu, A. (2017).
Maraicin Nawara. First Class Writters Assocition Com.L.T.D. Kano
2. Abdullahi, A. (2022).
Nana Fatima. Interligent Writters Association Com.L.T.D. Kano
3. Aliyu, S.R (2020).
Ummi Aisha. Writters Forum Company Press Limited Kaduna Zariya
4. Abdulmajid, R. (2014).
Rainonta zan yi. Khairat-up Company press limited Kaduna Zariya.
5. Bunza, A.M (2002).
Rubutun Hausa (Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa) Don Masu Koyo Da Koyarwa. Lagos
State, Nigeria.
6. Inuwa, Y.F. (2021). Ƙa'idojin rubutun Hausa. Gwammaja printing press, Nigeria
Limited, Kano state.
7. Junaid, A. (2020).
Ribar biyayya. Interligent writters Association com.L.T.D.
8. Muhammad, A. (2022).
Matar Soja. Writters Association Company, press Kano.
9. Tukur, S. (2022). Farar Wuta. Writters association Company Press
Limited Kano.
10. Yahaya, I.Y., Zariya
M.S., Gusau S.M Da 'Yar'aduwa T.M. (2007). Darussan Hausa, Domin
11. Yahaya, S. (2019). Shu'umin Namiji. Hajara Love Company Press Limited Kano
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.