Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Zan Aure Ka Ba Sai Ka Saki Matarka

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam na dade da aure amma bamu samu haihuwa ba. Matata tana yi mun biyayya sosai bani da wata matsala tare da ita. Kwatsam sai soyayya ta shiga tsakanina da 'yar gidan Kanin babana, ta yarda zata aureni amma bisa sharadin cewa idan na aureta sai na saki matata ta gida. Duk da cewa yarinya ce mai ilimin addini, nayi ƙoƙarin fahimtar da ita cewa wannan sharadin bai dace ba, amma taƙi amincewa wai dole sai nace na yarda da haka. Amma fa iyayenmu duk ba su san da wannan sharadin ba. Nace mata eh na yarda, amma acikin zuciyata ban amince ba. Kuma tabbas ina sonta amma bazan iya sakin Uwargidana saboda ita ba. Duk da cewa akwai yiwuwar ita ɗin zan samu haihuwa da ita In shã Allahu. (Duk dangin mamanta suna da yawan haihuwa) Yanzu haka anyi mana baiko, saura 'yan kwanaki a daura mana aure. Nace Shin Malam mene ne halascin auren nan namu? Domin ni dai gaskiya bazan saki matata ba..

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Lallai wannan alkawarin ko sharaɗin da kuka Ƙulla ba halastacce ba ne, don haka bai lazimceka ka cika sharaɗin ba. Amma dai aurenku da matarka ta farko yana nan, babu abin da ya taɓashi. Haka nan aurenka da amarya ma ya yiwu mutukar dai an Ƙullashi bisa sharudan da musulunci ya ajiye.

Duk wani sharaɗin da ya kunshi saɓon Allah, ko umurni da mummunan abu, bai lazimci musulmi mumini ya cikashi ba.

Abu na biyu kuma ina yi maka wasiyyah tare da ni kaina da kuma dukkan mazajen aure cewa muji tsoron Allah wajen mu'amala tsakanin iyalanmu bisa adalci da kyautatawa. Kada soyayyar wata daga cikinsu ya sanya ka wulakanta wata. Kuma kada ka munana wa wata don burge wata.

Allah ne ya sanyasu a ƙarƙashin kulawarmu bisa amana kamar yadda Alƙur'ani da Sunnah suka karantar. Kuma Allah ya sanya mu sutura ne garesu kamar yadda suma sutura ne garemu.

Allah ya ce "SU SUNA DA HAKKI (AKANKU KU MAZAJE) KWATANKWACIN WANDA KE KANSU".

Duk sanda mutum ya nufi yin Ƙarin aure, zai fi kyau ya kokarta wajen kwantar da hankalin matarsa ta gida tare da wa'azantar da ita a kan muhimmancin haƙuri. Sannan kada ka yiwa amaryarka irin wannan alkawarin na zalunci. Allah shi kiyayemu.

Ita dai haihuwa Allah ke bayarwa. Idan kayi haƙuri ita ma Uwargidan zata haihu in Allah yaso. Kai dai ka rokeshi ya baka masu albarka shike nan.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments