Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani A Kan Sallar Walha (Dhuha)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mallam yaya akeyin sallah walaha kuma su wani surori ake karantawa dakuma lokacin da za'ayi sallah

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Sallar Dhuha ita ce Bahaushe ke ce mata "Walha. Sallar Walha sunnace mai karfi wadda aka kwadaitar akan kowane musulmi ya raya wannan Sallar domin dacewa da abu biyu koyi da Manzon Allah da bin Umarnin da kuma dacewa da falala da lada mai yawa.

بن باز رحمه الله:-

Yana cewa:- "Sallar Walha sunnace ta Manzon Allah mai karfi wadda ya aikata ta kuma ya kwadaitar da Sahabbansa akan aikita ta".

Allah yana cewa:

وَالضُّحَى

Allah yana rantsuwa da Hantsi ko Walha idan Allah yayi rantsuwa da wani abu to yana nuna girmama wannan abu da matsayinsa awajan Allah".

Hadisan Manzon Allah masu yawa sunzo masu bayyana falalar sallar Walha, ga kaɗan daga cikinsu;-

1- Yazo acikin Hadisil Qudsy, Allah mai girma da Buwaya yana cewa:- {Ɗan Adam, kayi min Raka'o'i guda huɗu a farkon yini, zai isarmaka wannan yinin zuwa karshensa}

@أخرجه الترمذي (475).

"Wannan yana bayyana mana dukkan wanda yayi sallar Walha raka'a huɗu a farkon yini to Allah zai isar masa zuwa karshen yinin da kariyarsa da taimakonsa na musamman".

الطيبي رحمه الله تعالى:

Yana cewa; An isar maka al'amuranta da shagulgulanka da baka kariya da kiyayeka daga abin ki bayan sallarka ta Walha har zuwa karshen yini,......".

@تحفة الأحوذي :2/478

2- Manzon Allah yana cewa; (Jikin mutum akwai gabobi guda 360, kuma an dora masa yin sadaka akan kowace gaɓa) sai Sahabbai suka ce masa:

"Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon Allah ??" sai Yace;

(Goge majinar ko kakin da akayi a masallaci, ko dauke wani abin cutarwa daga akan hanya, idan kuma mutum bai sami damaba, to yayi sallah raka'a guda biyu na Walha ya isar masa)

@الألباني رحمه الله ,صحيح الترغيب

3- Manzon Allah yana cewa;

(Babu mai kiyaye Sallar Walha sai bayin Allah masu yawan komawa zuwa ga Allah, sallar Walha sallace ta bayin Allah masu yawan konawa zuwa ga Allah)

@صححه الألباني رحمه الله.

Mafi karancin Sallar Walha raka'a biyu, amma bata da adadi wajan yawanta ko nawa ka iya ne, amma wasu Malaman sun tafi akan mafi yawanta shine raka'a Takwas kamar yanda Manzon Allah bai wuce raka'a takwas ba kamar yanda Hadisin Ummu hany R.A ta ruwaito.

Lokacin Sallar Walha yana farawane daga fitowar rana ta ɗan daga kaɗan kamar bayan fitowar rana da minti 30 zuwa 45am har zuwa gab da zawalin rana daga tsakiya da yan mintina biyar.

@ابن عثيمين مجموع الفتاوى (14/ 306))

Wato kamar; "Daga karfe 7am zuwa 11:45am.

mafi falala da alkhairin lokacin yin Sallar Walha, shine lokacin da rana ta fara zafi sosai, lokacin da mutane sukafi shagaltuwa da aiyukansu na yau da kullum, kai kuma sai ka shagaltu da gani da Ubangijinka, gab da zawalin rana.

@اللجنة الدائمة (6/148)

بن باز رحمه الله:-

Yana cewa; "Abinda yafi muhimmanci shine idan mutum yana da damar yinta a lokacin mafi falala to yayi amma idan baya da dama to yayita a farkon yininsa, amma yinta lokacin da rana tafara zafi sosai yafi".

Daga Nana A'isha رضي الله عنها tace; Manzon Allah yayi Sallar wallaha, sannan yace;

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ, ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ , ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

"ALLAHUMMAGH FIR LI,WA TUB ALAIYA, INNAKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM" har sai da ya fadi hakan sau 100.

@رواه البخاري رحمه الله في اﻷدب المفرد وصححه الألباني رحمه الله حديث رقم 619.

ابن عثيمين رحمه الله

Yana cewa: "Sallar walha idan lokacinta ya wuce to ta wuce ba'a ramawa domin Sallah ce mai lokaci kayyadadde".

ابن باز رحمه الله:

Yana cewa: "Sallatul Ishraki wato Sallar hantsi itace sallar walha afarkon lokacinta, kuma sunnace ta kowace rana".

Allah ka bamu ikon kiyaye wannan sunnah mai girma.🤲

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.